Hajaratu......page 10

77 8 0
                                    

*Hajaratu*...................page 10

Fauwaz Zaune yake cikin office, ya kasa aiwatar da komai, sai tunani khaleel ya fahimci halin da abokin aikinsa yake ciki kusan 1 week baya baida wani kuzari, kuma yasan abinda ke damunsa duk da bai fad'a mishi ba, rashin ganin Hajara ne, murmushi khaleel yayi had'i da dafa kafad'ar shi, "haba fauwaz zaka zauna kana abu kamar ba namiji ba, yarinyar nan mutumce fa kamar kai, amma ka kasa fuskantar ta ka fad'a mata, sai dakon wahala kakeyi a zuciyar ka, ka dibi fa yanda kabi ka wani sukukuce d'an 8days d'in nan dakayi baka ganta ba, ka zauna nan kana zurfin ciki har wani yazo ya rigaka" wata raunanniyar ajiyar zuciya fauwaz ya sauke had'i da fad'an " ba haka bane abokina, Hajir tafi k'arfina, ta ko ina tafini ilimi wayewa ga uwa uba matsayi nan company sune nake aiki, kuma ina k'ark'ashinta, sa'an nan kafi kowa sanin kyawawan mata irin su Hajir ba ajin mu bane talakawa, gara kawai in rufama kaina asiri in rungumi jarrabawar da Allah ya d'ora min" " k'irjinshi khaleel ya doka had'i da fad'an "kazama namiji mana, shi so babu ruwanshi da duk wad'an nan abubuwa daka lissafo, indai har tayi na'am da soyayyarka anwuce nan, nidai shawarar da zan baka itace kaje ka tunk'areta kawai" fauwaz yace "ta yaya zan tunk'areta yarinyar da takeyima kowa kwarjini, dama irin mai d'an sakewa tayi hira da mutane ce" kaleel yace "da haka kuma tanada i don't care attitude, still ka rutsa nawa, kaifa namiji ne kasan duk wata hanyar da zakabi ka samu abinda kakeso" fauwaz yace "toh zan nemi mafita, don wallah tayimin d'aurin da bazan iya kwance kaina ba" kaleel na cikin yi mishi dariya ya hangota, hannu yakai ya tab'a fauwaz "kai nawan gafa mutuniyar nan tafe"  daganan kaleel yayi gaba, lumshe ido yayi tare da shak'ar dadda d'an k'amshimta lokacin da tazo wucewa kusa dashi, kai tsaye office d'inta ta nufa, aiki sosai ta taras babu wani abu da m'utaseer ya barkata, sai kud'ad'e da yawa da suka fita ta hanyar sa, ga wani baban contract data   wahala sosai akansa ya janyo sunyi asarar sa, tsaki taja had'i da fad'an ni wannan masifa dame tayi kama, haka ta kwashe wuni cur tana tana abu daya, tare da taimakon fauwaz, sai 4pm suka tashi dukda yau tana fama da matanan cin ciwon mara wanda in ya motsa mata takan cije leb'e kota d'ora kanta saman desk, duk wani motsi nata fauwaz yana lure da ita, sai dai inya tambeta tace kanta ke ciwo, gashi yaune rana ta farko da bakinshi ya fara had'uwa da nata, kaleel ne ke aiki tare da ita, yau plan ya had'a ya turo mata fauwaz da sunan baijin dad'in jikin shi, sosai fauwaz ya iya aiki He's very hardworking person wanna shiya birge Hajir dashi, arayuwa batason malalacin mutum tafison , mutum mai nagarta, jefi-jefi suke hira,  sosai take mishi kwarjini yarinyar tasan kanta. yaji ta k'ara shiga ranshi, tare suka fito, sun jero sai kace wasu sabbin masoya, tun daga nesa mu'utaseer ya hangosu, ranshi ne yayi mugun baci hannayen ya hard'e fuska ba annuri, Hajir agajiye take ko kallo bai isheta ba, wurin motar ta ta nufa fauwaz na binta d'auke da system d'inta ta bud'a mota ta amshi system d'in ta saka aciki sai alokacin ta hango mu'utaseer wanda ya tsareta da ido kamar tsohon maye, kallon fauwaz tayi cikin muryar gajiya tace "thanks so much fauwaz zan tafi Allah ya hutas da gajiya" shima murmushi yayi had'i da fad'an "toh sai gobe Allah ya tsare hanya" ta shiga ya rufe mata k'ofa, hannu ya d'aga mata itama ta d'ago mishi fuskarta d'auke da lallausan murmushi wanda ya kusa narkar da fauwaz, tana wucewa fauwaz ya sauke wani k'aton numfashi had'a dora hannunshi akan k'irji, mu'uta dake tsaye kamar gunki yana kallonsu, afili ya furta "shege gama kazo nan inci ubanka" Hajir ko dariyar k'eta ta rink'ayi a hanya don ta hango kishi bayyane a fuskar Mu'uta kuma shiyasa tayi hakan, juyowar da fauwaz zaiyi sukayi ido biyu da mu'utaseer.........

08100948996

Hajaratu Where stories live. Discover now