4

9 3 4
                                    

Sadiya ta jinjina kanta game da murmushi ga tsuntsuwa Daira. Daga bisani kuma ta murza wannan ƙarfen da ke daf da idon sahun hannunta. Ai kuwa sai ga taswira map ta bayyana inda take anyi alamar kore nesa da ita kuma wata danja ce take kawowa da ɗaukewa.

Sadiya ta dubi tsutsuwa Ɗaira tace "Yake tsuntsuwa Ɗaira, ki sani cewa a yanda na gani, akwai tazara mai yawa tsakanina da inda yan uwana suke, sannan sai nabi ta cikin kogi, gashi ban iya ruwa ba..."

Ɗaira ta katseta da wata dariya mai ban dariya daga bisani tace "Ceto su ya zamar miki dole muddin kina son komawa duniyar tsagera, fuskantar sarki Guldum ke kaɗai abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba, domin karfinsa ya wuce inda kike tsammani... Domin ba'a taba yin galaba a kansa ba, kuma ya jagoranchi manyan yaƙe-yaƙe... Tun yana waccan duniyar wadda ita ce ainihin duniyar da suke rayuwa yayi ƙaurin suna wajen tsagwaron jarumta da zalunchi. Musabbabin zuwansa wannan duniya kuwa zan gaya miki bayan kin ceto rayuwar yan'uwanki..."

Duka wannan batu da tsuntsuwa Daira take tana tsaye ne akan iska, tana kaɗa fuka-fukanta, yayin da ita kuma Sadiya take sake duba wannan taswirar wannan duniya.

"Ina iya ganin muggan halittu fa a hanyar da zata sadani da yan'uwana, anya zan iya tseratar da yan'uwana kuwa?" Sadiya ta ambata cikin alamun da ke nuna karayar zuciya.

"Daɗina da ke", Tsuntsuwa Ɗaira ta fada lokacin da take sakkowa kan kafadar Sadiya "shi ne... Kina da mutuƙar tsoro, kuma bai kamace ki ba, ki sani dukkanin ƙarfin da kike buƙata an baki shi. Domin kuwa kina da karfin da za ki iya faɗa da zaki ba daya ba ba biyu ba. Kai in takaice miki labari zaki iya tunkarar wani karamin gari ki tashe shi daga aiki... sannan kwarin ƙashinki ba kamar kwarin ƙashinki ba ne a duniyarku, ban san sunan da kuke kiran abin a kimiyyarku ba. Amma dai nasan cewa tabbas a duniyarku ko saman bishiya mutum ya hau yana dirgowa zai iya karyewa. Amma a wannan duniya ko saman tsauni aka hau aka diro bai zama lallai a karye ba..."

Sadiya kawai ta saki baki tana sauraron abin da wannan tsuntsuwa take faɗa, tana kuma tuno cewa kwarai tana da wannan karfin a wannan duniyar...

"Sai dai wani hanzari ba gudu ba" tsuntsuwa Ɗaira da take kafadarta ta ambata yayin da take cakar fuskar Sadiya a hankali sannan ta cigaba da cewa "kada karfinki ya ruɗeki domin akwai halittun da ƙarfinki da na su ba zai taɓa zuwa iri ɗaya ba a wannan duniyar... Kinga, Sarauniyar tsageru ki tashi ki fara tafiyarki domin lokaci ba jira yake ba."

Sadiya tayi ajiyar zuciya tayi godiya ga wannan tsuntsunwa sannan ta nausa ta fara tafara tafiya. Cikin gaggawa duk da dai yanayin yanda take tafiyar yana bata mamaki domin cikin sauri take tafiyar fiye da yanda take daga kafafuwanta, ta tsaya tana mamaki sai kuma ta tuno ashe fa wannan wata duniya ce wadda abin da bazai yiwu ba yana yiwuwa a cikinta...

Haka ta ci gaba da tafiya, idan ƙishirwa ta kamata sai ta tsaya tasha ruwan wannan ƙorama kamar yadda take tsinkar yayan itaciyar da ke gefen wannan ƙorama, hakanan babta riskar wani abu mai cutarwa sai yan kaɗan wayanda gamawa da su ba ya yi mata wahala, abin da yafi bata wahala mutuka shi ne yanda zata cire tsoro daga zuciyarta, domin kusan duk abin da take yi tana yinsa ne a matsayin yin ƙarfin hali...  Kwana ɗaya ya shuɗe gashi yammacin kwana na biyu ya kusanto ga kuma an bata labarin cewa idan yan uwanta suka wuce kwana uku ba tare da an kuɓutar da su ba to tabbas za ai layya da su.

Hakika zuciya da ƙuna
An raba ni da ku yan'uwana
Ga gajiya tabi duk jiki na
Tunanin rashinku yan'uwana
Ina tafe gareku don mu zauna
Muyi aiki mu koma ga dangina

Tana tafe tana rera wannan waƙa, bishiyu kadawa suke tamkar suna takawa ne ga baitukanta, rana da take sararin samaniya sai ta rage tafiya da sauri tana sauraron muryarta...

Kamu telah mencapai bab terakhir yang dipublikasikan.

⏰ Terakhir diperbarui: Sep 13, 2023 ⏰

Tambahkan cerita ini ke Perpustakaan untuk mendapatkan notifikasi saat ada bab baru!

MAFITA...Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang