3

11 6 3
                                    

Sadiya hankalinta ya tashi ganin irin halin da yan uwanta suke ciki.

Murmushin da Rubtas yayi shi ne ya ƙara ɓata mata rai. Ta galla masa harara tace "Don me za ka rinƙa farin ciki akan an kama yan uwana?"

"Ba murna nake ba,” Rubtas ya ambata cikin risinawa, "Ina gaban sarauniyar mata ne shiyasa nake kokarin ɓoye dukkan ɓacin rai..."

Sadiya ta waiga bayanta don ganin wacece sarauniyar matan, abin da ta gani ya mutukar bata mamaki domin kuwa ba ta ga komai ba inka ɗauke bishiyu da kuma tsuntsaye da suke tsalle daga wannan reshe zuwa wancan...

Rubtas yayi murmushi yana mai kallon Sadiya daga bisani ya numfasa gami da kaɗa jelarsa don kore wani tsuntsu da ya hau gadon bayansa. Daga bisani sautinsa ya bayyana yana mai cewa "Har kina tunanin akwai wata sarauniya bayan ke cikin fadin duniyar tsageru? Kece mace ta farko da ta taɓa halartar wannan duniyar tamu ta masu kafafuwa huɗu, don haka ni babban burina shi ne in kai ki wajen al'ummarmu don su ji abin da kakanninmu suke faɗa na cewa ana iya samun jinsin mata a duniyar tsageru wayanda suke iya tafiya da kafafuwa biyu..."

Shiru yayi lokacin daya ga tsuntsaye suna ta tashi suna guje-guje, a firgice ya dafa kirjinsa ya zaburo da gudu ya nufi inda Sadiya take da zuwansa ya buya a bayanta yana mata magiya... "Don Allah ki taimakeni ki cece ni daga Azzalumin sarkinmu. Tabbas yaji labarin zuwanki don Allah kada ki ce musu mun hadu dake don zasuyi tsatstsauran hukunci a gareni..."

Da faɗin haka kawai sai ya je bayan wata ƙatuwar doguwar bishiya ya ɓuya. Ɓoyewarsa keda wuya sai kawai ga wata rundunar wasu halittu masu kama da shi dukkaninsu suna tafiya irin tasa wato suna amfani da hannayensu da kafafuwansu. Duk da hakan amma suna ɗauke da muggan makamai. suna hangota suka bazamo kanta suna iface-iface.

Ganin haka yasa Sadiya ta zare takobinta, takobin tana wani haske kamar fitila duk da duhun hadarin da ya mamaye sararin samaniya amma sai haske ya gauraye ilahirin kewayen da take.

Bisa ga mamakinta, maimakon su nufota sai ta ga suna darewa suna wuceta...

Tayi ajiyar zuciya ta rintse ido cikin murna, domin ita a nata tunanin sun tsorota shiyasa ba mai iya zuwa ko biyowa ta inda ta tsaya...

"Ke tsagera, meya kawo ki duniyar masu kafa hudu?"
Wata murya ta tambayeta cikin tsawa, Sadiya ta buɗe ido a razane, ta kalli kewayenta sai taga wayannan halittu ne suke kewaye da ita.

"Tambayarki nake, ko kuwa ba za ki bada amsa ba sai kin ji azaba daga azabobin mai girma sarkinmu?" Muryar ta sake dira a kunnenta. Sadiya tayi yunkurin yin magana amma sai ta ji tsoro ya hanata furta komai.

"Kai kuma Rubtas ka bayyana a gabana kafin in nemeka domin tauraron kimiyya ya nuna mana cewa tabbas kai ne wanda ya fara haɗuwa da wannan tsagera ba tare da ya sanar da mu ba..."
Kafin mai maganar ya rufe baki sai ga Rubtas ya fito daga inda ya ɓuya jikinsa yana rawa yana mai kuka yana zubar da hawaye. Yana kallon sama.

Sai a lokacin sadiya ta ankara da wanda yake maganar, shima dai irin halittar waƴannan mutane gareshi, sai dai shi fatarsa koriya ce shar sannan idanuwansa suna wani jan haske tamkar ana hura garwashin wuta. A sama da su yake a bisa iska ba tare da ya dogara da komai ba.

Sadiya taji tamkar ta durkusa bisa gwiwarta itama ta nemi gafara... Amma kuma saita tuno itafa bata da wani laifi wannan duniya ma asali cikin rashin sani suka zo ta... Lokaci guda kuma ta tuno da irin karfin da take da shi a wannan duniya, ta tuno irin tsallen da take, da kuma takobin hannunta kamar yadda ta tuno da bindigarta. Don haka kawai sai ta fito da bindigarta ta sai ta wannan shugaban nasu ta rike bindigar da hannayenta guda biyu tana huci don barazana.

Maimakon shugaban halittun yaji tsoro sai kawai taga da shi da sauran halittun suna kyalkyala dariya, amma maimakon ta karaya sai ta gyara tsayuwarta tana mai ja da baya kadan... Kafin ta ankara sai ji tayi an cafki gashin kanta ana kokarin janta sama, dubawar da zatayi sai taga wannan shugaban ne yake janta da jelarsa, wadda ta tamke gashin kan Sadiya...

MAFITA...Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang