Chapter 08

74 5 0
                                    

🏤 *MASARAUTAR* *MU* 🏤
Story and writing
By

Fatima(Zarah)

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
https://www.wattpad.com/user/Zahrah193?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_campaign=invitefriends

In *the name of Allah the benefmosticent and the most merciful,all thanks be to Allahu SWT that gives me the health and opportunity to start writing this book.I pray to Allah to help me to write* *something that will benefit our Muslim ummah.*

*This is a fictional story.Names and incident in this story are just my* *imaginations.Any body that this story resembles his life is just an unplanned* *occasion.Please nobody should change my write-up in any other way,either by* *editing,printing and* *many more.*

*This story is created to educate,enlight and entertain our readers.Please support me by commenting and* *sharing this novel all over,because they are the backbone of my* *story,your* *support will keep my* *write-up survive,without you guys I can't make tiny of it,be with me* and *my story* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Dan Allah Ina cigiyar littafin life of Zarah,duk mai shi daga farko zuwa inda aka tsaya ya taimaka mun dashi ta wannan Number d'in 08063304625.

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

*Chapter 08*

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Kallon su bokan yayi yace"kar ku damu burin ku sai ya cika ko ta halin ka'ka,d dariya suka yi dukkan su cike da farin cikin abinda bokan ya sanar dasu,bud'e jakan da suka zo dashi sukayi suka d'akko rapper d'in dubu d'ad'd'aya guda biyar suka ajiye mishi,mi'kewa sukayi suka mai sallama suka tafi,cike da farin ciki bokan yace"dole nayi muku aiki sosai dan burin ku ya cika,dan nasan kuna hawa sarautar wannan garin nima zan samu Alkhairi",girgiza kai yayi sannan yayi dariya mugunta yace"kai Yarima shikenan na gama da kai,kamar anyi an gama ne".
Suna fita Matawalle ya kalli Wambai yace"kai gaskiya Matawalle baka da dama,yanzu duk nan nan dakai da maimartaba yake yi Ashe cin dunduniyarsa kake yi",dariya Matawalle yayi yace"haba wa sai ma na na'kasa mai yaron zai san yana nan nan dani",dariya sosai Wambai yayi yace"ai toh shikenan,ni babban matsala na shi ne ace yau yayi aure,toh fah lokacin ne zamu shiga cikin babban tashin hankali dan ba'asa wacce zai auro ba,kar yazo ya auri mana wacce ba a cikin mu take ba tazo ta haifo sarki kamar yadda mahaifiyarsa tayi",ajiyar zuciya Matawalle yayi yace"yanzu dai mu fara tackling wannan problem d'in daga baya nazo muyi tunanin mafita ta gaba",jinjina kai Wambai yayi yace"haka ne mai fuska biyu",dariya suka kwashe dashi dukkan su tare da taga hannu suka bar gurin,suna fitowa suka had'e fuska kamar wad'anda basu ta'ba sanin juna ba.Wannan abinda suke yi yana matu'kar d'aure ma 'yan Masarautar kai,dan in sun had'u a guri d'aya basa ga maciji sabida iya taku,amma ta bayan fage babu wanda ya kai su yin shiri.

*****************
Iya na shigowa ya tadda Gimbiya Zulfah cikin kogin tunani,kallon ta yayi sannan ya girgiza kai yace"Zulfah!,Zulfah!!,Zulfah!!!",sai da ya kira sunan ta sau uku kafin ta ansa a firgice saboda tayi nisa cikin tunani,kallon ta yayi yace"haba Gimbiya ta,wannan wani irin damuwa ce kika Sanya ma zuciyar ki,so kike ki jawo ma kanki wata cutar",ajiyar zuciya ta sauke sannan tace"ba haka ba ne,ina cikin matu'kar tashin hankali ne ga me a abinda nake so ya faru tsakanin Yarima da Sulaymi,amma yanzu na samo mana babban mafita wanda idan muka aikata zamu samu mafitar da muka dad'euna nema",cike da farin ciki Iya yace"haba Zulfah har sai kin ja mun rai kafin zaki fad'a mun wani irin mafita kika samo mana,dan Allah labarta mun wannan daddad'an labarin",dariya Gimbiya Zulfah tayi tace"kai Sarki na,ba wani mafita bane illa muje gurin sarkin bokaye na da,kasan yanzu Masarautar nan sun bar anfani da wata a'kida sai Sunnah,wai kamar Masarautar Turunku ce tabar kiran malamai suyi mata duba akan abinda ke damun Masarautar,shiyasa yanzu Masarautar mu ta lalace saboda barin al'adan nan da sukayi wai su masu imani",ta fad'i maganan da d'aci a cikin zuciyar ta sannan ta saki wani dogon tsaki saboda 'bacin rai,ajiyar zuciya iya ya sauke ya kuma girgiza kai yace"Zulfah baki kaini shiga 'bacin rai ba idan na tuna cewa yanzu an watsa da wannan al'adar,amma ba komai ko mai zai faru doleubi wannan la'asar ta bayan fage,dan ba zai yuwu mu zauna cikin duhun Kai ba babu wani mafita ga al'amuran mu na yau da kullum",dariya Gimbiya Zulfah tayi tace"haka nake so inji Sarki na,yanzu zanje in shirya anjima zamu tafi ni da Sulaymi,kuma tafiyar zata kasance tafiyar sirri ce",cikin jin dad'i iya yace"ai daman tafiyar dole ta zama ta sirri in ba haka ba magautan zasu Kai mu su baro",yana gama fad'in haka ya mi'ke yana cewa"bari inje gurin Wambai akwai maganar da nake so mu tattauna dashi",cikin sauri Gimbiya Zulfah tace"toh Daddyn Sulaymi mai zai hana ka mai magana akan auren Sulaymi da muke so Yarima yayi,kaga shi ma ba sa son Yarima,kaga zamu samu mafitakoh",jinjina mata Iya yayi yace"gaskiya brain d'in ki yana ja,bari inje muyi magana",yana fad'in haka ya fice daga d'aki cikin farin cikin solution akan problems d'in su ya fara bayyana.Ita ma Gimbiya Zulfah d'akin Sulaymi ta wuce ta tada ta daga bacci,saboda ta shirya tazo suje gurin bokan,ita ma so take tayi wanka ta shirya.Tana shiga d'akin ta tadda ta tana zaune tana chatting,kallon ta Tay tace"my dear tashi ki shirya mun samu wani boka zamu tafi gurin shi yanzun nan",tasowa Sulaymi tayi tace"wai da gaske Mummy,wai yanzu zan zama matar Yarima,kuma zan haifi sarki",cikin dariya Gimbiya Zulfah tace"Eh mana,ki sa a ranki kamar kin aurin Yarima Abdul,kuma kin zama matar sarki,mahaifiyar sarki kuma kalar sarki",daka tsalle Sulaymi tayi ta rungume Gimbiya Zulfah cikin murna,ta shige bayi don tayi wanka,ita Kuwa Gimbiya Zulfah dariya kawai tayi ta tashi ta tafi d'akin ta dan ta shirya,tana shiga wayar ta ta fara ringing,dauka tayi ta duba mai kiran ganin an sa my dear son yasa ta d'auka da sauri,cikin soyayyar uwa da d'anta Farouq yace"Good Morning Mummy",cikin jin dad'i tace"How are you doing my dear",Murmushi yayi wanda ke 'karama ma fuskar sa kyau yace"fine Mum", sannan ya 'kara cewa"Mummy I will be on my way tomorrow",cike da jin dad'i tace"really son,i can't wait to see",cikin jin dad'i ya jinjina kai sannan suka cigaba da hiran su,sun kai kusan 30mins kafin sukayi sallama akan cewa zai dawo daga India gobe saboda shima doctor ne acan.Gimbiya Zulfah na sauke wayan a kunnn ta tayi Jim tana tunanin dawowa Farouq,dan kwata kwata ya fita daga cikin su,a kullum wa'azi yake musu akan Subaru aikata abinda suke aikatawa in ba haka ba in Allah ya tashi kama su baza su ji da kyau ba ,amma in Banda hantarar shi babu abinda suke yi,yanzu ma dawowa nan da yace zai yi inda da akwai wani hanyar da zata bi ta hana shi dawowa da sai ta bi,dan yanda suka d'akko wannan maganar na Sulaymi da Yarima gadan gadan tasan sai ya nemi ya 'bata musu shiri,amma ai tasan ya zata yi dashi,bari dai ya dawo,ita babban bakin bikin ta shi ne yadda ya mai a Ammi kamar wata uwar sa sau abinda tace masa yake bi,dan kullun a part d'in ta yake yini indai yana garin.Katse tunanin ta tayi ta shiga cikin toilet da sauri,tunda dama tun d'azu tasa hadiman ta sun hada mata ruwan wanka,wanka tayi,tana zuwa ta tadda kayan ta a ajiye a gefen gado kamar yadda ta umurci hadiman su d'akko mata,da sauri da sauri ta shirya sannan ta d'auki alkyabba ta saka ta fito,sawa tayi aka kira mata Sulaymi,kallon hadiman tayi tace"kuje part d'in Iya ku gyara,ku tabbatar kun chanza bedsheet din kuma kun saka turaren wuta saboda na san warin ku ma kadai ya fishi d'akin",tana fad'n haka ta fice daga d'akin ita da Sulaymi tana ce musu zasu je gaishe da mai babban d'aki,suna fita suka bi ta bayan Masarautar suka fita wanda ya kasance duk masu fadin dake gurin mutanen sune.

********************
Su Yarima sun isa Masarautar Zazzau lafiya,idan suka tarar an had'a musu liyafa na gani na fad'a,in kaga yadda aka shirya liyafar zaka yi tunanin cewa Sarki guda ne zai sauka a cikin Masarautar,suna shiga cikin Masarautar Saleem ya taso cikin matu'kar farin ciki ya rungume Yarima yace"welcome to Zazzau Emirates",dariya Yarima yayi wanda hakan har sai da yaba ma su Husnah mamaki dan sun manta yaushe rabon da yayi dariya haka a gaban su,kallon shi Saleem yayi yace"shi ne baka fad'a mun da mata ta za kuzo ba ballantana in hada mata liyafa na gani na fad'a",harara Yarima ya zabga mishi sannan yace"babban banza kawai",dariya suka kwashe gaba d'ayan su cike da kaunar juna.........

In naga comment dinku yayi mun zaku samu da yamma,shiyasa ban muku da yawa ba.

Vote
Comment
Share

FATIMA ZARAH

MASARAUTAR MU Where stories live. Discover now