1

21 6 2
                                    

Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin rahama Muhammad (S.A.W).

Wannan ƙayataccen labari mai suna mafita ƙirƙirarren labari ne da na rubuta shi a wannan kafa ta wattpad don nishaɗantarwa gami da bayyana wasu darussa na rayuwa.

Ba labarin wasu keɓantattun mutane ba ne don haka idan yayi kama da abin da ya faru ga wani a gaske to kawai labarin ne yazo a haka amma ba hakan aka nufa ba.

Zan iya cewa wannan shi ne littafi na farko da na wallafa a wannan kafa ta wattpad a tsarin labarai na almara ba don komai ba sai don ganin muna da ƙarancinsu a jerin littafan hausa musamman waƴanda ake rubutawa a wannan kafa ta wattpad.

Allah nake roƙo da ya amfanar da ni da ku ya kuma sanyamu cikin ceton manzon rahama (S.A.W).







Farko...

Duk da tsananin sanyin da ake hakan bai hana su yin sammako ba, ba don komai ba sai don halartar ɗakin jarrabawa.

Su uku suke tafe, mace da namiji suna tafe cikin walwala da fara'a yayin da ɗaya namijin da yake daga bayansu za ka iske cewa tabbas dariyar da yake irin dariyar nan ce da ake cewa dariyar yaƙe, domin kuwa fuskarsa ba ta ɗauke da irin sinadaren da suke cikin irin dariyar da yayi.

Sararin samaniya yayi mutuƙar kyawu a wannan safiya domin saman tayi kalar shudi mai haske sosai, yayin da fararen gajimare sukai mata ado mai ban sha'awa. Kai kace wata saman ce ba irin saman da ta saba cika da hazo ba musamman a irin wannan yanayi na sanyi.

"Hamza, tunda akwai sauran lokaci kafin mu shiga exam ya kamata muje mu fara submitting practical ɗinmu. Kasan malamin nan ba mutunci ya cika ba..." Ɗalibar da suke tafe tare da ɗalibi namiji ta faɗa lokacin da take juyawa tana kallon na bayansu wato Hilal. Wanda bai iya ba da amsa ba domin kuwa baima san ta kalle shi ba sabo da tsananin tunanin da yake.

"Sadiya tana maka magana fa..."
Hamza ya furta a daidai lokacin da shi da Sadiyar suka tsaya suna sauraron ƙarasowar Hilal wanda tazararsu da shi bai wuce taku biyar ba.

Hilal yayi murmushi yace "Naji me tace ai, amma dai a sake maimaita mini."

Hamza da Sadiya sukai murmushi mai kama da dariya saboda sanin cewa abin da Hilal ya faɗa ba haka yake ba a zahirance, duk da haka  Sadiya sai ta maimaita masa abin da ta ambata da farko. Ai kuwa take yayi na'am da buƙatarta don haka sai suka nufaci lab don bada report ɗinsu kafin shiga jarrabawar ɗin.

Sadiya doguwa ce sannan ba fara ba ce, hakanan ba zaka sakata cikin jerin baƙaƙe ba, wasu daga mutanen da suke rayuwa da ita suna fadin cewa da ace ita fara ce da ba a san irin kyawun da za tayi ba domin a hakan bata taɓa jerawa da wani ko wata anga ya fita kyan gani ba. Ita kuwa a nata hangen tana ganin kasancewarta baƙa shi ne ya bata wannan kyan ganin, don haka koda wasa bata sha'awar sauya kalar fatar ta, don me zata sauya kalar da aka haifeta da ita?

Hamza bai kai Sadiya tsayi ba, sai dai idan ba masu bin ƙwaƙƙwafi ba gane hakan zai wahala. Shi Hamza fari ne ba sosai ba, sannan siriri ne amma ba sirantar nan irinta ƙashi da fata ba, kana kallonsa hancinsa ne zai fara maka maraba wanda yake siriri kuma mai ɗan tsayi. Sai bakinsa da yake dan karami tamkar ba zai bashi damar yin babbar loma ba.

Hilal kuwa fari ne tas, yana da zagayayyiyar fuska kamar ƙwai, sannan hancinsa yana da fadi kadan yanabda manyan idanu farare tas, sai wani matashin saje da ya kewaye fuskar tasa.

Suka tsaya sukai cirko-cirko a bakin lab din, Sadiya ce ta fara ƙwanƙwasa ƙofar, da fari sun ji motsi, amma sai suka ji anƙi zuwa a buɗe kofar.

Hilal da yake daga baya, sai kawai ya matso yasaka hannu ya tura ƙofar da dan ƙarfi ai kuwa sai ta buɗe.

MAFITA...Where stories live. Discover now