Chapter 25

77 7 2
                                    

MASARAUTAR MU

✍🏻 Zahraty ❤️

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

Don Allah kuyi mun Afuwa na rashin juna kwana biyu🙏🏻,amma yanzu everything is fine,insha Allah zaku rin'ka samun update kullum💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

25.

Jinjina kai Sofiyyah tayi cike da gamsuwa da maganar da Gimbiya Zulaihat ta fad'a mata,sannan tace"shikenan ummi,insha Allah komai zai zama dai dai Babu abinda zai 'kara damun Abbu,kumma Allah yasa ya iya cin wannan jarabawar",jinjina kai Gimbiya Zulaihat tayi sannan tace"Ameen ya Allah"tana share hawayen dake kan kumatun ta,rarrashin ta kawai take yi cike da matsannanciyar damuwar da ke kwance akan fuskar ta.

Kallon ta Gimbiya Zulaihat tayi tace"tashi kine sashen su Sumayyah ki zauna,hakab zai rage miki damuwa,kuma don Allah kar ki saka komai a ranki,kinga ke yarinya ce,kar ki yadda damuwa ta zame miki 'kawa in ba haka ba tun yanzu sai ki damu da hawan jini",ajiyar zuciya Sofiyyah ta sauke sannan tace"insha Allah Ummi zan bar tunanin,amma yanzu da kika ce inje side d'in su Sumayyah,ke fah?,ke kad'ai zan bari anan kema kiyi ta tunani,don Allah ki kyale ni anan mu zauna tare",murmushin ya'ke kawai Gimbiya Zulaihat ta saki cike da damuwa tace"nace miki ki tafi sabida ni Ina so inyi sallah ne,kuma nasan ke baza kiyi ba shiyasa",jinjina kai Sofiyyah tayi tace"shikenan Ummi bari inje sai na dawo",a hankali tace"a dawo lafiya",tana fad'in haka ta tashi ta nufi hanyar fita tana 'kara yi ma Ummi sallama sannan ta tafi zuwa part d'in su Sumayyah.

Binta da kallo kawai Gimbiya Zulaihat tayi har ta bar d'akin cike da tausayin 'yar ta ta,tasan Sofiyyah da sa abu a rai,kuma ta tabbatar wannan abun ba zai bar ranta ba,yana nan,tasan ba zata manta da wannan abun ba,yanzu ma kawai tayi shiru ne dan kar ta 'kara mata damuwa,murmushi kawai ta saki tana 'kara jin 'kaunr yarinyar a cikin zuciyar ta,tun yarinyar na 'karama take da matu'kar tausayi,bata son ganin ko da chanji a fuskar ta ballantana kuma 'bacin rai,ai a take hankalin ta yake tashi,ta kasa zaune ta kasa tsaye,girgiza kai kawai tayi ta katse tunanin ta sannan ta mi'ke ta nufi toilet,alola ta d'auro sannan tazo ta kabbara sallah.

Sofiyyah na shiga cikin part d'in su Surayyah ta tadda su zaune suna hiran su,kallon su tayi tace"'yan mata ana hira ne",kallon ta Husnah tayi kafin tayi dariya tace"kai Aunty Sofiyyah,wallahi kin bani dariya,wai 'yan mata,suwaye 'yan matan",dariya Sofiyyah tayi tace"ku mana,ai kune 'yan matan,yanzu dai a bar maganan ya hannu", Murmushi Husnah ta saki tace"lafiya qalau Alhamdulillah,yayi sau'ki,jibi ma zamu je a kwance d'aurin da aka yi",kallon Husnah Sumayyah tayi tace"kai uwar surutu don Allah kiyi mana shiru,tun dazu cu cu cu kamar wata tsuntsuwa",dariya Tasleem ta tuntsure dashi tana dukan kujera,ita kanta Sofiyyah da kyar ta iya shanye dariyar ta sannan ta kalli Husnah tace"kinji Sis kyale Sumayyah kawai fad'i take,ita ba taga surutun da take dashi bane sai naki,ki kyale ta kawai",jinjina kai Husnah tayi tace"ai dama na sani kawai fad'i take yi",dariya kawai suka yi suka ci gaba da hiran su cike da farin ciki da 'kaunar juna.

Sai da aka Kira sallahn la'asar sannan suka tashi suka wuce bedroom d'in,alola suka d'auro dukkan su banda Sofiyyah wacce take fashin sallah,tare suka yi jam'in sallahn,sun idar wa suka sanya hijab d'in islamiyya suka sanya,kallon Husnah Sofiyyah tayi taje"je ki Kira Sulaymi kice mata muna jiran ta kar muyi latti", ta'be baki Husnah tayi tace"ta'b,ni zanje in kirata,kawai ta nemi ta fad'a mun maganar banza",kallon ta Tasleem tayi tace"sannu uwar tsiwa,ba cewa aka yi kije ki kirata mana,obey before complain",kallon ta Husnah tayi sannan ta girgiza kai tayi waje zuwa kiran Sulaymi.

Tana shiga part d'in su Sulaymi ta tadda hadimai na zirga-zirga a parlourn,ta'be baki kawai tayi sannan ta nufi bedroom d'in Sulaymi kai tsaye ta nufi,tana shiga ta tadda ta tana bacci a kan gado,wani kallo ta watsa mata sannan ta fara kiran sunan ta,ganin bata ko motsa ba yasa ta jinjina kai a cikin ranta tace"dan'kari wannan ai sai a sace ta bata ma sani ba",bubbuga pillow d'in tayi,a firgice ta tashi,wani banzan kallo ta watsa ma Husnah sannan tace"malama lafiya kika shigo mun d'akin",dariya Husnah ta kwashe dashi tace"bani na kar zomon ba rataya aka bani,dama zaki biyayya ne da na miki hanyar wanda kike so",ta fad'a cike da tsiwa da dariya,wani ba'kin ciki ne ya mamaye zuciyar Sulaymi,d'agiwa tayi ta kalli Husnah tace"ni sa'ar ki ce da kike fad'a mun haka",dariya Husnah tayi tace"ai ba 'karya nayi ba,gaskiya na fad'i,bari in fad'a miki babu abinda ban sani ba game da ke,kallon ki kawai nake yi,amma inna tashi maganin ki bazaki ji da dad'i ba",cike da tsantsar mamaki,firgici da al'ajabi Sulaymi ke kallon Husnah,da kyar ta iya bud'e baki tace"ni kike fad'a ma haka Husnah",dariya Husnah tayi tace"kinga,yanzu dai abar zancen,ance in ce miki kiyi sauri ki fito zamu tafi islamiyya",tana fad'in haka ta juya tayi tafiyarta cike da farin cikin maganganun da ta fada ma Sulaymi,ita Kuwa Sulaymi da kyar ta mi'ke ta shirya ta fito.

Murmushine kwance akan fuskar Husnah ta fito daga cikin sashen,kallon ta Tasleem tayi tace"ke lafiya kike murmushi ke d'aya,me kika aikata,don nasan ke da Sulaymi bazaku ta'ba zama inuwa d'aya ba",dariya Husnah tayi tace"kai sis,kin sa mun ido da yawa fa",jinjina kai kawai Tasleem tayi tana murmushi don tasan Husnah ta takalo Sulaymi ne kawai , Sulaymi na fitowa daga part d'in su suka wuce,ba tare da sunce da juna ko 'kala ba.

Zaune mai martaba yake akan dadduma,kallon Ammi yayi yace"Ammin Husnah wallahi Wambai yana matu'kar bani tausayi,kin kika ganshi sai kin kusa zuba hawaye ya take ya fita hayyacin sa",ajiyar zuciya Ammi ta sauke cike da tausayin Wambai tad"insha Allah zai samu sau'ki,tunda gobe za'a fitar dashi",jinjina kai yayi yace"hakane",kallon sa Ammi tayi tace"ni fa har yau ban yadda cewa maganin asibiti Wambai ke bu'kata ba",kallon ta yayi yace"a'a ke dai bari kawai,in har aka kai shi can Indian in har bai warke ba sai nasan abin yi",jinjina kai Ammi tayi tace"toh shikenan,Allah ya dafa mana........


Gashi nan na daure nayi typing yau,don Allah ku rin'ka comment domin shine ke 'kara mun Kwarin gwiwa

Vote
Comment
Share


08063304625

MASARAUTAR MU Where stories live. Discover now