CHAPTER 3

386 30 2
                                    

CHAPTER 3
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
............ "Maza ku daina kallo na ku wuce ku cire uniform d'in Nan kusa wani Kaya, kun tsaya Kuna kallo na da ido kamar na mayu."

Ba musu suka haura sama Tace "Minti biyu na Baku ku kifo Kar ku wuce Nan, Wai mummy zamuje makaranta da wani kud'i za a biya muku? Mtssws" bayan sun fito ne ta d'aura musu talla.

Sun dad'e a yawon tallaan sai wajen karfe uku suka dawo gida.

Karb'an kud'in tayi Tace "Masha Allah Ashe Kuna da amfani" Nan ta Shiga irga kud'in sai taga naira hamsin da bakin sa ya d'an gutsire ta kalli kud'in dakyau Tace "Toh wannan Kuma waya cinye?"
Basu ce mata komai ba sai kallon junan su kawaii suke.

Tace "banda rashin hankali ma Kuna ganin kud'i ba kyau ku karb'a, ku Shiga Ciki Ku huta,idan Allah ya kaimu gobe tunda Kun sayar da wannan duka zamu sayo wasu"
Kallon Juna suka yi cikin Rawar murya Asiyah Tace "Mummy yunwa muke ji"
"Yunwa kuke ji?"
A tare suka amsa da "Eh yunwa muke ji"
Gyara Zama tayi Tace "Kuna nufin yunwa yunwa na cin abinci?"
Suka amsa da Eh.
Langwabe Kai tayi Tace "Allah sarki kun ga abin da nake fad'a muku Kenan Nima tun jiya banci komai ba"

Anisah Tace "mummy na kasa fahimtar abinda ke faruwa mun talauce ne ko me?"
Yar karamar dariya tayi Tace "Eh mun talauce Amma Alhamdulillah tunda muna raye, to yanzu ya zamuyi Kenan tunda Kuna Jin yunwa?"

Kallon ta kawaii suke suna rarraba idanu, Murmushi tayi ta sa hannu ta d'auko naira hamsin d'in Nan da ya yage tace "me wannan zai saya Mana muci tunda Allah ya had'a Ni da monkeys?"

Anisah Tace "Mummy Dan Allah ki Kira Daddy muyi magana dashi"
Tashi tayi Tace "Kina nufin na Kira mijina? Baku girma bane ta yanda zaku Rika fita Kuna neman kud'in da zakuci abinci? Wato na Kira shi?" tana maganar tana nuna kanta.
"Eh please call our Daddy he promise us that we will never lack anything"

A tsawace Tace "would you shut up your dirty mouth,I should call him kuce Masa me? Idan Kika kuskura Kika sake fad'a min magana makamanciyar wannan Anisah sai na karya ki"

Anisah Tace "But mummy..."
Katse ta tayi a tsawace tace "Get out from here useless children" tana maganar had'e da ture robobin da suka dawo dashi.

"Ku d'auki robobin Nan ku fice min daga gani"
A tsorace suka bar pallon.

A garden na gidan suka zauna Asiyah Tace "Anisah Dan Allah na roke ki wata alfarma?  ya kamata ki daina tan kamata idan tana magana"
"Meyasa kikace haka?"
"Sabida zata kashe mu wataran idan Kika cigaba da Mata Haka"

Murmushi tayi Tace "To Asiyah me banbanci mu da matattu, ba abinci, ba zuwa makaranta muke ba, ba kayan sawa kin San duk ta Kona Mana su,ba Uwa ba uba, har yaran da suke gidan marayu sun fimu da komai, to me Kuma ya rage? A raye muke dai Amma ta kashe mu"

"Na San da hakan Anisah Amma ya kamata ki d'auki magana ta Kinga nice gaba dake ko?"
"To shikenan zanyi yanda kikace"

Asiyah tashi tayi tace "Yauwa ko kefa Tashi muje muyi sallah muyi Shirin zuwa islamiyya"
"Gaskiya ni bazanje ba jiri ma nake ji Ina sallah zanyi bacci"
"To shikenan Nima baccin zanyi kawai."

Ganin ta nayi ta fito daga kitchen hannun ta rike yake da plate, fried rice ne aciki da cinyoyin kaji manya manya, d'ayan hannun Kuma kwalin Hollandia ne, Kai tsaye dinning table ta nufa tana ajiye plate d'in wayan ta ya Fara ringing tana picking ta amsa da "Hello qawata"

Bayan sun gaisa Tace "Ke dai Bari kawai qawata nayi duk yanda zanyi Amma shiru kike ji na rasa meyasa ban haihu ba sai faman bauta nake wa yan iskan yaran Nan."

Tana d'an yi shiru da alama tana Mata magana Wanda Ni na kasa ji sai ji nayi Tace "Ai wallahi Ina haihuwa Zan Kori monkeys d'in Nan a gida na, Kema kin sanni ai wallahi ba ruwana da inda zasu je suma mutu Mana"

MATAR UBA 2021(A TRUE LIFE STORY OF ASIYAH)Where stories live. Discover now