2

13 4 2
                                    

Hasken ranar da yake dukan fuskar Sadiya shi ne ya farkar da ita, buɗe idonta keda wuya sai ta ganta a ƙungurmin daji wanda ke ɗauke da wasu dogayen bishiyu, banda ƙarar tsuntsaye babu abin da take ji, ta kalli gabas da yamma bata ga komai ba sai waƴannan bishiyu birjik waƴanda wata matashiyar iske ke kaɗasu yayin da ganyayyakinsu suke zubowa ƙasa jefi jefi.

Ta sake waigawa kudu da arewa amma abin da ta gani a duban farko shi ne ya sake maimaituwa. Ta ɗaga hannunta da zummar ta kwarara ihu amma inaa... Sai taji alamar akwai wasu abubuwa a hannunta, dubawar da zatayi sai taga wani karfe ne kewaye da hannayenta kamar awarwaro sai dai shi yana da faɗi domin tun daga idon hannunta har zuwa kusa da gwiwarta duk shine...

Ta firgita mutuƙa, ta dora hannunta a kan ƙirjinta don tsoro, namma sai wani mamakin ya cikata, domin kuwa gani tayi ba kayan data sani bane a jikinta, maimakon lab coat sai taga tana sanya da kayan yaƙi irin waƴanda take gani cikin fina-finai...

Abin ya ɗaure mata kai. Ta sake duban jikinta taga wata takobi a cikin kufenta a rataye a kugunta daga ɓangaren dama, daga hagunta kuwa taga wata bindiga ce madaidaiciya mai daɗin riƙewa... Tabbas sai a yanzu ta gane cewa tana cikin koriyar duniya da yan'uwanta Hamza da Hilal suka zaɓar mata...
Shin suna ina?
Tambayar da ita kanta bata san amsarta ba kenan.
Ta sake duban dajin taga waƴannan bishiyun ne iyakar ganinta, daga nesa kaɗan kuma wata ƙorama ce ke gudana da tsananin gudu...

Sadiya ta kalli kasar dajin nan ta ganta baƙa-ƙirin ta duba sararin samaniya taga banda gagarumin baƙin hadari babu abin da take iya gani, ranar data tashe ta babu ita babu dalilinta.

Sai kawai ta samu waje ta zauna zaman dirshan, ta jingina kanta da wata bishiya tana tunanin me zai sameta. Zuciyarta ta rinƙa kawo mata tunane-tunane kala kala ga tsoro da ya cika zuciyarta.

"Barka da hutawa" kamar daga sama taji an ambata.

Ta duba sama da ƙasa bata ga kowa ba. Ta miƙe ta ɗora hannunta hannunta akan marikin takobin nan da yake rataye a ƙugunta kai kace wata mashahuriyar jaruma ce, ita kanta abin ya bata dariya a zuci. Zuwa wani lokaci sai taji ana ƙyalƙyala dariya, cikin hanzari ta aza hannu ta fizgo bindigarta, sai taji bindigar tayi wani ruri, daga bisani kuma sai wani jan haske ya bayyana a jikin bindigar. Ai kuwa sai ta saita wata bishiya ta matsa wannan bindiga kafin ta ɗauke hannunta har harsashi biyu ya fita, amma shiru babu abin da ya samu bishiyar tare da cewa waƴannan harsasai duka sun huda wannan bishiya, Sadiya tayi tsaki tayi jifa da wannan bindigar bisa ga mamakinta kafin bindigar taje ƙasa sai kawai ta juyo da kanta ta koma gidanta ta zauna a kugun Sadiya... Hakan kuwa yayi dai dai da lokacin da wannan bishiyar data harba tayi bindiga ta tarwatse.

Mamaki ya kamata, sai taji karfen  hannunta na hagu yayi motsi ai kuwa sai ta kai idanunta ta ɗago hannun sai taga karfen yayi haske da rubutu a jikinsa da yake nuna mata saura harsashi casa'in da takwas.

Sadiya tayi murmushi tace lallai ashe harsashi dari take ɗauke da shi.

"Maraba da gimbiya Sadiya daga duniyar Tsageru zuwa duniyar masu kafa huɗu..."
Ta ji wannan murya ta sake biyo iska ta dira a kunnuwanta.

"Wanene yake mini wasa da hankali? Ka bayyana kanka mana koma wanene..."
Sadiya ta ambata cikin dakiyar zuciya da jarumta.

Sai kawai taji motsi a bayanta, a tsorace tayi tsalle da nufin juyawa, amma bisa mamakinta sai taga tayi sama tana juyawa daga bisani tayo kasa luuuu bata san lokacin data fara ihu ba, amma bisa ga mamakin ta da ta faɗo ƙasa sai taga babu abin da ya sameta hasalima wata yar ƙaramar alkafira tayi ta mike tsaye... Abin ya mutukar ɗaure mata kai.. Anya kuwa ita ce Sadiyar data sani?

Sai ta sake daka tsalle a karo na biyu, sai kawai taga tayi sama harma ta wuce duka dogayen bishiyun wannan daji, abin ya ɗaure mata kai. Ta sake dirowa taga babu abin da ya sameta.

Ta sake daka tsallen nan a karo na uku, kafin ta diro kasa tayi nazarin wannan daji da take taga iyakar ganinta waƴannan bishiyu ne sai dai ƙorama wadda take gudana wadda bata iya hango karshenta ba itama.

"Zakiji mamakin ganina matuƙa" muryar ta sake ambata, a dai dai lokacin da wani mutum dattijo ya keto daga cikin wata duhuwa yana murmushi. Sai dai kuma abin da ya ɗaure mata kai shi ne wannan dattijo da ƙafafuwa huɗu yake tafiya tamkar yadda dabbobi masu kafa hudu suke.

Hannayensa yana amfani da su a matsayin ƙafafuwan gaba kamar yadda yake amfani da ƙafafuwansa a matsayin ƙafafuwan baya... Sannan yana da jela wadda tsayinta yakai tsayinsa a tsaye... Ga wani gemu da yake da shi wanda farine fat babu ko sirkin wata kala a jikinsa inka ɗauke tsakiyarsa da yake da kalar kore shar... Farar fata ne kuma da ace a tsaye yake da tabbas zai ninka tsawon Sadiya sau biyu, tsakanin bakinsa da hancinsa babu wata tazara domin kusan kana wuce hancin lebensa zaka tarar... Kunnuwansa kuwa tafka tafka ne kamar takardar rubutu sa'annan suna motsawa kai kace fifita suke masa... Duk da a durƙushe yake amma hakan bai hana sadiya ganin kirjinsa cike da gashi ba tamkar na ɗan biri...

"Wanene kai?"
Cikin rashin shakka Sadiya ta tambaya.

"Sunana Rubtas dan gidan Zubtar jikan Kubtas... Nayi farin ciki da na zama mutum na farko da ya fara gamuwa da ke a wannan duniya tamu mai albarka..."

"Kaga mallam..." Sadiya duk da tana cike da tsoron ganin yanayin halittar Rubtas amma sai ta katseshi, ta ci gaba da cewa "Ina yan'uwana suke?"

Maimakon ya bata amsa sai kawai taga ya ɗaga hannunsa wanda yake amfani da shi a matsayin ƙafar gaba. Sai ga wani ɗan awarwaro a hannun nasa. Ai kuwa sai ya saka ɗaya ƙafar gaban ya shafi awarwaron take sai ga wani haske ya bayyana a iska yana tartsatse kamar an kunna akwatin TV. Daga bisani sai hoto ya fara bayyana sai ga Hilal da Hamza ɗaure cikin sarƙa an tisa ƙeyarsu dakaru kewaye da su... Ko kaya babu a jikinsu idan ka dauke dan tofe da aka sanya musu don kare al'aurarsu...

"Abin da yake faruwa dasu kenan."
Rubtas ya faɗa cikin yanayin murmushi.

Zamu dakata a nan. sai kuma a shiri na gaba.

Naku
Naseeb Auwal

Ko me kuke tunani dangane da wannan labari?

MAFITA...Where stories live. Discover now