TNE
*15-16*
_THE NEW EMIR IS FOR SALE PAY BEFORE YOU READ🤟🏼HOW TO SUBSCRIBE 200 FOR NRML GRP,AND 500 FOR VIP GRP WANDA ZASU SAMU DUKA LITTAFAINA DANA RUBUTA NA KUƊI,DA KUMA PROGRAMS ƊIN DA ZAMU FARA GABATARWA NA MATA😍,ACCOUT NO 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK,PROOF OF PAYMENT SEND IT TO MY WASAPP NO 08119237616 KUDA KUƊINKA SAIDA RABONKA😂🤏🏼_
Yalwataccen gashin kanta wanda ya bazu saman fuskarta,runtsa idanunsa yay lkcn da ƙyaƙƙyawar fuskarta ta bayyana garesa,cikin nayanin mamaki da kuma al'ajabi yace.
"Aljanata"ya faɗa yana zuba mata idanunsu wanda suka soma juyawa zuwa jaa,ya kasa kasgatawa cewa ita ya gani hakan yana nufin ita ɗin mutunce ba aljana ba kamar yadda yay tunani a farko,a hankali ya ƙorawa ring ɗin hannunta idanu wanda ya haske masa idanu sbd sheƙin da yake,ƙara durƙushewa yay saman carpert ɗin tare da kamo hannunta ya haɗa da nasa wanda ring ɗin ke manne a jiki,wani ƙyaƙƙyawan haske ne ya haɗu waje guda sbd haɗuwar rings ɗin waje guda,cikin yanayin tsoro ya saki hannunta tare da miƙewa ya shiga takawa zuwa cikin bedroom ɗinsa,saukar daddaɗan muryarta cikin kunnansa ya sashi tsaya,tabbas itace hakan ya tabbatar masa cewa ita ɗin mutunce,mai yasa ta tsaya masa a rai?,mai yasa take zuwar masa cikin baccinsa?,mai yasa suke ɗauke da zobe iri ɗaya kuma a yatsa ɗaya? Jin cool voice ɗinta ba ƙaramin sauya masa tunani yay ba,tayi amfani da muryar tausayi rauni muryar ɗauke take da neman taimako,a ƙaro na biyu yaji ta ƙara faɗin.
"Please help me"ta ƙare maganar muryata na rawa alamar kuka gaf yake da ƙwace mata.
Yadda kansa ke juya masa yasa shi fara ganin wani duhu jiri ya fara ɗibansa,cikin nuni da shiɗin cikakken soja ne maiji da isasshiyar lpa da ƙuzari,ya saka hannunsa ya dafe kansa dake barazanar tarwatse,tsananin sara masa da kansa keyi masa ne ya sashi taune laɓɓansa,jarumtar dake garesa ya sashi soma takawa zuwa bedroom ɗinsa idanunsa rufe,ba tare daya saurareta ba ko kuma ya duba halin da take ciki ya shige bedroom ɗin tare da banko ƙofar da ƙarfi ya murza key.Zarina najin shigewarsa cikin ɗaki ta fashe da kuka zuciyarta na aiyana girman wulaƙancinsa,bashi da zuciyar imani da kuma tausayi,jikinta na rawa ta miƙewa tsaye a hankali ta soma takawa tare da niyar ficewa a sashin,zafin zazzaɓinta ne ya ƙaro lkcn da sassan jikinta suka fara amsar iskar da take kaɗawa a wajan masarutar,runtsa idanunta tayi tare da taune lips ɗinta,teeth ɗinta na haɗuwa waje guda suna bada wani sauti,a haka taci gaba da jan jikinta dan bata burin ci gaba da zama da mutum irin mara imani bare tausayi,tana fita sashin ta suka haɗu da Kuyanga Kulsum,cikin tashin hankali Kulsum ta kalli Zarina tace.
"Thank God you are fine,Zarina ina kika shige tun asuba muke nemanki shuru hankalinmu duk ya tashi?"zuba mata idanu kawai tayi ba tare data ce ƙala ba,sbd nauyin da zuciyarta tayi mata tamkar ansaka dutse an danne mata zuciya haka ta keji,wasu sabbin hawayene suka ƙara sauka daga cikin idanun Zarina su take tace wani abu amma ta gagara faɗa sbd nauyin da laɓɓanta sukai mata,gane hakan yasa Kulsum saurin kama hannunta wani tausayinta ya kamata,cikin muryar Kuka Kulsum tace.
"Mun shiga uku Zarina,wannan wacce irin rayuwa muke ciki ne haka?muna rayuwa kamar a bariki,muna rayuwa kamar prison wlh na gaji wannan abun yay yawa,ai mulki ba hauka bane,anci *ZARAFI* nmu ana nuna mana za'a iya komai damu da ƙarfin mulki,Zarina rayuwarki aƙwai matsala wlh damu dake duk muna cikin matsifa yanzu haka Mai martaba ne yaywa Zaitun faɗe gaba ɗaya bata gane komai banda sunanki babu abinda take faɗa,shine tun jiya nake bulayin nemanki amma babu ke sai yanzu da aka aikoni wajan Captain Saifu kawo masa breakfast na ganki,mene kike cikin ɗakinsa badai a can kika ƙwana ba?"Kulsum ta ƙarasa maganar cikin kuka da tsoro haɗi da firgici.
Kasa cewa komai Zarina tayi sai jikin Kulsum ta faɗa tana sakin kuka mai tsuma zuciyar dukkan mai saurare dama mai karatu,kukane wanda yake nuni da yankewar jin daɗin rayuwa,kukane wanda yake nuni da fidda rai dajin daɗi,kukane dake nuni inama Allah zai ɗauki raina na huta da wannan rayuwa,kuka ne dake nuni da zallar baƙin ciki damuwa ƙuncin zuciya,tabbas banda yazu a hadisi cewa idan mutum ya kashe kansa wuta ce masaukinsa babu shakka da ita da kanta zata kashe kanta,bata saba ba,bata san mene tashin hankali ba,tana jin kanta kamar wata sabuwar halitta sbd tension ɗin da take ciki,ganin kukan yayi yawa yasa Kulsum tsagaitawa da nata kukan ta shiga rarrashin Zarina,ƙara fashe Zarina tayi da kuka wanda hakan ya ƙara bawa zazzaɓin jikin damar ƙara ta'azzara,cikin Kuka tace.