CHAPTER 1

1.1K 63 3
                                    

💦💦💦💦💦💦💦💦💦
           *MATAR UBA*
💦💦💦💦💦💦💦💦💦
       _(A True Life Story_ )
            *Short story*
'''Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)'''
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️
_('Kungiya d'aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA*  Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK*  much Love.

'''CHAPTER 1'''
Zaune na gansu a Kan sallaya da alama sun idar da sallah ne. Yara ne Mata Wanda baza su haura shekaru Sha hud'u a duniya ba.

Bangaje kofar tayi ta shigo tana huci Tace "Ke Asiya don ubanki Ni sa'ar kice da d'azu mijina Yana min magana Kika sa Mana  Baki?"
Wacce aka Kira da Asiya sai rarraba Ido take ta kasa cewa komai idanun ta sun yi jajir cike da tsoro da fargaban abinda zata Mata,finciko ta tayi tana jaaan kunnen ta Tace "Daga yau idan Ina magana da mijina Wanda ya auro Ni a matsayin matar sa Yana min magana Kika sa min summan Bakin ki" tana maganar tana Jan bakin ta.
"Kar na Kuma ji ko gani kin fad'a Masa cewar bana kyauta ta muku kina jina?" chan Ciki ta amsa da "Eh" maruka masu kyau ta shafa Mata sannan Tace "Kice Ni yar banzar yarinya ce" cikin kuka Tace "Ni Yar banzar yarinya ce" hankad'e ta tayi ta fad'a a kan gado, da sauri ta karaso inda take tana kokarin d'aga ta.
"To Munafuka Meyasa kike rike ta da alama Kema Marin kike bukata,kina hauka ne? Da nice na haifi kamar biri kamar ku da na dad'e da kashe ku" ba b'ata lokaci ita ma ta karb'i nata marukan guda biyu.
"Mahaukatan banza mtwwws" sai tayi ficewar ta.

"Anisah ki daina kuka kinji? Inda sabo ai mun Saba,tashi mu cigaba da addu'ar mu" hannu ta sa ta sharewa kanwar ta hawaye sannan suka koma suka zauna a Akan sallaya, Anisa ce ta d'aga hannu sama Tace "Ya Allah Kaine Allah ka ga abinda matar uban mu take Mana ya Allah ka Kare mu daga sharriin ta" anisah ta amsa da ameen.
Tashi sukayi, sukayi addu'ar bacci sannan suka kwanta.

*WASHE GARI*
Zaune take a parlor tana kallon TV hannun ta rike yake da remote ko me ta tuna sai ji nayi ta kwala Kiran sunan "Anisah!!! Asiyah" shiru ba su amsa ba ta sake Kiran sunan su a Karo na biyu jiki a sanyaye suka fito jikin su a sanye yake da Riga da Wando jeans yayi matukar karb'an su sannan ko Wacce tasa ribbon kalar rigan ta tayi parking gashin ta, sunaa da tsawon gashi, gashi Baki Kirin.

Zuwa sukayi suka tsaya a gefen ta, kallon su ta Shiga yi daga sama har kasa sannan tace "Bakin ku ciwo yake da Kuna ji Ina Kiran Ku baku amsa ba, maza kuyi kneel down Ni sa'ar kuce da za ku Zo ku tsaya min a Kai?" Ba musu sukayi kneel down.

Tsaki tayi Tace "Daga gani cikin ku biyun Nan akwai mayya" tana nuna su da Yar yatsan ta akwai Wacce take kawo Mana matsala a gidan na rashin kud'i gashi Kun sa mun Fara Shiga talauci, ko kud'in da mijina yake kashewa a makarantar ku ma ai asara ce ban ga amfanin ta ba sabida haka na yanke shawara daga yau Kun daina makaranta a gidan Kar ku kuskura naji Kun ambaci sunan makaranta ko da dawasane" ganin tayi shiru suka tashi a tsawace Tace "Don uwar ku wa ya ce ku tashi maza ku koma kneel down, raise up your hands and close your eyes" a tsorace sukayi yanda tace sun dad'e a haka Kan tace "babu abinda kuka iya sai Kama gashi da ribbon zan Baku shawara gara ma kuje ku koyi sana'ar d'inki ko salloon Yan iskan Yara kawaii tashi ku bani guri" cikin sauri suka Mike suka bar gun.

Bayan Mahaifin su ya dawo daga aiki Yana zaune a parlor suka shigo suka tsaya a gaban TV idan ya karkata kansa sai su tare sunyi hakan kusan sau uku sannan yayi Murmushi yace "To naji naji me Daddy yayi wa little angels d'insa Kuma wanna karon?"
Anisah Tace "Daddy Meyasa kace zaka cire mu a makaranta?"
Kallon su yayi d'aya bayan d'aya sannan yace "Na cire ku a makaranta? Me zai Sa na cire ku a makaranta?"
Asiyah Tace "Mummy ce tace Mana za'a cire mu a makaranta"
Cikin rashin fahimta yace "Meyasa?"
Anisah Tace "Cewa tayi babu kud'i Yanzu ana cikin marra"
Murmushin gefen baki yayi yace "Haba duk talauci na bazan ki saku a makaranta ba Kuma Alhamdulillah muna ci muna Sha babu abunda muka rasa, maybe mummyn naku Wasa take muku ko Kuma Bata San me take fad'a ba"

Anisah Tace "Allah yasa dai bata San me take cewa bane" ta Maida kallon ga Asiya Tace "Asiyah Zo mu tafi" d'akin su suka haura suka barshi zaune Baki a bud'e yace "Ikon Allah, wato dai Baraka baza ta canza ba" Kiran Sa akayi a waya Yana wayar ya haura saman su inda ya Samu tana zaune gaban mirror tana taje gashin kanta jikinta Kuma sanye yake da sleeping dress iya gwiwa yellow ne aka Masa flowers da jaan color, sai da ya gama wayar da yake sannan tace "Naji kana maganar tafiya"
Murmushi yayi yace "Eh tafiya xanyi zuwa London next week insha Allah"
"Masha Allah tare zamu tafi ko?"
Yar karamar dariya yayi yace "tafiyar Nan na office ne Kuma sai naje dake? Idan na tafi dake wa zai kula da yaran?"

Tashi tayi a tsawace Tace "Ni fa matar kace ba baiwar su ba, ko Kuma ka auro Ni ne don na Zama baiwar su?"
"Haba Baraka Kar ki manta Kan na auro ki kin San da zaman su Kuma kin tabbatar min da ba matsala Zaki kula dasu Amma Yanzu kiji abinda kike cewa 'ya 'yan ki ne fa?"

A tsawace Tace " 'ya 'yan ka dai zaman ka nakeyi ba nasu ba ka gane ko? Kuma da kake cewa sai da na amince Kan akayi auren do you expect me to refuse your proposal?"
"No no Baraka ba haka nake nufi ba" wayar ta tasa hannun ta d'auka sannan ta nufi hanyar fita Tace "Sai Kuma kayi ai."

"Baraka!! Baraka!!!" Bata tsaya ba bare ta saurare shi.
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
Please Vote and comment.
MATAR UBA KENAN KAD'AN DAGA CIKIN CHAKWAKIYAR DAKE CIKIN LABARIN ASIYA DA ANISAH.

Sai na ga Ruwan Comments zan cigaba
MILHAAT CE
YAR TERAWA

MATAR UBA 2021(A TRUE LIFE STORY OF ASIYAH)Where stories live. Discover now