Chapter One

236 7 4
                                    

KADDARAR RAYUWA

Story and Written by Hauwa Muhammad Sani (Hauwatyerh)

Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah (S W T) tsira da aminci Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu (S A W) iyalan gidansa da sahabbansa.

--Inspired By A True life Event--

Bismillahir rahmanin Rahim!

Tafe take kanta a kasa cikin natsuwa take tafiyar a hankali kamar mai tausayin kasa tana sanye da uniform ga dukkan alamu daga islamiyya tadawo, sallama tayi tashiga cikin gida a tsakar gidan ta tarar da ummah tana fifita wuta ga dukkan alamu wutar na wahalar da ita dan itacen basa ci ummah ta amsa sallaman nata "Wa'alaikumus salam" ta amsa tana cigaba da fifita wutan.
Bahijjah ta karasa gurin Ummah ta duka ta gaida ta kamar yadda takeyi a kullum idan zata gaidata. "Yauwa Bahijjah kindawo". "Eh ummah ya aiki?". "Lafiya kalau dama ke nake jira shiga daki ki cire uniform kizo ga wake cen ki surfa min" Ta nuna mata inda waken yake. "To Ummah.." Bahijjah ta amsa seta mike ta shiga daki ta cire uniform din nata seta sa kayan da take sawa aduk lokacinda zatayi aikin wake, sannan ta fito ta dauki waken tafara surfawa sannu-sannu harta kammala sai ta dauko tabarma ta baza waken akai.
Tsintsiya Bahijjah ta dauka tafara shara, ta share gidan kaf duk da kasancewar gidan babbane kuma ba siminti a tsakiyar gidan kasace amma haka take tsaftace shi safe da yamma, anfara kiraye-kirayen sallah magrib se Bahijjah ta dauka buta ta dauro alwala sannan ta shiga daki, kwance ta tarar da inno. Inno itace yayar Bahijjah sai Abdul amma mai kudi shine sunan da suke kiransa dashi sai nasir da kuma bello. bello shine auta, su biyar ne agurin mahaifansu Malam Tanko, dayake Allah yayiwa mahaifinsu Malam Tanko rasuwa, Malam Tanko mutumin kirki ne dan kaf unguwarsu bawanda bai san Malam Tanko ba sabida kirkinsa da girmama dan adam tunda yake a unguwar bai taba samun sabani da kowa ba to hakama yayansa sunbiyu halinsa sai dai dayace batayo halinsa ba wato dai albasa batayo halin ruwa ba.

Kasancewar Inno halin Babarsu tayo dan Ummah tanada zafi mace ce mai fada sosai ga rashin son raini sai dai Ummah tanada son mutane kuma abunta baya hadata da kowa ma'ana tanada son kyauta duk da cewar su talakawane amma takanyi kyautar abinda takeda idan taga wanda bashida ko mabukaci hakan zata daukeshi koda shikadaine hakan zata bada shi sai dai kash bayan rasuwar Malam Tanko kowa ya juya mata baya ba wanda ke taimaka mata hatta yan uwansa basa taimaka mata koda da abinda zasuci ne sai dawainiyar yaran tadawo kan mahaifiyarsu, dayake ita ba cima kwance bace tanada kokarin sana'a. Bayan tagama takaba sai tafara sana'ar kosai da kunu da safe dakuma daddawa.
Yaya, yayan Bahijjah ce ke tashin Inno dan da Yaya take kiranta, Inno tashi tayi a fusace tafara masifa "Ke dan uwarki ubanwa yasa ki tasheni ina bacci?". "Dama Yaya ankira sallah ne shine na tasheki kiyi sallah" Tayi magana a hankali
"Dan anfara kiran sallah shine zaki tasheni ina baccina mai dadi, to anki ayi sallar dan uabanki kuma bara kisake ganin ina bacci kitasheni wallahi sai kin yabawa aya zakinta!" Inno bata saniba ashe karab a kunnen Umma. Sai umma tahauta da duka tareda masifa "Yau ga yar iskan yarinya dan ta tasheki kiyi sallah shine kike zaginta harda fadin bazakiyi sallar ba, kinsan dama inada cikinki ko?, kin manta yau bakije islamiyya ba katuwar banza har yar kanwarta takai hizib arba'in amma ke ko ashirin bakikaiba sai rashin kunyar banza da kika iya! Wawuya mai kwanyar kifi kawai!" Ta kare fadan tana cigaba da dukanta, da kyar Inno tasamu ta kwace daga hannun umma.
Ta fita da gudu sai tura baki take tana magana kasa kasa yanda bawanda zai iyajin abinda take fada, arwala ta dauro tazo tayi sallah.
Zaune suke a tsakar gida suna cin abinci, tuwo ne da miyar kuka Inno kuwa cin tuwon kawai takeyi dan ji take kamar maganine take ci dan a rayuwar Inno ta tsani tuwo da miyar kuka hakadai suka kamala cin abincin! Bahijja kuwa tashi tayi ta kwashe waken da ta shanya ta je ta feceshi tazuba acikin roba ta ijiye taje ta kwanta dan kasancewar dare yayi.

Inna Sahiya kuwa hankalinta yakasa kwanciya sabida gaba daya yinin yau batayi waya da Lawal ba, Lawal shine babba sai kuma Hauwa yar Kuluwa yadda suke kiranta sai Bashir dakuma Sa'a, wadda itace auta. Inna Sahiya matace masifaffiya, dan fadanta bai tsaya kan yayanta ba har mijinta bata kyaleba har tasa bayada wata kima a idon yayansa musamman Sa'a dan kamar itace tadauko halin Inna Sahiya danma har tafi Inna rashin mutunci da rashin kunya dan hatta Innar bata kyaleba, badajin tsoron kowa dagakan iyayen harkan yayyun sai mutun daya shine Yaya Lawal shi kadaine take shakka acikin gidan sai dai kash shi ba mazauni bane.
Police ne ana yawan posting dinsa a garuruwa inda a halin yanzu anyi posting dinsa a jahar Zamfara yanzu dai a kalla zai kaishekara daya a Zamfara. A kowace rana yakan kira mahaifansa domin jin lafia suke kuma yakan tanbayi kanwarsa Sa'a dan dama yar Kuluwa tayi aure! Ranar wata lahadi tun safe har dare Lawal bai kira inna ba sai hankalinta yatashi dan bai taba wuni daya bai kirasu ba yau sai gashi har dare bataji kiransa ba kuma idan ta kirasa bata samu ba.

Ta gefan Lawali kuwa tun a daren assabar suka samu bayanin sirri akan cewar yan bindiga dadi sun aikawa kauyen baba dulun dake cikin karamar hukumar Bungudu a jahar zamfara takarda akan kowane lokaci zasu iya kawowa kauyen hari shine sai aka turasu domin bada tsaro ga kauyen kasancewar a garin ba network shiyasa bai samu damar kiran gida ba kuma koda sun kirasa bazasu sameshi ba.
Karfe 4:30 na asuba Umma ta tashi Bahijjah domin taje takai markaden waken, tashi tayi ta dauki waken dan dama Ummah ta wanke, dan haka seta dauka taje tayi markade! Ita kuma Inno bucket ta dauka ta nufi rijiya domin dibo ruwa Ummah kuma wuta ta hura ta daura sanwar ruwan kunu! Takammala dibar ruwa dai-dai lokacinda Bahijjah ta dawo daga markade. Ummah kuma tana dama kunu alwala suka dauro suka yi sallar asuba sai suka fara fitar da kayan kosai a kofar gida inda Ummah ke sayar da kokon da kosai, bayan sun gama fitar da kayan a waje sai suka fara shirin makaranta bayan sun kamala sukaje suka karbo koko da kosai suka sha sai suka wuce makaranta.

Hakadai rayuwarsu Bahijjah taci gaba da tafiya a kwana a tashi rayuwa sai tafiya take. Inno kuma rayuwa ta chanja duk tsananin Ummah da tarbiyar da tabasu sai Inno tayi watsi dasu, makarantan ma tadaina zuwa idan kuma tasa kafarta tabar gidan tofa sai baba tagani wani lokacin takan dawo gida ta kwana wani lokacin ma takanyi kwana uku har sati takeyi bata dawo ba! Tun Ummah na dukanta harta gaji tasawa sarautar Allah ido.
Allah yabawa su officer Lawal nasarar cafke shidda daga cikin yan bindikar da sukakaiwa kauyen Baba dulun hari dakuma kashe biyu daga ciki, bayan sun dawo ne ya dauko wayarsa don kiran Inna, ringing daya ana biyu sai ta daga bayan sun gaisa ya bayyana mata dalilin da yasa bai kirataba da kuma rashin samunsa da sukayi a waya taji dadin takuma yimasa addu'ar Allah yakara basu nasara akan aikinsu, sai kuma tamasa maganar kudi dan ita mai idon cin naira ce.
Itadai batada magana data wuce kudi, dalilin hakane ma yasa idon Sa'a suke a bude! Lawal yayimata alkawarin dazarar aka yimusa salary zai turo mata kudin "To Lawal amma katabbata da zarar an biyaku ka turomin kudin!" Ta jaddada mashi "To inna insha Allah! Ki gaida min da mallam". "Toh zeji!" Sannan sukayi sallam. Halin mahaifiyarsa yana matukar damunsa itadai batada wata magana sai ta kudi ko sata zakayi matukar zaka kawo mata kudi zata goyi bayanka shiyasa halinda yar uwarsa take ciki yafi ganin laifin mahaifiyarsu dan bata tsawatar mata.

Vote &Comment

Kaddarar RayuwaWhere stories live. Discover now