part 51&52

2.6K 66 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
          *BARIKI*
     _Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Written by FENERH

*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby

51&52

Motocine guda shida aka ajiye musu sababbi dal suna sheki ta tsakiyar tasha Adon balloon  kana gani Kasan motar AMARYA ce ta fito tareda su Aunty Halima  driver ne ya bude mata ta shiga suka shiga sauran motocin,  BARIKI  suka nufa basu tsaya ko ina ba sai 2 batallion officers mess,  tundaga titin farko zakasan an kawata wurin sosai ga sojoji  tundaga farko baka ganin karshen su kowane sanyeda ceremonial dress sunyi matukar haska wurin ga fulawowi da aka watsa saman red carpet  suna tsayawa aka bude mata tafito wasu Y'an mata ne suka jero suna paret sanye da ceremonial dress na mata mai sket  su goma,  suka sata a tsakiyarsu gaba daya tafara rudewa don bata taba tunanin haka taron zai Kasan ceba,   ko ina shi uban gayyar yake oho?  Fushi ma takeyi dashi tunda rabon da ta sanya shi a ido tun ranarda yazo aka kirashi  saidai yakirata yaji lafiyar babyn shi ya kashe that's means ta tashi aiki ita tunda yasamu ciki a jikinta tana haihuwa kuma shikenan,  

Hango shi tayi yana takowa cikin nashi ceremonial dress din da yaji stars da igiyoyi dauke kuma da aninan shi da zasu Nuna maka he is the boss wata sandar girma ce a hannun shi yana dogarawa yayi masifar kyau tundaga nesa suka zubawa juna idanu yana mai jin farin cikin ganin ta gashi ta  fito kamar wata tauraruwa  karasowa yayi,  ta dauke kanta tareda hade rai ya na zuwa ya rungume ta batareda ya damu da mutanen dake wurin ba ya dora hannun shi a marar ta "ya baby na?  Rage murya tayi a hankali tareda cewa "ni nazama hoto ai yanzu wallahi a matsa inyi flushing din shi inga tsiya,  "what me kikace?  Tayi mai banza ya matse fuska sosai ya riko hannun ta suka shiga ana take musu baya ga masu hotuna tuni sun fara Aikin su,

A she kallo na ciki don Fadin kawatuwar wurin kawai zai cinye fejin yau saidai BARIKI fan's  zasu baku labarin haduwar wurin ba Abinda ya burgeta irin ganin y'ar uwarta datayi a  wurin ga yaronta da ke cikin nashi ceremonial dress din na yara harma da hula yayi kyau da y'ar karamar pistol ta wasa a soke a Aljihun shi,   wurin zaman su suka nufa batareda ya kuma ce mata komai ba don yaji mai tafada,        ga Army bands sai sakin kida sukeyi da kuma busa wurin ya tara manyan sojoji da matayen su Abokan Aikin shi gefe daya matan NAOWAS ne wato NIGERIA  ARMY OFFICER'S WIFE ASSOCIATION ne suncian  anko mai dauke da tanbarin gauraka Abin ba a cewa komai  Abin ya mugun kawatar da ita su Aunty Halima ma gefe guda aka ware musu man yan yayyi Aunty maryam ta jone cikin su,   aka fara gudanar da taro party ne mai Aji ba wani hayaniya harka ce ta girma sai masu  raba drinks da kayan motsa baki keta kai  da kawowa   snacks ne da su namomi Kala Kala kawai kake gani,  tuni na hango Ummu jidda na boye kularda ta yo guzuri don zuba rice sai yakasan ce bikin ba na rice bane, 

Wani cikin manyan sojojin ne ya mike tareda gabatar da taron ta hanyar taya Abokin Aikin su murnar Aure tareda fatan Allah yabada zaman Lafiya  gefe daya suka gabatar dashi a matsayin jarumin soja mai hazaka da gaskiya akan Aikin shi  sun yaba mai sosai a irin kokarin da yakeyi akan Aikin shi,  tareda bashi A word a kan nasarar da yake samu a operation din da aka turashi,   yanda suke yabai tareda saramai lokacin da ya karbi a word trophy din ya mugun burgeta ga wani paret da ake bugamai tun tasowar shi a yau ta kara sanin waye take Aure   taji takarason shi  ko ba a fada ba tasan mijin nata jarumi ne, 

Saida ya karbi trophy din ya karbi speaker tareda godiya cikin halshen turancin shi mai tsada,  kafin ya juya wurin Y'an Uwan shi ya kara musu godiya akan irin soyayya da goyon bayan da suke nuna mai  kafin ya juya kan yasmin data hakimce ta zubawa tsadadden mijin nata ido, 

Ya tako zuwa gaban yasmin data zuba mai ido yafara zubo mata kalamai batareda ya damu da duniya na kallon shi ba "you are my happiness you are my world,  yaci gaba da koro mata kalamai cikin harshen na nasara,  samun ki a rayuwata shine babban farin ciki yasmin Kasan cewar ki a inuwar gidana shine muradin Rayuwa ta kece kika cikamin burin Rayuwa you thank you for being my wife tank you for giving me the best happiness in the world that's  my unborn child in your belly  please take care of my baby I love you now and I will continue loving you, 

         _*BARIKI*_ 👨‍✈ _Auren soja_👨‍✈   Where stories live. Discover now