Hajaratu.......page 12

61 9 0
                                    

*Hajaratu*........................page 12

Tana  shiga bedroom ta fad'a kan bed tana dariya, mara sauti, kaisa ta bita da kallo cike da surprise, tace " ke wannan irin dariyar fa meya faru?" Sai da ta gama dariyar ta s'an nan ta mike tsaye tana juyi had'i da fad'an "look at me  baby, wai mu'utaseer zaice yana sona" k'arasa maganar tayi tana dariya itama kaisar dariya takeyi,  tace "ehem why don't you accept him, his handsome"
Zama tayi ta dafa kaisar, sa'an nan tace " sister ni ayanzu soyayya bata gaba na, asalima bana sa ran zanyi aure koda nan gaba ne, don babu wani abu daya ragemin arayuwar nan" binta kaisar take cikin rashin fahimta tace "ban gane ba ya Ummi, me kike nufi da bazaki yi aure ba?" Kai ta d'aga mata alamar eh, tab'e baki kaisar tayi had'i da fad'an " hauka kikeyi sis, har yanzu dai baki sami wanda zuciyar ki take so bane"
Hajir tace "you think am joking koh?" Kaisar tace "yes, and if da gaske kikeyi meye hujjarki na fad'an haka, there must be reason about anything" "tashi Hajir tayi tana fad'an " nan gaba zaki fahimta".

Mu'utaseer koh bedroom d'inshi ya shige ya rufe kanshi, zaune yake hannunshi dafe da kai, zuciyarshi tana ci gaba da harbawa, meyasa Hajir bata bashi amsa ba, meyasa zuciyarshi ta kamu da sonta after all abunda ya faru, lallai mata suna suka tara, wata irin wutar so da sha'awar hajir ke k'unar zuciya da ilahirin jikin shi,   a fili ya furta "inkin san wata baki san wata ba, wallah dole in mallakeki hajir kota wacce hanya ce" tashi yayi ya fito bedroom d'in direct part d'in Baba ya nufa, ya tura k'ofar ya shiga bako sallama, zaune ya sameshi a falo yana kallon labaran kebbi tv na Hausa, kujerar dake facing d'in baba ya Zauna, shuru na d'an min tuna, Baba ya kawar da shurun da fad'an "ya dai, d'an baba me kakeso na lura da kai kwanan nan kana cikin damuwa?" Cikin gadara yace "Baba akan maganar aure ce wadda ka jima kana yi min" Baba ya k'ara gyara zama had'i da fad'an "ina sauraron ka" mu'uta yace "toh yanzu dai na shirya, zanyi aure don na sami yarinyar da nakeso, kuma banso maganar tayi tsawo very soon nake so ayi auren" dariya Uncle Hashim yayi irin tasu ta man ya acikin zuciyar sa kuma dad'i da bargaba ne kwance, yace "wacece yarinyar da kakeso, wane mahaifinta, kuma a ina take?".

Kai mu'utaseer ya d'an sosa had'i da fad'an, "ba kowa bace illa 'yarka Ummi, Hajir ta nan gidan"  baki Uncle Hashim ya washe, had'i da fad'an Alhamdulillah dama na dad'e ina yima kwad'ayin ta, yanzu sai kaje ku gama dai-dai ta kanku wan nan da wata d'aya ma sai a d'aura auren ku kai da ita" cikin murna mu'utaseer yayi hugging d'in baban shi yana godiya.

Zuciyar shi fal da farin ciki, ya fito daga part d'in baba ya jima zaune a babban falo yana hira da Innah idon shi yana kan k'ofar d'akin su ko zata fito ya ganta, shuru har magrib dole ya fita zuwa masallaci..............

Leemert A Rufa'i............✍🏼

Hajaratu Место, где живут истории. Откройте их для себя