die

989 37 15
                                    

THE NEW EMIR

*WRITING BY*
*AUNTY NI'EEMAEH*

  NIMCYLUV🤏🏼🔥


*17-18*

ALLAHAMDULILLAH KAMAR YADDA NAYI ALKWARIN ƘARA *FREE PAGE* GA SHINAN NA ƘARA HAR PAGE GUDA UKU KUMA A WANNAN ZAN TSAYA DUKKAN MAI BUƘATA YAJI SHIN *ZAITUN* MUTUWA TAYI KO KUMA TSAFI AKAI DA ITA? YAYA BATUN *SEENAT* DA GASKE ALJANA TAZU ƊAUKAR MATA FANSAR ABINDA *LIL PRINCE* YAYI MATA? 😱😱TURƘASHI A INA *LIL PRINCE* YA SANYA HANNUNSA? WANNAN AMSAR TANA PAID GRP KADA KA BARI ANYI BABU KAI DOMIN TAFIYAR YANZUN AKA FARA SAI NA JIKU MASOYAN AMANA😍

_THE NEW EMIR IS FOR SALE PAY BEFORE YOU READ🤟🏼HOW TO SUBSCRIBE 200 FOR NRML GRP,AND 500 FOR VIP GRP WANDA ZASU SAMU DUKA LITTAFAINA DANA RUBUTA NA KUƊI DA KUMA PROGRAMS ƊIN DA ZAMU FARA GABATARWA NA MARA😍ACCOUT NO 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BAN,PROOF OF PAYMENT SEND IT TO MY WASAPP NO 08119237616 KODA KUƊINKA SAIDA RABONKA IDAN BA SIYA ZAKAI BA PLS KADA KAYIMIN MAGANA😂🤏🏼_

Gaba ɗaya Fadawanne suka tsaya suna kallonsa cike da mamakin tsawar da yayi masu,tsawar dako  Lil prince bai taɓa yi masu ita ba,tsayawa Prince yay tare da harɗe hannayensa yana jiran ƙarasuwar Saifu,Cikin taƙama da izza Saifu yake takawa zuwa gabansa,wata irin tafiya yake tamƙar ɗawisu ya zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa,yana ƙarasawa wajansu yaja ya tsaya kana yaja numfashi tare da lumshe idanunsa few minutes ya ware saman fuskar Kulsum wacce ke zube gabansu tana kuka tamkar ranta zai fita,taɓe baki yay tare da ɗauke kai daga kallonta,gyara tsaiwarsa yay tare dajan ma dai²cin gemunsa yace.

"Wannan fa?"ya tambaya yana mai ƙawar da kansa daga kallonsu tamkar bashine yayi maganar ba,daga bayansa yaji ance "nine ya kamata ka tambaya basu ba"juyawa yayi ya kalli Lil prince wanda ya ƙarasa maganar cikin ɓacin rai,wani shegen murmushin gefen baki Saifu yay wanda ya haddasa lumawar beauty points ɗinsa tare da bayyanar gav teeth ɗinsa wacce take siririya,ɗauke kansa yay daga kallon Prince ba tare daya tankasa ba,gaba ɗaya hankalinsa ya mayar kan Fadawan yana jiran jin abinda zasu faɗa masa.

Wani ƙwarjinsa ne ya ninku a idanun Fadawan jikinsu na rawa suka faɗi ƙasa tare da faɗin "Umarnine daga magajin Mai martaba,ya nemi ta fito da *Kuyanga Zarina* amma taƙi kuma an tabbatar da itane ta ɓoyeta"suka ƙare maganar suna kallon Kulsum,cikin kuka Kuslum ta shiga faɗin.

"tabbas ɗazu naga Zarina lkcn dana fitowa daga sashin wannan mutumin daga nan taje ɓangaren Zaitun a nan na fita na barsu"ta faɗa tana sharce majinar data silalo ta cikin hancin sbd tsabar kuka.

Waro manyan idanunsa Saifu yay tare da juyasu kaɗan wanda hakan ba ƙaramin ƙyau suka ƙarawa fuskarsa ba,cikin zazzaƙar muryarsa mai ɗauke da nutsuwa yace "Ni!?"ya faɗa yana mai ɗan ɗaga muryarsa,domin bai fahimci yarinyar da suke magana akanta ba,jinjina kai Kulsum tayi tace.

"eh! kai domin tun jiya muke nemanta bamu ganta ba,sbd ita baƙuwace a masarautar bilhas ba ko'ina ta sani ba,bayan gari ya waye nazu shiga sashinka domin kaima breakfast na haɗu da ita a hanya haka ya tabbatarmin da a wajanka ta ƙwana"

Wani baƙin cikine ya kama Lil prince,babu abinda ya ɗaga masa hankali wai a wajansa ta ƙwana,gaba ɗaya ya ruɗe tsantsar kishinta ya bayyana a kan fuskarsa,tabbas sai yanzu ya tabbatar ba ƙaramin so ya kewa yarinyar ba,son da baiyi tunanin zaiwa wata ƴar mace irinsa ba,son daya kejin zai iyayin komai a kanta haka nan zai iya hqr da komai a kan ya mallaketa,kasa cewa komai sai numfashi daya shiga saukewa,Saifu kam sai yanzu ya fahimci yarinyar da suke magana a kai,to ina taje ina ta sani a wajan,mai yasa ma ya barta ta fita tana cikin hali na neman taimako,mai yasa ya kasa tausayinta bare har yayi tunanin taimakonta kamar yadda ta buƙata,shurun da yayine,yasa Fadawan ci gaba da jan Kulsum suka bar wajan.

The New EmirWhere stories live. Discover now