CHAPTER 17

205 24 2
                                    


NOT EDITED
CHAPTER 17

cikin muryar kuka yake magana "Nana Ni? Ni zakiyi wa haka yau ke na Kaka red handed da wuni turmi da tarb'arya kin cuceni Nana, Allah ya Isa tsakani na dake" Banda kuka babu abinda da take yi, ganin bokan na kokarin guduwa ya cukumo shi ya fara na d'a Masa na jaki ran Soja ya b'aci sanda ya had'a Masa jini da majina ya kyale a tsawace yace "Ke kuka wuce mu tafi" jiki na rawa ta fice daga bukkar da gudu ta Shiga motar ta ta nufi gida Shima ya bi bayanta.
💦💦💦💦💦💦💦💦
.......... Nana na isa gida Kai tsaye bed room d'inta ta nufa, a kusuwar d'akin ta rakub'e ta zauna sai aikin kuka take.

Baban Yesmin na shigow parlor bai ganta ba hakan yasa ya haura sama don ya tabbata tana parlor, Yana shiga d'akin yana ganin ta sai yaji tausayin ta ya Kama shi, tabbas so makahone Zama yayi a bakin gado ya had'a Kai da gwiwa ya rasa me yake masa dad'i, babu Wanda yace was d'an uwansa komai sun dad'e a Haka kana yayi ajiyar zuciya yace "Nana kin cuce Ni, kin zalunce Ni kin ci amanta, me na Miki da na chanchanci it  wannan cin mutuncin, ke wace irin jarrababbiyace ina sane da duk Abubuwan da kike yi, jiya kin Kwana da wani da safen Nan ya tafi hakan Bai ishe ki ba Kika koma gun boka kazami, Kai ya Salam, Allahumma ajirni fii musibati, wannan masifa da me tayi Kama?" Ya karasa maganar Yana share hawayen da ke zubo masa.

Cikin kuka tace "Dan Allah kayi hakuri ka yafe min nasan ban chanchanci yafiyar ka ba amma Dan Allah ko don Yesmin...."

A tsawace yace "Yesmin? Da kin San da ita ne kike iskancin ki har cikin gida? Ke Baki ji tsoron Kar wataran ta ganki ba me zaki ce mata in ta ganki kina aikata wannan mumu Nan aikin?"
Kasa cewa komai tayi sai aikin kuka take ta dad'e tana kuka yayin da shi Kuma Yana jin zafin kukan nata sabida Yana son matar sa sosai, chan Ciki Tace "Abban Yesmin kayi hakuri wallahii bazan sake ba Amma Ina so late sani Nima ba yin kaina bane, Abban Yesmin kayi guje Ni ka fifita aikin ka a kaina yau kimanin wata shida Kenan ban sa ka a Idona ba, bayan kasan cewa ba ci da Sha da tufatarwa bane kad'ai hakkina Akan ka, Kuma ka hanani zuwa inda kake,  kasanni Ni Wace irin mace ce Amma ko kad'an baka tausayi na... " Kuka ne ya kwace Mata ta kasa karasa maganar.

Maganar Abokin sa Ameenu ya tuna tabbas shine silar halin da ta Shiga ko da ace tana da laifi to nashi yafi yawa, cikin murya Mai sanyi ya ambaci sunan ta "Nana Khadija" a hankali ta d'ago kanta sukayi Ido had'u Murmushin takaici yayi yace "Kinyi gaskiya laifi nane Amma ki koma ga Allah ki ruki gafarar sa sabida Zina babban zunubi ne, da auren ki kike zina" shiru ya d'an kananya d'aura da fad'in " Bazan rabu da Ke ba sabida ina kaunar ki Nana, auren Soyayya mukayi sannan idan Yan gidan mu sukaji abinda kikayi har ya Kai ga mun rabu zasu min dariya, ke Kanki kin San irin wahalar da nasha Kan mukayi auren Nan, sabida Haka na yanke shawara zamu koma Kaduna da Zama ki Sanar da Yesmin ki Fara Shiri" tashi yayi har ya bud'e kofa sai ya juyo yace "ki shirya muje asibiti sanadiyar tashin hankalin da na Shiga d'azu na buge wani yanzu haka Yana asibiti Rai a hannun Allah."
Yana Kai Nan ya fita.

Nana tayi matukar da na sani har sai da taji ta tausayawa kanta har da shi mijin nata, ajiyar zuciya tayi ta d'aga hannun ta sama Tace "Ya Allah nagode maka da aka azurtani da miji irin Isah, ya Allah ka gafartamin" tana Kai Nan ta mike ta Shiga ban d'aki ta watsa ruwa ta tarar dashi a mota Yana jiran ta, Basu zarce ko ina ba sai asibiti, bayan sun Isa Kai tsaye d'akin da baba Mai gadi yake suka nufa har yanzu dai bai farka ba, hankali a tashe ya Shiga office d'in Dr, Dr ya tabbatar Masa da zai tashi ya kwantar da hankalin sa, zuwa yayi ya biya kud'in magani sannan suka soma d'akin da yake, shiru yayi baice komai Nana ce Tace "Abban Yesmin tunda Yana bacci me zai Hana mu koma gida sai mu turo Mairo tazo ta Rika kula dashi, Ina ga kamar barin shi, shi kad'ai abun baiyi tsari ba"

" Eh hakan za'ayi"
" Amma ya Naga Banga ciwon da yaji ba?"
" Eh dake ya juya Mana baya ne, ki koma ta gaban sa Zaki ga ciwon da yaji"

" A'a ba sai na duba ba, Allah ya bashi lafiya" ya amsa da "ameen, mu tafi ko? in ya so anjima mairon sai ta dawo"

MATAR UBA 2021(A TRUE LIFE STORY OF ASIYAH)Where stories live. Discover now