Hajaratu .............page 48

49 7 2
                                    

*Hajaratu*..................... *page* 48

*By leemert A Rufa'i*

Zuciyarshi cike da fargaba na rashin sanin dalilin kukan ta alokacin da ya zo mata da labarin farin cikin su, iya rarrashi yayi amma tak'i ta dai na kukan, dole ya katse call d'in zuciyarshi a jagule ya nemi wayan kaisah, 2 miss call bata d'aga ba haka ya sake kira a na 3 yayi sa'a ta d'aga, " hello ya fauwaz, ina lecture inna fito zan kira ka" ta katse call d'in ba tare da ta jira me zai fad'a ba, hannu ya jimk'e ya doki table ya rasa ina zai tsoma ranshi.

A b'angaren Hajir kuma kuka tayi sosai, hak'ik'a tanason Fauwaz so mai tsanani amma tasan dole ta hank'ura dashi don aure ba zai tab'a yiyuwa ba atsakanin su, sai yanzu take takaicin kanta take kallon kanta a matsayin azzaluma, me zaisa tabar Fauwaz ya kamu da soyayyar ta haka, me ya hana ta fad'a mishi larurar da take d'auke da ita, hak'ik'a ta yaudari Fauwaz kuma ta yaudari zuciyar ta, don ahalin yanzu ji take bazata iya rabuwa da Fauwaz ba wanda shima kanshi tanada tabbacin abu mai wuyane ya iya rabuwa da ita, afili ta furta lokaci yayi da zan fito fili in fad'awa Fauwaz ina d'auke da cutar k'anjamau koda hakan yana nufin rabuwar mu, amma bazan tab'a cutar dashi in aureshi da wannan larurar ba, hannu takai ta dafe kanta dake masifar ciwo, dak'yar ta iya tashi ta shiga toilet d'in dake cikin office d'in ta wanke fuskan ta, ta dawo ta zauna ahaka ta kammala ayyukan da suka saura mata, ta had'a kayanta, Massinger ta kira yazo ya kwasa ya kai mata a mota, ta biyo bayanshi jiki ba kwari, haka ta isa gidan kai tsaye bedroom d'insu ta shige duk da ta lura yau gidan cike yake da 'yan'uwa ga alama Mu'utaseer ne aka sallamo daga asibiti, kwance ta sami kaisah tana sharar bacci ga alama a gajiye take, bata tadata ba, wanka tayo had'i da alwala tazo ta gabatar da sallar la'asar, tana zaune kan sallaya, Hauwa ta turo k'ofar ta shigo, zama tayi gefen gadon tana jiranta, bayan ta kammala azkhar Hauwa tace " sister Ummi kizo inji Baba, kuma yaya mu'uta ma tun d'azu yake tambayar ki" Hajir tace " toh kice ina zuwa yanzu, yaushe aka sallamo mu'utaseer d'in?" Hauwa tace "tun da safe bayan fitar ku" maganar su ce ta tada Kaisah daga bacci, Hauwa tace "Kaisah yaushe kika dawo banji shigowarki ba?" d'an yamutsa face kaisah tayi had'i da fad'in " yaushe zakiji shigowa ta, bayan yau duk kun hargitsa gida da hayaniya kamar Kasuwa" dariya Hauwa tayi don kwanan nan sun d'an fara shak'uwa dasu Kaisah kuma tasan halin kaisah ba damar kayi magana sai ta mayar ma da bak'ar magana ga shegen tsiwar tsiya, Hajar ce ma ke d'an tankwasa ta har tana d'an fitowa falo suna hira ko ita Hauwa ta shigo bedroom d'insu, hirar ma kaisah bata faye saka baki a ciki ba sai jefi-jefi, wata black abaya ce a jikinta batada wani ado sosai kasancewar komai nata simple ne bata faye son abu mai ado da yawa ba, rigar tayi matuk'ar dacewa da jikinta, da kuma kalar fatar ta, Jan mayafi ne qarami akanta, tace " Hauwa zo muje, keko kaisah ki tashi kiyi shirin zuwa Islamiyya 4 har ta wuce, kin makara ma" daga nan ta nufi part d'in Uncle Hashim, kwance ta sameshi yana kallon TV, kan kujera ta zauna had'i da fad'an "Uncle gani". wunqurawa yayi dak'yar ya iya tashi ya d'an kishin gid'a, har yanzu yana jin bala'in nauyinta a idon shi, sai da yayi gyaran murya sa'an nan ya d'auki remote yayi lowering volume na TV, Ummi ya kira sunan ta, Hajir ta mayar da hankalinta akanshi, tana fuskantar sa, yace " nasan bani da wata sauran k'ima a idanuwanki, kuma ban can-canci yafiyarki ba" Hajir ta katse shi da cewar " Uncle you should stop biting around the bush, go street and tell me the reason why u call me, inaga yanada kyau mu daina magana akan baya, WATA SHARI'A SAI ALLAH".
hmmmm ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, yace "dama batun maganar aurenki da mu'utaseer ne" ji tayi gabanta yayi wani mummunan fad'uwa ahaka ta dake tace " uhm " yace " nakiraki ne in shaida miki na janye wannan maganar abisa wani dalili, kuma idon har kinada wani wanda kikeso ya kwanta miki arai ki kawo min shi na amince zan aura miki duk wanda kike so" cikin mamaki tace "Uncle wane irin dalili ne zai sa ka janye maganar aure na da mu'utaseer bayan kace mutuwa ce kawai zata sa afasa auren" Uncle Hashim baiyi mamakin jin yanda Hajir ke yi mishi magana without respect ba, yace " Ummi na janye maganar aurenku ne saboda yayanki yana d'auke da kwayar cutar HIV positive " d'an zaro ido tayi cikin firgici tace "what?" hannu ta sa ta dafe goshinta tare da mik'ewa tsaye, afili ta furta " ya salam yau zargina ya tabbata" da gudu tabar falon idanuwanta a rufe, bata damu da mutanen dake cikin gidan ba, kai tsaye d'akin shi ta kutsa ta shiga, zaune yake kan kujera sai da ta kai daf dashi ta cira hannuta ta wanka mishi lafiyayyun maruka har Uku, wanda yayi dai-dai da shigowar innah, aiko innah tayi kanta cikin masifa da bala'i, innah ta cira hannu zata wanka mata mari, Mu'utaseer yayi saurin mik'ewa ya shiga tsakanin su inda yatsun Innah masu kama da bushasshen icce suka sauka a kumcensa, fayau sai da yaga wurgawar wani haske, cikin muryar kuka yace " Innah don Allah kiyi hak'uri ki zauna ki saurareni, wallah na can-canci duk wani kalan hukunci da Hajir zata d'auka akaina koda hukuncin ya kasance na kisa ne" tsaye Innah tayi sororo tana kallon Mu'utaseer wanda take tunanin ya samu zautuwa.................

If you are interested in my story please share and comment, it's on whattpad.

08100948996

Hajaratu Where stories live. Discover now