hajaratu.............page 25

77 6 0
                                    

*hajaratu*................page 25

Mama kasa danne damuwarta tayi sai hawaye suka fara gangaro mata, fauwaz yace "zo muje in maida ki gida, tafe suke ba wanda yayi magana har suka isa gida, zaune suke jugum-jugum cen fauwaz yace " mama wai yanzu menene mafita?" Share hawayenta tayi had'i da sauke nannauyan ajiyar zuciya tace " fad'an da yafi k'arfinka ai ido kake sa mishi amma, ni inaji a jikina, yaran nan duk inda suke suna cikin mawuyacin hali, musamman kaisah wadda ke kwance rai a hannun Allah" kasa k'arasa maganar tayi ta fashe da kuka, fauwaz yace "mama kuka baida wani amfani anan we have to find a solution" tace "wane solution, sanin kankane bamuda wani k'arfi ko ikon da zamu iya yin wani abu akai" sauke numfashi fauwaz yayi had'i da fad'an "toh mama me zai hana mukai maganar nan ga hukuma?" Murmushin takaici mama tayi had'i da fad'an "hukuma kuma fauwaz inmunje me zamu fad'a musu, bamuda wani iko akan yaran nan kuma sanin kan kane koda munada iko a k'asar nan tamu talaka bai isa yayi dogon motsi ba, koda an takashi sai dai ya barwa Allah, yanzu abu daya zamu iya wanda nake ganin zai taimaka" gyara zama fauwaz yayi had'i da fad'an "mene wannan abun ?" Mama tace " gobe litanin zamu d'auki azumi, muyi talata, narba da kuma Alhamis, acikin wad'an nan ranakun kuma inaso muyi saukar Alk'ur'ani mai tsarki daga k'arshe mu rok'i Allah akan duk inda wad'an nan yaran suke ya kub'utar dasu, ya tseratar dasu, ya kuma Bawa kaisah lafiya, ina ganin hakan shine kad'ai mafita , don wallahi ina zargin k'anin mahaifin nan nasu" fauwaz yace "insha Allahu mama haka zamuyi, ina Alfahari da samun uwa tagari irinki".

Mu'utaseer ba k'aramar damuwa ya shiga ba, rashin Hajir, koda ya tambayi baban shi sai cemishi yayi, " ta d'auki kaisah sun gudu Maiduguri uwin dangin mahaifiyar su, duk irin k'ok'arin da yakeyi akan su bata gani ba, saboda haka babu wanda zai bisu, kuma kar wanda ya sake yin maganar su agidan nan" jiki ba kwari mu'utaseer ya koma part d'insu bedroom d'in Innah ya shiga ya sameta kwance tana call, zama yayi harta gama, tace "lafiya ka zomin d'aki gaka sukuku kamar wanda akayiwa mutuwa?" Yace " Innah yanzu kina ganin abinda baba yayi ya kyauta kenan, ya saki yaran nan su biyu kawai zuwa maiduguri, kuma yace kar wanda yayi maganar su ko ya nemesu, kijifa halin da kaisah take ciki?" Tsaki Innah taja had'i da fad'in "kaga inhar ba wata maganar arziki ta kawoka ba, to don Allah ka tashi ka fita min d'aki" zai sake magana tace "kaga inbaso make in sab'a makaba ka tashi kabani wuri, dacen daya d'aukosu shawara yayi dani, shi yaji yana iyawa, yanzu kuma sun bujire misgi, ina ruwana?" Hawayen takaici ne suka gan garo mishi, cikin ranshi yace "nikam banyi dacen iyaye na gari ba, shiyasa rayuwata gaba d'aya a gurb'ace take" tashi yayi ya fita had'i da ja mata k'ofa, bedroom d'inshi ya shiga yayo banging door, ruf da ciki ya fad'a saman gado yana kuka kamar wani yaro, wutar so da tausayin Hajir fal azuciyar sa.

Hajir dakyar ta iya jan k'afa ta shiga toilet tayo alwala tazo yin sallah amma babu hijab ko gyalen da zata sutur ta kanta, rakub'e tayi agefe sabbin hawaye suka k'ara gangaro mata, ga hannunta still yana mata azabar ciwo, ga yunwa na addabar ta, don ko kallon ledojin da mutumin ya kawo batayi ba Balle ta bud'e taga meke ciki, d'aga kai tayi sama tana kuka tace "Ya Allah kai kad'ai nake bautawa kuma gareka kad'ai nake neman taimako, Allah banda k'arfi banda dabara, Allah kai mai ikone akan komai, Allah inhar mun aikata wani aikin laifi wanda yasa ka jarabcemu, Allah ina rok'onka da sunayen ka kyawawa Allah ka gafarta mana ka kub'utar damu daga hannun wannan azzalumin ba naka" ka'ara rushewa tayi da wani irin kuka mai cin rai, hannun ta dake ciwo ta d'auka ta qara bugashi ga bango, had'i da kwala wata irin k'ara" duk abinda takeyi mutumin nan yana zaune yana kallonta da CCTV, duk da kasancewar shi Christian yaji tausayinta ta ya dira a zuciyar shi, rutse ido yayi sosai hawaye suna bin kumatun shi, bai tab'a jin tausayin wani mutum a rayuwar shi ba kamar wannan yarinya,

Allah sarki kaisah tun bayan tafiyar Hajir babu wanda ya lek'a inda take sai bayan sallar magrib mai gadi ya tafi masallaci, baba ya lallab'o ya shiga bedroom d'in su ya nad'ota cikin bedsheet ya fice part d'inshi da ita, d'akin shi na tsafi ya shinfid'ata, had'i da fad'an "toh yanzu kam matsalata ta kau" ya janyo k'ofa ya rufe.........

Leemertu.............✍🏼

Hajaratu Donde viven las historias. Descúbrelo ahora