Tabashi Usman yayi Usman abokin aikinshi ne, ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yashiga "Officer Lawal lafiya dai tun dazu nake kanka inata kiranka amma bakama san inayi ba sai da na tabaka?" Ajiyar zuciya ya sauke "Hmmm Usman kaidai bari ba komai family issues ne kawai nake tunani"
"To Allah ya warware komai!". "Ameen Usman nagode!" Ya mishi godiyan kulawan da yake nuna masa, ''murmushi yayi yace Bakomai karka damu we are all thesame, ka tashi muje masallaci dan ankira sallah" A haka ya tashi suka nufa masallaci.Bahijjah dai yanzu ayyukan gida duk sun dawo kanta kancewar Inno bata cika zama a gida ba, har jikin bahijjah yasaba da aiki har takai batajin wahalarsa ko ganin yawansa! Yau dayake alhamis ne kuma makarantar su ta boko basa zuwa ranar alhamis da juma’a dan makarantar boko da Arabic ne, kalwa tadauko tafara gyarawa tana ciccire dattin da ke ciki, bayan ta kammala turmi ta dauko tafara surfa kalwar tanayi tana rera karatun suratul jinni da zazzakar muryarta mai dadin kira’a kamar wata balarabiya da tafito daga Saudi, haka dai harta kammala gyara kalwar tsab ta hura wuta tadaura tukunyar dafa kalwa taje kuma tasa wake ta surfa shima ta bazashi akan tabarma saiga Nasiru ya shigo dauke da markaden geron kunu. Ta karba seta yunkura zata kunna wuta kenan setaji sallama.
"Assalamu Alaikum!" Sallamar Ummah taji tadaga kanta ta kalleta "Wa'alaikimus salam, sannu da dawowa Ummah!". "Yauwa Bahijjah me zakiyi?" Ummah ta tambayeta. "Dama naga baki dawoba kuma ga yamma tayi shine nace bara na daura girki" Ta fadi cikin natsuwa "Aa bari kawai tunda na dawo sai na daura naga baki share gidan ba". "Eh Ummah yanzin nan na kammala tace markaden kunu shine nace bara na daura sanwa idan na daura sai naje na share dan naga yamma nayi!"
"To yanzu ijiye ashanar je ki dauki tsintsiya ki share gidan Allah yayimiki albarka" Ameen ummah !" Dan haka se Bahijja ta mike kawai se suka fara jin ana kunduma ashar a wajen gida kasancewar sun gane ko murayar waye shiyasa ba wanda yafita! Sega Inno ta shigo gidan tanata famar zage-zage kowa yatabata oho Allah kadai ya sani sai ita, dan bawanda yacemata cikanki dan ran Ummah yagama baci irin yanayin da taga Inno a ciki ita dai ba shigar arzikiba kuma sai famar tangadi take kamar zata fadi daka ganta ko ba'a fada ba kasan tadan watsa ne harta shiga daki tanata famar zagi, Kai Ummah ta girgiza acikin bacin rai tace "Allah yashirya, Allah kabani ikon cinye wannan jarabawar dakamin dakuma wannan ita ce 'Kaddarar rayuwata"
"Ameen Ummah Allah yashiryeta yakuma ganar da ita" Bahijjah tayi nata addu'an "Ameen Bahijjah!" Inji Ummah.Inna sahiya sai famar masifa takeyi dan yau Basher bakin halinsa yatashi bai kawo mata naman da yake kawo mata ba dan nama yake sayarwa kullun sai ya kawo mata nama amma idan bakin halinsa yatashi to ko karnin nama bazataji ba.
Malam yashigo yatarar da itatana sana'arta "Sahiya lafiya kuwa? Waya tabaki?" Ya tambayeta. "Waye kuwa banda wannan shashashan yaron Basher yau bakin halinsa ne ya tashi ko hanji bai kawo min ba bare nama tunda kai haka allah yayika da matattar zuciya dan kosan naira ashirin bazaka iya siya ka kawo min ba sai dai in kwadayi zai kasheni ya kasheni, mema akeyi da kaddararren aure irin naka? Sunan kawai mutun nada igiyar aure akansa ba abinda kake tsinanawa mutum!" Ta gama magana rai a bace.
"Allah yabaki hakuri Sahiya, tunda kedai kullun halinki sai abinda yaci gaba ba abinda ke raguwa! Kin tsufa amma bakisan kin tsufaba!" Seya mike ya nufi dakinsa ya barta tanata famar mita "oh Allah nagode maka da wannan Kaddarar rayuwa da ka kaddareni da ita, dan auren Sahiya kaddarane tun bata koyi batan wataba tafara nunamin halinta hargashi yanzu tsufa yakama amma ba abinda ya sauya daga halayenta! Allah nagode maka!" Ya gama magana yana zama.Shikuma Basher yana daga dakinsa dake a zauren gidan yana juyo fadan Inna harda yadda sukayi da Malam yace "Ai sai kiyi kigaji kibari wallahi yau ko karnin sa bazakijiba bare kici, tsohowa sai tsinanen kwadayi!" dayake shima ya dibo halinta rashin kunyane fal a cikinsa.
"Ayye lale iyaraye ayye lale maraba sangaya!" Sa’a ce tashigo cikin gida bako sallama sai famar cin cingom take kamar wata tsohuwar yar tasha. Inna Sahiya ta tarar tanata fada gurinta ta nufa tace "Sahiya me akayi maki? Waya tabaki?" dan a haka take kiranta kuma tana amsawa. "Nida wannan dan banzar yaron mana yauko hanta bai kawomin ba bare tsoka!"
Fuska Sa’a ta bata tayi gaba abinta tana fadin "Wallahi ni nazaci wani abin kirkine ai shine dai dai ke tunda bakinki baya gajiya da cin nama kullun sai kace mayya da tsinannen kwadayi!" Ashe tana jinta. "Sa’a ni kike kira da mayya?" Seta mike tabi bayanta daganin haka sai ta kwasa da gudu sai cikin daki tamayarda kofar ta rufe tana dariya "Dakin tsaya yar banza in nunamiki cewar ke karamar marar kunya ce"Malam dake daga daki yana jinsu "Kadan ma kika gani" shima Basher dayake daga cikin dakinsa duk yanajinsu dariya shima yake sun mayar da ita kamar mahaukaciya! Zama tayi akan kujerar dake tsakar gidan tana fadin zaku fito ku sameni tunda kun mayar dani mahaukaciya sai famar jijjiga jiki take tana ta haki da zufa
***.
Akwana a tashi har Bahijjah ta kai shekarar karshe na karamar makaranta wato primary 6, ayukkan gida kuwa sai abinda yaci gaba kasancewar ita kadaice dan Inno a halin yanzu bawanda yasan duniyar da take kusa shekara daya kenan basu sata a idonsu ba! Bayan fitar Inno daga gida, Zamfara ta nufa ita da kawarta Maryam amma reza shine sunan bariki da ake kiranta dashi. A wani gidan karuwai suka sauka! Wata magajiya wadda tayi suna awajen tara yara mata akan karkatacciyar hanya ta bin maza hannu bibbiyu. Magajiya takarbi su ganin cewar tasamu sababbin customers zata samu kudade! Dan Inno mace ce mai kyawon gaske ga diri ko mace yar uwarta ta ganta sai ta yaba bare da namiji.
Maryam ma kyakkyawace amma bata kai Inno ba sabida tsabar jan hankali a dakinta ta saukesu sabida su baki ne basuda dakin kansu!
Bayan kwana biyu da zuwan su reza sai magajiyata zaunar dasu inno ta tambayi sunansu ko wacce ta gabatar wa magajiya da sunanta sai tace Inno bai dace da itaba dan haka zata bata sunan da zata dinga anfani dashi inno tace "to ai sai abinda kikace uwar bariki" dariyar yan tasha magajiya tayi tace "tabbas wannan suna nane to daga yau ki ajiye Inno a gefe sunanki yar gwal" murmushi kawai Inno tayi tana kada kai irin na gogaggin yan bariki ko ince yar gwal dan yanzu shine sunanta sai magajiya tace.Vote &Comment
YOU ARE READING
Kaddarar Rayuwa
ActionA True Life Story!!! kaddarar rayuwata littafine da yake magana akan yanda rayuwa take, zaka iya tsintar kanka acikin kowane yanayi na rayuwa idan kuma kayi hakuri to zakaci muriyar hakurinda kayi...