CHAPTER (SIX) 6

29 1 0
                                    

Alhamdulillah sai gashi ta sunbulo babynta namiji kyakkyawa mai kama da mahaifinsa, akwana a tashi ba wahala har gashi ana gobe suna abun mamaki har lokacin Inna Sahiya bataje ganin jikan nata ba, dakyar aka samu aka lallabata taje yau ranar suna yaro yaci suna Kabir ansha bidiri sosai dan mutanen Gusau ma sunzo anyi biki lafiya an kammal lafiya! Washe gari da safe yan Gusau suka kama hanyar komawa gida.

Inno kuwa bariki ma yanzu ta fara dan yanzuma ta zama magajiya sannan ta koyi darasi dagakan hafiz taki bari ta sake daukar wani ciki tana murza barikinta yanda takeso ko wai wayen gidama batayi yanzu hafiz yanada shekara daya da wata bakwai, Sa’a kuwa yanzu ta fandare dan itama yanzun zaman kanta take ta kama daki sai dai ita batabar garinsu ba a garin take tata barikin sa'a banna shine sunan da ake kiranta dashi na bariki, Allah sarki duniya Malam yayi bakin ciki halinda yarsa ta zabarwa rayuwarta yayi kukan safe yayi da rana yayi na dare har ya dangan yasawa sarautar Allah ido domin yanzun inba addu’a ba, ba abinda zaiyiwa sa’a dan yayi fada yayi mata fada amma tayi biris.
"Kasan Allah ba inda zakaje sai ka biyani kudina, haka kawai kana nufin zakaci banza ka tashine? to bashi na fito yi ba bariki nazoyi dan haka idan kaga na sakeka to wallahi ka biyani kudina!" Sa'a take wannan masifan.
"Haba sa’a ai ba cewa nayi bazan biyaki bane, ba kudine a jikina amma gobe zan baki kudinki" Yayi kokarin yi mata bayani cikin natsuwa "Kutmar uba! aikin zunubin ma harda bashi? karfa ka manta ba aikin lada bane aikin haram ne ga zunubi ga bashi ai sai abin yayi min yawa wallah yau zanci gutsun uwarka idan baka bani kudina ba zan maka tsirara anan gurin!" Taci kwalarsa tana jijjiga jiki irin na shahararrun yan tasha wayanda idonsu ya bude da bariki, ba shiri yaga da gaske take dole ya ciro kudi ya mika mata bata karba ba tace masa nawane dari biyu ne ta buga masa ashar "......... Kamayar dani karamar karuwa mai neman abinda zatasawa bakin salatinta ko? to ba yunwace ta koroni daga gidanmu ba aa son duniya da kwadayin rayuwar bariki wallahi zanmaka uwalakanci idan baka bani kudina ba, ai ba dari biyu mukayi ba!" Tana masifa tana giggiga, dayaga da gaske take dole ya zaro dubu daya ya bata seta ja tsaki ta karba "Da dai yafima, karamin dan tasha kawai" Seta shiga dakinta, haka ya tafi bako kunya.

Yaune Bahijjah ta cika arba’in da haihuwa ga al’adar sakkwatawa idan yaro yayi arba’in akanyi masar sadaka arabawa makota haka kuwa akayi, Ummah tayi masa mai yawa sosai ta rabawa makota da yan uwa! Washe gari Inna Sahiyya tun da safe misalin karfe takwas na safe sai gata ta daka sammako a gidansu Bahijjah, takuwa yi sa’a dan ta tarar da Ummah, sallama tayi tadanna kai acikin gidan "salamu alaikum....." tana wani yamutsa fuska "wa’alaikissalam aa yau Sahiya ce agidan?"  da fara’a Ummah ta tarbeta "eh nice!". "Shigo daga ciki mana...." "Aa bazamane ya kawo niba, daman nazone nasanar daku gobe-gobe nakeson Bahijjah ta dawo gidan mijinta tunda ta cika arba’in!" Tayi magana cikin gadara se Ummah ta kalleta da mamaki "Gobe-gobe fa kikace sahiyya?"
"Eh gobe fa, dan bansan zaman da takeyi ba tunda tayi arba’in zaman gidan ya isa tadawo gidanta dan nagaji da dana yana ciyarda kartin wai da sunan tana zaman jego!" Tana magana tana jujjuya baki da ido irin na rashin mutuncinnan.
"Toh Sahiyya Allah yakaimu gobe lafia...." "Ameen inda gaske kike, to ina ita Bahijjar bazatazo ta gaida ni ba?"
"Batanan taje yawon arba’in gidan kawunta taje ta gaida su!" "Hmmmm aini nasan arina daman yawon taso ta zauna tayi to bazata sabo ba bindiga a ruwa, to a daiyi hanzari a dawo gobe naga ta karshen yawo!" Tana tafiya sannan tana daga murya ita kuma Ummah tana binta da ido.

Kaddarar RayuwaWhere stories live. Discover now