END

2.6K 83 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
          *BARIKI*
     _Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Written by FENERH

*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby

69&70➡🔚

Alhmdulillah Anwatse taro lafiya yarage daga mai jego sai su mama hindatu da hajiya Aunty maryam ma ta nufi nata gidan ba karamin Alkhairi tasamu ba a wannan haihuwar daga Y'an uwa da Abokan arziki
Yaranta na samun kulawa sosai,  mama hindatu taso tafiya da Yasmin gida kodan rawar kafar da taga MA nayi kar suje su cutar da yara tunda Yasmin din ma batawa kanta fada Amma ya murzawa idon shi toka yace Sam ba inda za akaima i mata da yara dole suka hakura don har su baba aka fadama suyi mai magana baban zango ya hau fada "hindatu Al Ada ko addini kubar yarinya a dakin mijinta kici gaba da kula da ita in ta cika sati biyu ki tattaro kidawo tunda uwar mijinta na nan kuma tanasa ido,  baba ma ya yarda da maganar kanin shi dole hakan suka hakura,  tuni sun fara tsumata domin gyara hanyar da ya'ya uku suka fasa,  gyara suke mata na musamman harda hajiya ta gayyato wata y'ar Niger tazo ta fara gyara ta,  su hajiya sun sami lafiya domin sati daya da suna MA yaje jaji yin wani aiki na kusan wata daya,  ita kanta Yasmin taji dadin tafiyar don mugun tausayi yake bata don tasan halin kayanta mayenta ne idan suna kusa da juna baya iya hakuri,  don koranar da zaitafi saida ya latseta ciki da waje kafin ya wuce,

Sati biyu mama hindatu ta shirya komawa gidan ta Hajiya da kanta ta mata Alkhairi bare uban gayyar da ya bata dubu Dari harda zannuwa masu tsada itada mama kafin ya tafi yasmin ma ta kara musu,  saida tayi kuka saboda murna tace " nikam bana kishi da wainnan kishiyoyin gaskiya ga takwaran me gida ga kuma kuma kishiyar saurin kwarai Allah dai ya raya manasu akan sunnah,  hajiya tace Amen,  kamar karta tafi sukeji,  driver yakaita gida cikeda harkar arziki,  gida yarage daga hajiya sai masu aikin,  yaran sunyi bulbul dasu kyansu na kara Fitowa da wayau,  kullum sai sunyi waya da ubansu sama da goma yana tanbayar yaranshi, 

Yauma suna kwance a gefen hajiya itama tana zaune suna hira ya kira wayar ta  ta dauka tareda yin sallama,  Ajiyar zuciya ya sauke,  " baby ina kewarki fa kinsani gaskiya zanshigo,  " ga momy na zaune,  tayi saurin bawa hajiya wayar,  dariya yayi wato bazata iya Amsa mai ba tunda tana kusa da hajiya,  saida suka gama gaisawa kafin ta tashi ta fita,  "my beautiful wife say something are you missing me too?  "Sosai ma ai basai na fada ba,  ya dauke ne?  "Mene?  "Jinin.  "Aa ta "har yanzu?  Tree week's fa baby,  "idan ya dauke zanfada maka kazo ai nima ina kewar ka sosai mijina,  "tanks my wife, I love you ,  yana kashewa tace tab bangama hadewa ba nasan kana zuwa saika tsoma inkasan ina sallah,  dole intaimaki kaina ai don kana shiga kaji canji daraja ta zata iya raguwa,  sorry  zauji kainakewa tanaji,   ita kanta tasan tanashan gyara ga na HQ gana ciki duka y'ar Niger ke mata ga wani irin murjewa da takarayi tayi shar da ita,  tasan oga na ganinta zai rikice,

Saida suka kwashe sati uku cur kafin yasamu shigowa kaduna saboda wani couse sukeyi na karin girma ranar surprise yayi musu  suna baje a falon ta yaran na cikin gadajensu dake falon don baban ko ina ya Ajiye musu gadaje,  akwai a dakin shi akwai anata kuma,  Abulkhair ne kawai ke kan kafar hajiya,  " Fatima wannan me gidan sai kin dage akwai tsotso shiyasa yafisu karfi duk da shine karami,   "wallahi momy har ma kar dare yayi mai hakuri sai momy na ko Ihsan tana taba rigima,   dariya hajiya tayi tana mejin dadin yanda yasmin ke mata kara a KO ina tana kiranta Momyn ta  don haka take karajin sonta har cikin jinin ta,   

Ai da wuri zaki fara basu Abincin su bari baba yazo don ma kinada wadatar ruwan nonon da akwai damuwa shayarda ya'ya uku,  Sallamar shi ya katsesu tareda    zubamai ido cikeda mamakin ganin shi,   tunda ya iso ya zuba mata ido kamar baitaba ganinta ba don tayi kyau sosai cikin super din dake jikinta green ta zubo kana nan kalabarta a kafada tana daukar ido tayi wani irin cika mai burge duk wani namiji,  itama kallon shi takeyi yanda yayi kyau a cikin kakin kanshi ba hula sai boot dinshi dake sheki Alamar sabuntaka  yayi mata kyau sosai,  wurin mahaifiyar shi ya karaso tareda daukar yaron ya fara gaisheta,  " Sannu Hajiyar yasmin " yauwa mijin yasmin dina shigowar bazata Kayi mana?  "Wallahi momy bamu dade fa da gama waya dashi ba baifada min zai shigoba,   wani Abu kallo kawai yake aika mata don hajiya na wurin ne yasa  bai isa jikinta ya rungume taba,  bin ko ina na jikinta yakeyi da kallo kamar zai cinyeta duk dokin ganin yaran shi da yakeyi maman su ta daukemai hankali saida hajiya tace  kawoshi ni inshiga ciki  lokacin sallah yayi kar ya dameta don shi rigimamme ne,  mikewa yasmin tayi ta nufi kitchen  yabi bayanta da kallo tana juyamai kwakwal wa,  da gayya don tasan ya gama sumewa,  hajiya ta ganoshine tsab yasa ta basu wuri,   wani irin Y'ar yaji tsigar jikinshi na tashi  ya mike tareda leka fuskokin Y'an matan shi ya basu fake a kumatu " sorry my girls mom is calling yafada tareda nufar kitchen din cikin saurin shi,

         _*BARIKI*_ 👨‍✈ _Auren soja_👨‍✈   Where stories live. Discover now