CHAPTER 32

281 23 11
                                    

Hannun Baraka tayi da sauri ganin tana kokarin kallon abinda take kalli. Tace "Muje ko?"
Ba ta jira amsarta ba taja ta suka fita.
💦💦💦💦💦💦💦💦
........... Baraka motarta ta shiga itama Nana ta shiga motar ta, barakace ta fara fita Nana ta bi bayanta,sai da ta bari Baraka tayi nisa tayi reverse ta dawo gidan, parkour ta zarce Kai tsaye a hango Asiyah ta had'a kai da gwiwa tana kuka, da sauri ta nufi inda take hannunta ta riko suka shige d'akinta Asiyah Rungumar tayi ta Bud'e sabon shafin kuka,cike da tausayi Nana take rarrashin ta zaunar da ita tayi Tace

"Dole kiyi kuka Asiyah Ni kaina na daure ne don Kar aikin da muke ya lalace Amma ina so ki sa a  ranki asirin Baraka ya kusa tonawa insha Allah Nan ba da dad'ewa ba"

"Allah yasa, na tsane ta na tsane ta inda za a bani wuka wallahi sai na yanka ta gunduwa gunduwa"
" Kar ki damu kinji yanzu Ni zan tafi Kar ta dawo ta tarar Dani a nan don na ga alama ta fara zargina"
Tashi tayi ta fita , Asiyah ta Mata godiya Nana Tace "Shine kad'ai hanyar da iya zan wanke laifina Kar ki damu" ta Mike ta fita tana Isa kofar parlour tasa hannu zata Bud'e taji an turo kofar d'an jaa da baya tayi ga mamakin ta taga Baraka na tsaye na cin chingam.

Eye glass 'din dake fuskar ta, ta cire kallon Nana take cike da mamaki Tace "Lafiya naga kin dawo?"
Murya na rawa Tace "Am......ammmm wayata...."

"Wayar ki?"
",Eh wayata na manta gata nan na 'dauko"
Ta nuna Mata wayar da ta zaro a jaka.

Tace "Ke me Kika dawo yi?"
"naga kin dawone shiyasa nace bari nazo na duba ki ko Lafiya"
" Oh ayya wayata na manta"
"alright naga ma kin bar motar ki a waje"
" Eh dake bana son na shigo na yi tasa Mai gadi Bud'ewa da rufewa"
"Kya jiki da wani magana ba aikinsa ba kenan? Kud'i nake biyan sa fa"
"Hmm duk da hakan ba dad'i ai"

"Kanki a ke ji, gara ke nikam bari na tafi Yana chan yana jirana sai faman kirana yake"
"To a dawo Lafiya"
"Ameen,Amma kawata zan so had'aki da mutumin nan, ya iya sarrafa mace,gashi abun......"

Dariya Nana tayi tace "Baki dama" ta wuce abinda ta,tana shiga mota gida ta zarce direct ita Kuma gogar taku ta wuce hotel d'in da shaid'anin nata ke jiranta.

Hashim taimakon gaggawa a ka basa, idan ya farka sai ya Kuma Suma a haka ya kwana har garin Allah ya waye,likitan dake kansa ne ya fito ya nufi inda mom take "Kece kikawo sa?"
Tashi tayi jikina rawa tace "Eh nice?"
"Amma me ke damun sane naga Yana cikin tashin hankalin"
"Babu" kawai Tace Masa Kai a kasa kamar yaso ya gane abinda ke faruwa yace "well rayuwar sa tana cikin had'ari inaga akwai labarin da yaji ne Wanda ya tada Masa hankali, Amma idan kin San abinda yake bukata a Masa shi cikin gaggawa if not......" Sai Kuma ya yi Shiru.

Tace "If not what Dr?"
" Zamu iya rasa shi, zuciyar sa zata iya bugawa"
" Innalillahi wa Inna lillahir raji'un, zan iya ganin sa?"
"A a tukunna sabida har yanzu bai farfad'o ba kiyi abinda nace" Yana Kai Nan ya koma d'akin da Hashim yake.

Asiyah sai da tayi kuka Mai isarta ta d'auko wayar ta tayi dialling number Hashim, sau uku ta Kira but no answer, tana ajiye wayar ta kwanta ruf da ciki ta cigaba da raira kukan ta.  Tana Jin wayarta ya Fara ringing tayi saurin d'ago kanta hannu tasa ta d'auko wayan Yar karamar tsaki tayi,tayi picking da "Hello Aunty Diyya!!!
"Asiyah Dan allah kunyi waya da Hashim?"
"A'a tun jiya rabona dashi,yanzu ma na Kira Bai d'aga ba"
" Nima haka baya d'aga kirana"
" Allah yasa dai Lafiya"
Diyya ta amsa da "Ameen, idan naji wani labarin zan Kira ki na Sanar dake"
"To insha Allah nima naji zan Kira ki"
A tare suka kashe wayar.

Kwankwasa kofar ta taji anyi ta taso ta Bud'e turo Baki Safiyya tayi Tace "Asiyah!!!
Wani irin kallon da ta matane yasa Tace " Aunty Asiyah,Dan Allah kunyi magana da hashim?"
"A a lafjyay?"
"ba Lafiya ba tun jiya da ya bar Nan ban sake ji daga gare shi ba,shine nace Bari na tambaye ki"
" Hmm a a ban San komai Akan hakan ba"
Ta juya ta turo kofarta ta bar Safiyya a  tsaye,tausayin Safiyyar take ji Amma ita kanta tayi mamakin yanda har Safiyya yace ta Mata magana da sanyin murya ko dai dukan da ta matane yasa ta shiga taitayinta, wata zuciyar Tace a a ai yau bata Sha maganin ba tunda kin zubar, Murmushi tayi Tace "Insha Allah zna sa Ido Akanki,bazan Bari Safiyya ta sake Shan maganin Nan ba."

MATAR UBA 2021(A TRUE LIFE STORY OF ASIYAH)Where stories live. Discover now