_EPISODE ONE AND TWO_
shigowa gidan Hanne tayi a firgice kamar an je hota, idon Inna Asabe ya faɗa kanta, ko ba'a faɗa mata ba tasan yau inIinna Asabe ta kamata mai ƙwatarta sai ya shirya,
Kukan kura Inna Asabe tayi ta cakumo wuyar hijabin Hanne ta fara jibgarta kamar jaka, ihu Hanne ta ke yi da iya ƙarfinta tana neman taimako gashi Baffanta baya nan babu mai ceton ta sai Allah, Salima ce ta ɗauko wayar wuta mai ƙarfe ciki ita ma ta fara dukan Hanne har sa ida su ka ga tayi luɓus a lamun babu numfashi tartare da ita tukum Salima ta cema Inna Asabe su kyale ta haka nan ta jigata,
Tafiya su ka yi suka barta yashe a wajen bata ko numfashi,
Suna shiga cikin ɗaki suka kulle sannan Salima ta ɗauko ma Inna Asabe baƙar ladar da ta shigo da ita,
Washe baki Inna Asabe tayi tana faɗin "'ƴar albarka sannu da ƙoƙari yau ma Adamun ne ya baki ladar kenan?"
"Kedai buɗe kiga abinda ke ciki Innar mu basai kin tsaya tambaya ba kawai goge haƙoranki dashi,
Washe baki Inna Asabe tayi ganin lafiyayyar kaza mai miya ƙamshi sai tashi ya ke yi,
"Salima yanzu duk Adamun ne ya baki wannan, kiji yaron kirki wanda a ka haifeshi ƙuda na barci, ai irinsu a keso, ki buɗe kunnuwanki kiji abinda zan faɗa miki, karki tsaya sanya samarin yanzu sai ana haɗa musu da wayau tukum za'a ci abin hannunsu, dan haka kisan yadda za ki yi ki sami na ki,"
"Yo ke Innar mu in banda abinki in ban nemi na wa wajen samari ba mai zanyi? Ki bari kawai rayuwar nan ta zama bani gishiri in baka manɗa,"
Ta fawa su ka yi kamar ƙawaye tukum Inna Asabe ta fara cin namar kazar kamar tsohuwar mayya, saida taci mai isarta sannan ta suɗ'e hannu babu ko wanke wa ta ja barbaɗɗar tabar marta ta kwanta ta bar ma Salima gadon,
Sanyin Asuban dake hurowa ne yayi sanadiyyar farkawar Hanne daga doguwar suman da tayi, dagyar ta iya tashi daga inda take kwance ta daddafa ta shiga ɗakin ta, bata ko zauna ba ta jiyo kiran sallar Asubah, a daddafe ta gabatar da sallar asuba sannan ta koma ta kwanta saboda wani kalan zazzaɓi daya kawo mata farmaki, ga ciwon kai kamar kanta zai tsage gida biyu bakinta da fuskarta duk sun kumbura, ga zanen bulala nan ya fito ruɗu ruɗu a jikinta dake farace duk jikinta yayi jawur,
**********************************
Sai da gari ya waye yayi haske sosai tukum Baffan Hanne ya shigo gidan dan dama da anyi sallar isha inya fita gidan sai kuma da safe zai dawo saboda yana gadin gidan wani attajiri dake bayan gidan na shi mai suna Alhaji Ahmad maƙarfi, nan yake samun na kashe wa duk da albashin shi ba wani kuɗin zo a gani bane dubu biyar ne a wata, ɗ'akin Hanne ya shiga ya ganta lulluɓe da wani tsohun zanin gado ya sha wahala harya 'k
ƙoshi,bubbugata yayi ta buɗe idonta wanda sukai mata nauyi sosai, buɗe ɗaramin bakinta tayi da faɗin "ina kwana Baffa",
Kallonta Baffa yayi yana faɗin meke damunki Hannatu meya sameki haka?
Waro idanunta tayi waje sannan ta ri'ko hannunshi dukka biyu tana fad'in "kai baffa lafiyata 'kalau ba abinda ya sameni fa, dubeni dakyau Baffana", ta idashe maganar tana 'ka'karo murmushin 'karfin hali,
Da ido baffan ya bita yana sa'ke sa'ke a zuciyarshi tunani kala kala na zuwar masa Allah yayi miki albarka ya furta afili,
"Amiin Baffa kaje, ka kwanta nasan baka samu barci ba, kuma ka ga yanayin jikin ka sai ahankali ko?"
Mi'kewa Baffa yayi ya mata sallama tukum ya fito ya shige d'akin shi,WAIWAYE.
Waye malam mamuda?
Malam mamuda wato mahaifin hannatu cikakken bafulatani ne dan asalin jiyar taraba, karatune ya kawoshi garin kaduna lokacin befi shekara goma sha takwas ba, ananne allah ya had'ashi da me gidanshi alhaji shu'aibu shanono, bayan yakwashi shekaru agidan alhaji shu'aibu shanono ranar wata larabar da baze ta'ba mantawa ba, lokacin d'alibai sunyi hutu kowwa yadawo gida gaban mahaifinsa ananne ya had'u da babbar yarinyar alhaji shu'aibu shanono mesuna shafa'atu, gaba d'ayansu allah ya sanya soyayya mai 'karfi tsakaninsu wanda ita shafa'atun tasan wannan auren nasu bamai wuyawa bane saboda iyayenta karatu sukesu tayi mai zurfi sose amman soyayya ta rufe mata ido hartake ganin in akarabasu toh tabbas babu makawa mutuwa zatayi, shima wajen mamuda hakantake, tun iyayensu basu sanda maganar soyayyarsu ba hartakai ga sunsani amman kuma ansami babban akasi, dan sunce 'kwata 'kwata basu yarda da maganar ba ita 'yarsu karatu takeyi bazatai aure tun yanzu tana kasa kanta da kanta, itako shafa'atu soyayya ya rufe mata ido da hartake ganin indai aka 'kara rabasu awannan karon to tabbas guduwa zasuyi su tafi can wata uwa duniya ad'aura aurensu,

YOU ARE READING
RAMIN MUGUNTA
Misterio / Suspensolabari ne akan hassada keta da....... Ku biyoni dan jin abinda zai faru cikin littafin