Hajaratu.....page 22

61 6 0
                                    

*hajaratu*.................page 22

Dakyar doctors d'in suka amince aka mayarda kaisah gida, amma da sharad'in bayan kwana biyu duk doctor zaizo ya kara mata jini kamar yadda suke mata acen, har yanzu tana nan a matsayin patience d'insu, Uncle ya amince da haka, cikin  ambulance aka  sakata, suka bi bayansu sai gida mutanen gidan ma da sauran mutanen anguwa sun d'auka ko kaisa ta rasu ne, in ka dubi kaisa sau d'aya dole ka zubda hawaye indai har kanada imani, duk tayi duhu tayi rama sosai, haka aka shifid'ata kan gado kamar gawa,  tare da mamar fauwaz suka dawo gidan, batayi mamakin irin halin ko in kula da inna ta nuna ba, sai ma wani kallon kyama da take binsu dashi, yaranta ma da suka taras falo suna hira ba wanda ya ce musu uffan, mama ta taya hajir suka gyara d'akin tsaf, ta fesheshi da turare, tarin kayan wankin su mama ta tattara ta kulle cikin bedsheet, tace "ki kira mai wankinku yazo ya kwashi kayan nan" hajir tace "toh mama bari inyi sallah in diba harabar gida ko zan ganshi" toilet ta shiga tayo Alwala ta fito itama mama Alwala tayo, bayan sun kammala sallah ne, mama ta ciro wani d'an k'aramin littafin azkhar mai dauke da ayyatusshifa tare da wad'an su muhimman addu'oi wad'an da ake karantama maras lafita ta mik'ama hajir tare da mp ta mik'ama hajir tace "akwai complete Qur'an aciki, inaso kullum ki kunna shi a d'akin nan, musamman suratul bak'ara da Ali-imran safe da yamma azkhar d'in kuma shima safe da yamma zakiyi kina shafe ta dashi, kinji" cikin ladabi hajir ta karb'a tare dayin godiya, mama tace "ni zan tafi, kuma insha Allah akwai wani bawan Allah dayake bada taimako na matsala kowacce iri ce zan je in sameshi inyi mishi bayani, ko akwai wani taimako da zai iya bata" har k'ofar gida hajir ta raka mama, don mama tak'i yadda hajir ta kaita gida a mota, acewar ta in suka tafi wazai kula da kaisa don itakam mama sam bata yadda da inna ba,

Hajir tana dawowa daga rakiyar inna, tashige bedroom d'insu agajiye ta fad'a saman bed, mp d'in ta janyo ta kunna suratul bak'ara a bedside ta ajiyeta gefen kaisa, ahankali sautin karatu ya garwaye room d'in, hajir najin nutsuwa tana saukar mata cikin zuciya,  ido rufe take bin k'ira'ar har bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita.

A bangaren Uncle Hashim koh sai murna yakeyi ganin sundawo gida yanzu baida wata fargaba, ya matsu dare baiyima ya shiga d'akin bautar sa, yanaso ya gana da dodo first yake wace wanga zai bullo don kawar da tunanin Hajir, don yanzu inhar baiyiwa tufkar hanci ba zata fara nemawa kaisa magani daga nan kuma zata iya dacewa da wanda zai fasa kwan sa, asirinsa ya tonu,

Mu'utaseer ba k'aramar damuwa ya shiga ba ganin yadda shak'uwa mai k'arfi ta k'ullu tsakanin fauwaz da Hajir, har yake hango zallar soyayya da suke nunawa junansu, ga maganar aurensu an jingineta gefe har sai kaisa ta warke...................


Leemert A Rufa'i............✍🏼

Hajaratu Donde viven las historias. Descúbrelo ahora