part 17&18

2.5K 80 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
          *BARIKI*
         _Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

_written by FENERH_
Maman Ammar

*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby

17&18

Wani irin ja da baya YASMIN tayi domin tayi mugun tsorata da ganin shi a irin wannan Unguwar da za a iya sace mutum a gudu,
Nan take jikin ta yafara rawa ta fito da idanuwan ta duka waje tana ja baya,

Shikuwa wani irin farin ciki Yaji na ganin ta nan ya fara sauke ajiyar zuciya  yana tunkarato,
Taku biyu ya riko hannayen ta yana mai kare mata kallo kamar wani mayun wacin Zaki,

Saida ta fada kirjinshi yayi wata wawuyar ajiyar zuciya,  kafin ya bude baki ya fara magana,  ", baby guduna kikeyi? 

"Toh ki daina couse koda birnin misra kikaje zan nemoki,  kokarin fisge kanta takeyi tareda d'an dukan shi a hankali,

"Ka barni banason iskanci ni ba irin Y'an iskan Y'an matan ka bane,  "Zaki zama fiye dasu baby tunda raina ya biya akanki kinga kinada laifi daban daban kizo muje mota zanfada miki laifin,

Wasu irin hawaye ne suka zubo mata yau Allah ya hadata da d'an guguwa ba d'an iska bama kadai,

Cikin karfi yajata da hannu daya ta tirje ya tsaya cak tareda zuba mata idanu cike da wani irin kallo irin na Y'an duniyar maza,

"Zan daukeki idan baki wuce mun tafiba, sautin kukanta tuni ya fito tafara y'ar fa hannu "don girman Allah ka wuce ka kyaleni yanzu mijina zai zo ya dauke ni ka rufamin asiri,

Wani irin fisgota yayi cikin karfi ya jefata motor kafin ya daga jakar ya jefa baya ya rufe cikin tsananin takaici ya tayar da motar batareda ya ce mata komai ba,

Da gudu yake tukun idanun shi sunyi mugun kadawa kamar wuta saida yayi nisa sosai da Unguwar  kafin ya koma gefen titi ya faka,  ita kuwa ai ta dade da sallamawa Allah ikonshi yau tana ganin rayuwa,

Juyowa yayi bayan ya dauki lokaci kanshi nakan sitiyarin motar,  "tell me yaushe kikayi Aure?
Saida ta Kara mannewa da murfin motar kafin tace "ankusa yine ba ayiba,

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kalleta cikin wani irin yanayi "zakiyi kuskure  baby,  karki fara y'arda da Auren wani, 
"Ko bazan Aureki ba dole ki rayu dani y'anda nakeso Aure baya cikin tsarin rayuwa ta don haka kizo kiyi rayuwa dani shine kawai kwanciyar hankalinki da nawa baki daya,

Ai tuni taji tsoran shima da takeyi yafita a cikin zuciyar ta don iskancin nashi ya girmama,  ta k'ank'ance idanun ta domin fara zubomai ruwan rashin kunya,


"Kutumar bala'i me ka dauki mace?  Wallahi ko a mafarki Kayi tunanin rayuwar BARIKI dani Allah  ya isa bare a zahiri,  kai mu ya'ya ne NA halas ba haihuwar dadiro ba kuma duk d'an halas bazai taba y'ar da tarbiyar da iyaye na gari suka bashi ba,

"Bari kaji ra ayina akan ka da duk wani namiji irinka natsani halayenka tir da bunsurancin ka Allah ya wadaran duk wani namiji mai halaye irin nak.......

"Shhhhhh,  ya Dora Han nun shi a kan bakinta yace "breath  baby ki numfasa haka mana ya furta yana mai fitarda wani irin mugun murmushi,

"Kina yiwa uban yaranki dazaki Haifa a dadiro baki ki Bari karki lalata min Yara, 

Wani irin kallonta yakeyi tundaga Kasa har sama hijab din yayi mata kyau Amma shi zahirin ta yakeson gani a yanzu,

Tana kan ruwan bala'i ta tsinci hijabinta a Han nun shi  ai kuwa a razane ta kurma mai wani irin ihu har saida ya to she kunnen shi,

         _*BARIKI*_ 👨‍✈ _Auren soja_👨‍✈   Where stories live. Discover now