part 61&62

2.2K 65 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
          *BARIKI*
     _Auren Soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Written by FENERH

*Dedicated to*
Fiddausi mainasara feby

61&62

*Aha masoyan korai kunayi inajin dadi kuna bari inajin haushi,  a gaskiya comment dinku jiya ya zaburar dani fiye da tunanin ku naji dole in muku typing a yau naga masoyan Asali naga masu kaunar FENERH fisabillahi ina matukar godiya agareku Allah yabar kauna*

Gyara kwanciyar ta tayi dai dai tana wasa da nana akan gadon mama hindatu tayi haka ne don gujewa hayaniyar da tayi yawa a cikin gidan saboda taro shiyasa ta shige kuryar daki,  ganin kusan minti goma bata fitoba ya tura mata text akwai tsarabar ki kizo ki sa a kwashe su zamu wuce masaukin mu yanzu inason inyi wanka,  budewa tayi ta karanta ta goge tareda ci gaba da Abinda takeyi, 

Fitowa yayi daga cikin motar cikeda tunanin mafita,  da Sauri ya karasa wurin da baba suke zaune yace "baba bismillah,  baba ya mike cikeda jin dadin kamar wannan babban mutum din mai matsayi yana bashi girma a baynar jama' a dole yayi farin cikin samun suruki nagari,  wurin motar suka karasa ya bude boot din dake shake da kayan rabon da yazo dashi gefe daya kuma drinks ne a dayan motar dasu ruwan gora shake yasa aka fara fitar dasu ana jerawa dakin waje shaddodin baba ya kira baban zango yace yasan inda zasu ajiye wannan in angama taro a rabawa Y'an uwa,  bayan hilux kuwa kayan Abinci ne shake irin su shinkafa taliya su jarkokin mai da sauran tarkace yace akaiwa Amarya gara,  su baba sun rasa bakin godiya baban zango yafara share kwalla,  "Allah ya kareka muhamdu Allah ya tsareka,  kullum Alkhairin da kake mana baya karewa muna godiya Allah ya biya,

Wata jaka ya fitar katuwa ya kalli gefen su ismail ya daga mai hannu,  cikin girma mawa ya matso yace " ranka ya dade gani Allah yasa ba laifi nayi ba?  Koda yake aini akayiwa kulli ta kafa rike hannun shi yayi tareda daukar jakar gefe daya sukabar su baba nata godiya,  " ai harda kafafu ma nayi maka idan ta kama har dungure zan iya maka akan my Yasmin,  please muje ka rakani wurin ta inaso ma in gaida su mama inyi musu Allah sanya Alkhairi,  dariya ismail yayi sosai tareda cewa " yanzu zaka iya shiga ciki kuwa akwai fa mata cike Koni na kasa shiga ciki tundazu,  " me I can't nakirata taki fitowa bazan iya five minutes bangantaba muje ko inshiga ni Kadai,  aa muje bari inkira Ahmad mu tafi baki daya,.

Ahmad ya matso tareda karbar jakar suka shiga cikin shine agaba kamar d'an gida su baba na ganin su Abin ya mugun  burgesu ganin yanda ya dauki kanshi d'an gida ba girman kai,   kamshin shi yafara sallama a tsakar gidan kafin   suji sallamar shi  ,  gaba daya matan ido suka zuba mishi don da yawa basu sanshiba,  Aunty maryam ta matso cikin sauri suka fara gaisawa su mama sai kai da kawowa sukeyi,  mama hindatu ce da tafito daki rikeda d'an bokiti a hannun ta tafara Maraba da surukaina  ku iso,  gaisawa yafarayi da matan kafin ayi musu jagora zuwa cikin falon mama hindatu dakin ba laifi don akwai kujeru harda kayan kallon ta gefe kuma katon deep freezer dinta ne datake sana ointa dakin duk da ana biki tsab yake domin duk yawancin mata na sauran dakunan gidan da kuma tsakar gidan,

Tana kuryar dakin taji muryar shi tayi saurin zabura ta mike zaune  tareda dafe kirjin ta  ya shigo?  Ta fada a bayyane  NANA ta kalla dake baccinta ta zuro kafa ta leka ta window tana kallon yanda yake gaisawa da matan har zuwa lokacin da aka shigo dasu ciki,    komawa tayi ta zauna tana fargabar Abinda zai biyo baya,  shikuwa yagama baza idanun shi a cikin gidan kaf bai gantaba,  bayan sungaisa dasu mama hindatu itama mama ta shigo ya musu Allah sanya Alkhairi suka fara zubamai godiya domin baban zango ya fada musu komai,  mama hindatu ta kalleshi tace "ka ciri tuta ba yanda yaya baiyi da shi ya koma cikin gari yaki Amma sanadinka ya Amince muna matukar godiya,  "bakomai mama Addu ar ku nake nema kawai,  mama ta fita ya ce " banga yasmin din ba?  " ai tana ciki,  Aka kira mama hindatu a waje ta mike tareda cewa Mama ki fito ga mai gidanki duk da nasan kina jin komai,  Aunty maryam ta shigo musu da kayan motsa baki irin na biki dasu drinks Zainab ma ta shigo taga Wanda ya taimaketa yarabata da kishiya,

         _*BARIKI*_ 👨‍✈ _Auren soja_👨‍✈   Where stories live. Discover now