Kidnap

435 40 5
                                    

THE NEW EMIR

_Wattpad *Nimcyluv*_

*_@Telegram_*
https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ

5-6


Shuru Mai martaba Khalid yay,yana auna maganganun boka,shi yanzu a ra'ayinsa baya da wani buri na kasan cewa da ƴar mace balle under age mai ƙarancin shekaru,mai ma zai ɗauka a jikinta for God sake? Shi yanzu bashi da buri daya huce ya ingata rayuwar Lil prince,ya zama mai ƙarfin mulki da isa da gadara haɗi da izza,maganarsa ta zama kamar umarnice wa talakawansa,wannan shine hope ɗinsa  a kan Lil prince,shurun da yayi ne yasa Boka ƙara mai²ta masa abinda yace,cikin gajiyawa da maganar bokan ya ɗaga idanunsa da suka soma jaa sbd yadda tsotsotsar ta fara masa aiki,a gajiye yace "What about Lil prince? Ina tunanin wannan aikin dashi ya dace ba wani ba?"ya faɗa yana karkarwa sbd yadda yaji kansa ya fara juyawa hakan kuma shine alamun nasarar aikin.

Rubuce² Boka yay saman allon tsafinsa kana ya dubi Mai martaba yace "aƙwai matsala babba,bana da ikon yiwa Lil prnce aiki a yanzu saiya gama mallakar ƴan mata guda ashirin kamar yadda yake a tsari,dan aljanin dake shanyen jinin matan shine mai akula da prince kuma bai idda shan jinin ba kamar yadda ya buƙata,babban abuma shine kaine a kan karagar mulki bashi ba,so dole wannan aikin naka ne,amma yana da sharaɗi"ya ƙare maganar yana ɗauko wata gawar mahauniya wacce aka jiƙa jikin jini kana ya cilla cikin wuta.

Jinjina kai Mai martaba yay tare da gyaran murya hakan ya tabbatarwa da Boka Mai martaba Khalid ya amshi ƙudurinsa kamar yadda yake buƙata,saida ya kammala komai na aikin sannan yace "Sharaɗin ba'a faɗarsa, kawai dai ka kiyaye da wannan yarinyar da zaka samo"ya faɗa yana shigewa cikin wani kurmin ɗaki mai duhun gaske,Mai martaba yaywa alama da  hannu akan ya shigo,miƙewa yay tare da  fara tafiya,yana shiga suka rufe ƙofa,wajan 3mins na jiyo surutansu sama² da kuma ihu²😱komai suke aikatawa uhuu,saida suka kammala abinda suke kana suka fito fuskar Mai martaba cike da farin ciki da alama dai aƙwai abinda akai masa wanda shima yake buƙatarsa,cikin nutsuwa ya sanya kayansa ya koma Sarkinsa sak komai na kamala ya fito,idan kaga Sarki Khalid ba zaka taɓa cewa zai aikata wani abu na saɓon Ubangiji ba,bai fiye fitowa a asalin colour ɗinsa ba,yana ɓoye mummunan habit ɗinsa sannan ya bayyana good habit ɗinsa,wannan halin duk cikin iya takune dan haka da wahala ka fahimci yana aikata mummunan abu,sai wanda suke good tym dashi.

N.S Quest Place
Shine Hotel ɗin da suka sauka cikinsa,Hotel ne mai ƙyan gske kuma da tsari sosai manyan masu kuɗi suke sauka cikinsa,room 123 shine na Mai martaba,124 kuma na Lil prince sauran rooms ɗin na amintattun Sarki da suka taho tare,daman alrdy pilto yay tafiyarsa sai gari ya hawaye zai dawo.

Yana zaune a kishin giɗe yana kallon new a B.B.C Lil prince ya turo ƙofar ɗakin hotel ɗin ya shigo,zama kusa da mahaifin nasa yay cikin girmamawa yace "Allah ya ƙara maka yawan rai da ƙwana ya mahaifina,wata buƙata gareni idan an bani damar faɗa?"

Gyara zama Mai martaba yay tare da maida hankalinsa kan Lil prince yana fatan ace ba wata babbar matsala bace take damun yaron nasa,cikin tausassiyar murya Mai martaba yace"Haba magaji matsalanku ai tamu ce,faɗi ina jinka"murmushin  jin daɗi Lil prince yay yace " Allah ya taimaki Sarki ina buƙatar kuɗi masu yawa sbd nayiwa friend ɗina ƙyautar motar as her birthday gift,Papa wallahi Heroine naji dani sosai kuma naga tana mutuwar son mota Bugatti  shine nakeso nai mata gift da ita"

Girgiza kai Mai martaba yay cike da farin ciki yace "ba wani abu za kaga alert anjima shikenan?"ya tambaya cike da ƙaunar ɗan nasa mafi soyowa cikin ransa da zuciyarsa,dariya Lil prince yay tare da hugging mahaifin nasa yace "Thank you soo much Papa heroine na gdy ƙwarai"bayansa ya ɗan bubbuga yace "it ok,Magaji meye tunaninka ga wannan hotel ɗin?"shuru Prince yay dan baiyi wani tunani ba,"i don't think anything kawai dai yay ƙyau sunsan aikinsu"nisawa Mai martaba yay yace "ni ina da ra'ayin gina irinsa a garin Bilhas"ɗan waro idanu Lil prince yay tare da faɗin "but ina zaa samu babban fili cikin jama'a haka?"wani shu'umin murmushi Mai martaba yay yace "muke da gari fa,zanwa Governor  magana akan babban filin da wani malami ke buƙata zai gina makarantar ismaliya so gwamma ni na amfana dashi tunda harka ake ta kuɗi"jinjina kai Prince yay yace "amma makarantar fa ya...'✋🏼ɗaga masa hannun da Mai martaba yay ya sashi yin shuru dan haka yay masa Goodnight ya fice a ɗakin shime shirin ƙwanciya yay domin yana buƙatar magana da shugaban sujoji yana buƙatar a bashi mai kula da lafiyarsa data Prince da wannan tunanin ya ƙwanta bacci.



The New EmirWhere stories live. Discover now