Hajaratu.........page 16

60 5 0
                                    

*hajaratu*........................

Page 16

Zaune suke cikin bedroom d'insu Hajir tana shirya kayan kaisah  a wardrobe kaisah tana kwance kan bed tana chat, sai dariya takeyi "Hajir tace, wai ba jibi zaku fara exam bane, kika kwanta kina cht, inaga sai amshe wayar nan in fasa shi" dariya kaisar tayi had'i da fad'an "am so sorry my second mum, kin san halin mutumin nawa fa bazai iya jure rashi na a online ba yanzu zai damune da call" tsaki hajir taja had'i da fad'an "ku kuka sani da shiriritar ku, ai kema d'in bazaki jure rashinsa ba" baki kaisah ta turo had'i da fad'an "Uhm Uhm ya ummi nid'in kuma" hajir tace "No me, ki ajiye wayar nan ki tashi zuwa read ko in sab'a miki" wurgi tayi da wayar had'i da fad'an "Oh my goodness, ni kin takurani fa" hajir tace "wata rana bazan takuraki ba, in bani" shuru kaisah tayi tana kallon hajir tears suka zubo mata ta share,   tausayin 'yar'uwar ta ya kamata, goran swan d'in dake kan bed side ta dauko zata kafa a baki da gudu hajir tazo ta karb'e da shouting tace"are you mad, Abunda na kafa bakina akai zaki kafa naki?". baki kaisah ta sake tana kallonta for some second, sai masifa hajir akeyi, "bakida hankali ne, ko so kikeyi kema ki kamu da cutar da nake d'auke da ita?. tana cikin masifar kaisah ta fige robar ruwan ta kafa a gakinta tasha, wani azababben mari ta kifawa kaisah sai da robar ta fad'i ka'asa hannu kaisah tasa ta dafe kumce had'i da sakin gigitaccen kuka, nan take jikin hajir yayi sanyi, zama tayi cike da tausayin kaisah itama hawaye ne ke fita a idon ta, fad'awa jikin ta kaisa tayi sukayi hugging d'in juna, cikin kuka kaisah ke fad'in "habba sis me kike nufi ne, so kike in kyamace ki, kisani ciwon dakecin jikin ki nima yana cin zuciyata, ko kina me kike gudu ya sameni? Karki manta nimafa ina d'auke da cutar da tafi taki had'ari, cutar da ko yanzu zata iya daukar raina, karki manta da kulawarki da taimakonki nake raye,  ki daina damun kanki ko tsoron kar cutar k'anjamau ta kamani, don duk ranar da kika mutu nasan nima bazan k'ara ko da 1 second ba zan biki, mark my word, dama shiyasa kika ware komai naki daban, kina kike gudun in sharing dani?" Ajiyan zuciya Hajir tayi kalaman kaisah sun kashe mata jiki, she is speechless, bayan kaisa taci gaba da bubbugawa had'i da fad'an " kiyafeni sis i didn't mean to hot you, all I mean is to protect you" ta k'asa maganar cikin kuka kaisar ta d'ago daga jikin hajir tana share tears had'i da fad'an "no sis don't cry, Kuka ai ya k'are mana, we have to be strong" hannu tasa tana share tears d'in da suka wanke fuskar hajir, smile ta k'irk'iro itama hajir smile d'in ta mayar mata, kaisa tace "ko kefa, bari inyi wanka inzo ki tayani karatu accounting d'in nan ba ganeshi nakeyi sosai ba, ki k'ara koya min shi" hajir tace "ok".

Wayar  hajir ta shiga ringing, murmushi tayi ganin sunan Fauwaz ya bayyana da pic d'inshi, takai wayar a kunnen
Hajir " hello friend ya akayi"
"normal kawai na kira naji muryanki"
hajir "really"
Fauwaz "yes"
Hajir "ok thanks"
Fauwaz " me zan samu ne?"
Hajir "Me kake so ?"
Fauwaz " ke nake so"
Hajir " stop it ka fara koh"
Dariya yayi had'ida fad'in " am not joking, hajir nake so"
Dariya tayi itama " taka ce ai"
Fauwaz "inama Allah zai mallakamin ita dana more"
Hajir "Uhmm kaji dashi, ya jikin mum?"
Fauwaz " da sauk'i sosai, yanzu na fito room d'inta, batason shan magani"
Hajir " ka kulamin da ita sosai, gobe in mun gama aiki da wuri sai muje na dibata "
Fauwaz "ok Allah ya kaimu"
Hajir "Amin"
Wani irin mumfashi tajiyo yana fitowa daga toilet, sallama tayi da fauwaz ta nufi toilet d'in tana kiran sunan kaisah jin ba amsa yasa ta tura k'ofar da k'arfi ta shiga, wata irin razananniyar k'ara ta saki had'i da fad'an "Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un"..............

Leemert A Rufa'i.......✍🏼

Hajaratu Onde histórias criam vida. Descubra agora