Chapter Eight (8)

23 2 2
                                    

A daren ranar Bahijjah batayi bacci ba, sallah tayi takai kukanta a gurin ubangiji saida aka kira sallar asuba ta tashi ta gabatar da sallah tayi zaune akan sallaya tana jan charbi bacci barawo yayi gaba da ita.
***
A bangaren Inno kuwa taji labarin kanwarta Bahijjah tayi aure a zamfara take zaune da mijinta tasha alwashin sai ta gano gidanda Bahijjah take tayi binchike sosai ta kuwa yi nasara ta gano gidanda Bahijjar take tayi shigarta ta kamala ta kama hanyar zuwa inda Bahijjah sai dai kash batasan bahijjar batanan ba tayi sallama ta shiga dan tabbas wanna gidan shine gidanda akamata kwatance "Wa'alaikumus salam" Maman Abdul ce zaune a tsakar gida ta amsa sallamar
"Ina wuni?" Inno ta gaisheta "Lafiya kalau baiwar Allah..."
"Dan Allah tambaya nakeyi"
Maman Abdul tace "Allah yasa na sani" Da fara'arta "Dan Allah nan gidan Bahijjah take?" "Eh nan ne..."
"Dan Allah inane dakinta?" Tana magana kaman wata mutuniyan kirki. Maman Abdul tace "Baiwar Allah ke kuwa wacece ke da kike neman Bahijjah dan a iya sanina Bahijjah batasan kowa ba a garin nan bayan mutanen  dake cikin gidan" Murmushi Inno tayi tace "Ni yayarta ce uwa daya uba daya, sunana Inno". "Allah sarki kece Inno?" a cikin  alamar mamaki take magana "Karaso Inno tabbas Bahijjah tabani labarinki, shigo baiwar Allah ashe da rabon zan ganki...."  daki Maman Abdul ta shiga da ita ta kawo mata ruwa sannan ta kawo mata abinci,  kadan Inno ta tsakura. "...Bahijjah ko tabani labarinki, tace tanada yar uwa a zamfarar nan amma bazatace ga inda kike ba da tasan inda zata ganki da taje ta ganki danta dade bata ganki ba tun batayi aure ba, murmushi kawai Inno takeyi dan tasan abinda Maman Abdul take fada gaskiya ne ba karya a ciki "Bahijjar batanan ne ko taje unguwa?"
"A'a Inno, Bahijja ai tana Sokoto ta haihu har tayi arba’in!". Inno tace "To me ta haifa?"
"Namiji ta haifa, Kabir shine sunan yaron...." "Allah sarki, Allah ya raya mana shi!". "Ameen ya rabbi!" Maman Abdul ta amsa "To ni zan tafi sai kuma idan ta dawo insha allah zanzo tunda yanzu nasan inda take" Tama magana tana mikewa. "To Inno mun gode kwarai!" har kofar gida Maman Abdul ta raka Inno.
***
A firgice ta tashi, cikin bacci taji kamar kuka ashe kabir ne ya tashi yake kuka, a daidai lokacin ne Inna Sahiyya ta karaso kofar dakin tana kwallawa Bahijjah kira daukar kabir tayi sannan tazo ta bude dakin "Wai me kikeyi ne tun dazu nakejin kukan yaron nan kinaji kuma kin shareshi ko dukansa kikayi ne?" a cikin sanyin murya Bahijjah tacewa "Inna Sahiyya ina kwana?". "Bansani ba, idan ke keda kwanan to ki kwace shashashar yarinya ina magana kin mayar dani sa’arki!" Tana magana tana daga murya.
"Yi hakuri Inna bah aka bane?" Tayi magana a hankali "Idan bah haka bane to meye? ina gabas kina yamma kodan kinga mijinki ya kusa zuwa to bara kifara raina ni tunda zaki tafi kidaina ganin makiyarki ko?" 
"Yi hakuri Inna wallahi bacci nake bansan ya tashi ba, acikin bacci naji kukansa tashina kenan najiyo muryarki kina kirana..." Ta fara mata bayani
"Ba me? Bacci fa kikace? yanzu karfe nawa? karfe takwas amma baki tashi ba lallai iyye sannu sarauniya ga bayinki kin ije sumiki breakfast!"
"Yi hakuri inna yanzu zan fito na dora" Ta sake bata hakuri dan ita kwata-kwata ba meson tashin hankali bane "Mtsss! Aikin banza da kinjira wani ya girka miki!" Ta juya tayi wucewarta.

Koko Bahijjah ta dama kasancewar lokaci ya kure Sa’a ta fita tasiyo masu kosai amma ko kwara daya basu bawa Bahijjah ba kokon ma ba sugar haka  tasha.
***
Ranar juma’a tun karfe shida bahijjah ta tashi ta fara gyaran dakinta tayi duk wani aiki datasan tanayi acikin lokaci sabida yaune Lawal zai dawo yayi kwana biyu sai su wuce. Inna Sahiyya ce ta dawo dan fita tayi taje unguwa tatarar da bahijjah taci ado kamar sabuwar amarya salati tayi tana tafa hannu tana fadin "Yau me nake shirin gani, Bahijjah lalle fa naga kinyi harda kitso duk na murnar dawowar miji ne? Tunda nake dake ban taba ganin kinyi irin wannan ado ba sai yau dan mijinki zai zo nashiga uku ni Sahiyya, jama’a kuzo ku tayani gani bariki a fili!"
Tana maganar tana rike baki, Bahijjah dai kasa magana tayi dan batasan me zata fada ba, Inna Sahiyya ko sai abinda ta manta tanata famar zazzaga masifa sallamar malam ce tafanshi Bahijjah.
"Ina wuni Baba" Ta gaisheshi cikin biyayya kamar yadda ta saba a kullum. "lafia kalau Bahijjah ya kike ya gida?"
"Lafiya kalau Baba". "Ina abokin nawa ne?" Ya tambaya cikin wasa seta sake dukar da kanta "Yana daki bacci yakeyi..." Mtsss tsaki Inna Sahiyya tayi ta watsawa Bahijjah wata uwar harara tafice tana fadin "Aikin banza duk yanda kikayi bazaki iya asirce min yaro ba kiyi kissarki ki gama!" har tashiga daki tana bata daina Magana ba.

Baba ya girgiza kai cikeda takaici seya kalla Bahijjah "Kiyi hakuri bahijjah komai mai wucewa ne watarana sai labari, ni kaina hakuri nakeyi da halin Sahiyya zama da ita sai kayi hakuri dan Allah karkisa abin aranki har yazo ya haifar miki da wani ciwo na daban kinji?" "To Baba insha Allah nagode kwarai"
"Ba komai Bahijjah Allah yayi maki albarka" ta amsa da "Ameen Baba".
***

Kaddarar RayuwaWhere stories live. Discover now