PART FIVE AND SIX

330 27 1
                                    

🪦🪦 *WAYE SANADI?!* 🪦🪦

           *By*
*Ummu Sumayya*
*Wattpad Bintubaby*

*PAGE FIVE AND SIX*

"Mekike nufi Haulat yanzu duk yanda nake baki amanar kanki saida kikaci Haulat nizaki tozarta kije wani yamiki ciki sannan kidawo garenk wallahi tallahi kinji na rantse saikin barmin gidana yanzu basai anjima ba kije idan kin haihu ya aure ki maza kitashi kibarmin gidana yanzun nan" ta'karisa maganar cikin hargagi da tsawa tana nuna ma Haulat d'in k'ofa,
Cikin wani irin yanayi Haulat tayi kneeling tana ri'ke kafar Maman ta amma takasa cewa komai saboda yanda kuka yaci k'arfin, wani irin hankad'a ta Mama tayi kafun cikin takaici kuka yana kufce mata tarufe Haulat da duka iya k'arfin ta tana fad'in "wallahi gwamma inkashe ki da wannan abun kunyar dakika kwaso min natsane ki Haulat haihuwar ki bataimin rana ba da haihuwar ki gwara b'arin ki"
Gaba d'aya tarikice dukan Haulat take iya  k'arfin, Salma dake gefe tana kuka itama ganin Maman zata illata Haulat ne yasa taje da'kyar takwace ta, cikin takaici takalle su suduka biyun tace "wallahi kafin na irga biyu kisa tabarmin gidana inba haka ba wallahi saina kashe ki da hannu na dan bazan zauna ahaifa min d'an gaba da fatiha ba tatafi gidan su Aliyun can tazauna inta haihu suyi auren yaron nan yacuce ni nan yazo yadinga min dad'in baki nabarki kikaje makarantar nan ashe cuta na zaiyi Allah ya isa tsakanina dashi bazan ta'ba yafe mai ba" tana gama maganar fuuuu tayi d'aki tana sharar k'wallah,
Sosai Salma take kuka ganin kamar Haulat bata numfashi hakan yasa tatafi randar k'asar su tad'ebo ruwa tazo tashafa mata har kusan sau uku sannan tayi ajiyar numfashi gaba d'aya numfashin nata yacanza daga yanayin dayake futa zaka gane tana cikin wani hali kafun salma takai ga magana saiga Mama tafuto da hijab ajikinta tana zuwa tami'kar da Haulat tsaye sannan takama hannun ta tajata sukai waje layi na d'iban ta cikin sauri Salma tasa hijab tabisu har lokacin bata bar kuka direct gidan su Aliyu taga sun nufa kasantuwar layi d'aya suke sauri sauri tabisu ganin yanda Haulat ke layi amma Mama bata damuba sai janta take.

****

Ammi nazaune ad'aya daga many'an kujeru palourn ta ga y'ar aiki tana ta matsa mata k'afa hannun ta ri'ke da tuffa tanaci tana kallon TV hankalin ta kwance,
Wani irin shigowa palourn Mama tayi babu KO sallama ranta amugun b'ace ta ingiza Haulat kan Ammi tana fad'in "ga irin tanan tun farko ban so makarantar nan ba na nuna bana so d'an ki yadage yadinga min dad'in baki ashe cuta ta yakeson yi to ga abunda yafaru nan yabita har makaranta yad'irka mata ciki saiki san yanda zakiyi da inta haihu inzakuyi biki kwa gayyace mu" tana kaiwa nan amaganan ta tajuya xata futa afusace amma saita tsinkayi muryar Ammi na fad'in,
"Dakata malama kina tunanin zaki xo gida na ne kicimin mutunci agaban y'an aikina sannan kice zaki tafi batare dakin karb'a hukunci ba eyee"
Cikin tsaurin idanu Mama tajuyo takalle ta tace "abunda d'an ki Yashuka ne dole ku girba tare"
Tana kaiwa nan tafuta daga palourn,
Salma ne taduk'a har k'asa tacema Ammi "Dan Allah kiyi ha'kuri Ammi badan halin muba"
Tsaki Ammi tayi tahankad'a Haulat ranta amatuk'ar b'ace tace "kitattara y'ar uwar ki kubarmin gida na yanzu nan bance taje wani yama ta ciki ba balle amak'ala ma d'ana dan anga baya gari kawai daga taimako sai ace nice sanadi to bafa zai yiwwu ba mtssss" tasake jan wani wawan tsaki ta aje tuffan hannunta tai cikin gidan,
Sosai Salma ke kuka taitayan Haulat tayi da jikinta ba wani k'arfi suka bar gidan, gaba d'aya Haulat bata san ma awace duniya take ba batajin komai bata gane komai ahaka sukaje gida daga bakin xaure Mama tatsare su tace "tunda ke kinji kin gani kince zaki taimaka mata ohyy kujiya kubarmin gida na dan bazan zauna da mazinaciya ba harda cikin shege kai Allah ya isa tsakanina dake Haulat kincuce ni" saita fashe da kuka gunun ban tausayi Cikin kuka salma taduk'a tace "Mama kitaimaka mana kinsan bamu da kowa aduk duniyar nan daga Allah sai manzon sa saike ina kike tunanin zamuje kece dolen mu duk abunda yafaru musaka shi a mezanin kaddara domin bawa bai isa yakauce ma kaddarar saba kitaimaka mucinye kaddarar nan data tun karo mu domin koda kin kore Haulat batasan ina zataba tana iya xuwa tafad'a wani halin dabai dace ba kiyi ha'kuri tabbas abun da ciwo kiyafe mata domin fushin ki agareta babban bala'e ne balle dama ga zunubin abunda ta aikata kiyi ha'kuri Mama bamu da kamar ki duk duniyar nan"
Sosai kikin Mama yayi sanyi duk da shaid'an yanata zugata amma saita fi k'arfin zuciyar nata yahanyar maimaita  innalillahi wa-enna ilaihirraji'un zama tayi tana sauke ajiyar zuciya tsayin lokaci kafun yashare hawayen fuskarta tace "haka ne salma na gode da tunatar wannan naki Allah yamiki albarka"
Da amin ta amsa sannan tad'auki Haulat takaita d'aki ruwa tadinga shafa mata amma numfashin fa yayi k'aura wani ihu tafasa dayasa Mama tashigo d'akin afujajan ita kanta dataga yanayin Haulat d'in saida ta rude dasauri tace "kamota mutafi asbiti"
Da'kyar suka kamata suka futa Allah yatai makesu suka samu wani mai adaidata ya sauke wasu zai juya arud'e Mama tace "Aminu kano zaka kaimu gyara parking karta mutu dan Allah"
Ganin yanayin tane yagyara musu suka shigarda Haulat d'in sannan yaja suka tafi Mama sai kuka take kamar me (tabbas tsakanin d'a da uwa sai Allah)
Suna zuwa aka amshe ta emergency akafara dubata gaba d'aya jigum jigum suka zauna cikin tashin hankali,
Kusan awanni biyu sannan Dr yafito yana son ganin Mama koda tazauna yakalleta dakyau yace "meyasa kika bud'e ma y'ar ki idanu tafara zubar da ciki yanzu gashi mahaifanta yasamu matsala"
Cikin tashin hankali Mama takafe Dr da idanu kafun tace "Dr kana nufin tazubar da cikin jikinta dama Alhamdulillah Allah na gode maka Allah ka k'ara rufa mana asiri duniya da lahira"
Galala Dr yayi cikin takaici yami'ke yana tura mata takarda yace "muna bu'katar magungunan nan yanzu zamuyi amfani dasu"
Dasauri tad'auki takardan tabi bayan Dr d'in salma ta aika gida tad'auko kud'i da tabarma sai pilo da za'a kwanta adaren sukai ciku ciku itada Salma suka biya komai na hospital d'in dan Salma har wayanta ta saida sosai Haulat tabasu tausayi inda suka jingum jingum gefen gadon ta suna kallon yanda take sauke ajiyar zuciya ga numfashin ta yana futa da'kyar babu wanda yaruntsa acikin su har safiya tayi bayan sunyi sallah ne Salma tasiyo waina taci biyu da'kyar ta aje sauran cikin damuwa take kallon y'ar uwan nata hakama Mama takasa cin komai tana ganin kamar itane taja ma yar ta data karb'a kaddara tun farko da ba hakaba sha d'aya daidai Haulat tafarka tana kallon d'akin saikuma ta lumshe idanun ta tabud'e ahankali tafurta "ruwa" Salma dake gefe tami'ke cikin sauri tace "ruwa bari dai na kira Dr" tana kaiwa man amaganar ta tafuta daga d'akin tare da Dr d'in suka dawo yaduba Haulat d'in sosai sannan yace "zaku iya bata amma kad'an kuma mai d'an zafi sannan abata vegetables dan jinin ta yayi k'asa sosai" kai Mama tajinjina tana mai godiya yafuta tea Salma tahad'a Mama tabata tana tayi mata sannu,
Kwanan Haulat biyu a hospital d'in tad'an maro tunda tadawo hayyacin ta take kuka har saida Mama tanuna mata zatayi tafiyarta muddun bata kwantar da hankalin taba,
Dole tacire damuwa azahiri amma aranta zafi da rad'ad'in cin amanar da akai mata yana damunta lokaci d'aya Khadija tazamo sanadin rasa farin cikin ta da karatun datake da buri akan shi sosai Salma da Mama suke k'ok'arin bata abubuwan k'arin jini dan har tausayin su takeji dan tasan matsalar su bashi garesu ba kuma azaman hospital d'in ba k'aramin kud'i suke kashewa ba hakan yasa take d'an k'arfafa jikinta take nuna musu taji sau'ki.
Kwanan biyar aka sallameta suka dawo gida sosai Mama da Salma suke kula da ita basa so suga tazauna shiru kuma sukanyi k'ok'arin faranta mata sosai Mama aiki take zuwa awani gida dake Dab'ai sabuwar madina Salma kuwa koyawar take a wata makaranta kasantuwar ta kammala secondary d'in ta kuma Allah bai kawo mata miji da wuri ba insuka tafi takanci kukanta tagode Allah amma kuma ta fawwala ma Allah lamuran ta tana ta istigfari.
*After two years*
Rayuwa taci gaba da tafiya watarana dad'i wataran kuma akasin hakan amma kuma koda yaushe idan kasa ha'kuri arayuwar ka yakan zama sanadiyyar farin cikin ka Haulat tana zaune tsakar gida tana yanke ma Mama farce yayinda Salma keta aikin abinci suna ta fira jifa jifa wani yaro ne yashigo gidan da sallama yace "Aunty Haulat ana kiran ki awaje"
Kallon yaron tayi kamar bazata tanka ba saka makon tunda tadawo makaranta tadaina kula kowa Mama tayi fad'an tayi fad'an amma ta'ki muryan Salma taji tana fad'in "jekace gata nan zuwa"
Dasauri yaron yajuya yatafi, du'kar dakanta tayi k'asa tana share hawayen daya zubo mata dan tsoronta bai wuce tayi aure miji yace yajita ba abudurwa ba kwanaki kadan yasako ta Mama ne takalle ta ranta ad'an b'ace tace "tashi kije kuma kika kuma koran wannan ma wallahi saina sa'ba miki dan naga ku baku da kishin zuci kunfi so naita jerawa daku akasa banbance waye uwa balle y'a mtssss tashi kibani waje dalla"
Asanyaye tashiga d'aki tad'auki hijab d'in Salma tazumbula dan yanzu kayanta duk Salma ne tabata wasu dan nata Dija ta kwashe'
Bata shafa ma fuskan ta komai ba tafuto fuu ta wuce su tafuta waje kanta a'kasa ta'karisa inda tagan shi atsaye abakin moto atsorace tad'ago kanta jin wani irin k'amshin da bazata ta'ba mantawa ba arayuwar ta murya na rawa ta furta "Aliyu!?"..............✍🏻

WAYE SANADI!?√√ BOOK ONETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon