🌺🌺🌺🌺
*WAYE SANADI!?*🪦🪦*By*
*Ummu Sumayya*
*Wattpad #Bintubaby**SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITATTAFAN HAUSA TV_http://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
*Masha Allah Habibatie😍 am sorry am so sorry once again da late update kaina ne ke min ciwo sosai but Alhamdulillah naji sau'ki sosai masu kira da wad'anda suka ajemin sa'ko inbox nagode sosai domin kune k'ashin bayan nasarata 🔥😍 ibaku babu ni dan haka karku manta akakkab'e zani agayara zama asambad'a min comments da sharing dan Allah ataimaka agantala shi koda group biyu ne na wanda kake ciki🥰 hakan zai k'aramin kwarin gwiwa masoya na ina godiya alkhairin Allah ya cimmuku a duk inda kuke Shamsiyya tana muku son so 😍 fisabilillah🌹💃🏽*
*BINTU KITCHEN INGREDIENTS AND INCENSE*
*Ina kuke ma'abota son k'awata girke girke da sinadaran girki masu k'amshi da sa dad'in girki uwar gida kai harda amarya kuna ina ku masto kusa ku mallaki Bintu curry powder ingantaccen sinadarin girki mai sa girki k'amshi da dad'i curry powder mu yasamu had'i na musamman daga ingantattun kayan k'amshi masu sanya girki d'and'ano har lau Bintu curry powder basu tsaya anan ba sun kawo muku had'add'en yaji dayaji kayan k'amshi mai k'ara lafiya ajiki dakuma had'in daddawa mai sanya miya k'amshi da sa oga santi muna da kitchen ingredients kamar haka*
Curry powder
Garin citta kanin fari dan lipton
Hadd'd'en yaji mai kayan k'amshi
Had'add'en yaji mai tafarnuwa
Had'add'iyar daddawa mai kayan k'amshi
Duka akan farashi mai sau'ki muna turawa ko ina afad'in arewacin nigeria kayan ki su iso cikin salama uwargida amarya maza ku hanzarta siyan *Bintu kitchen ingredients* sai angwada akan san na kwarai! Zaku iya tuntu'bar mu akan wannan number 07017296839*abun bai k'are haka ba akwai ingantattun turarukan mu masu sanyin k'amshi masu dad'i munada turaruruka kamar haka*
Humra
Farar humra
Ba'kar humra
Ja humra
Kulacca
Turaren wuta na kaya
Turaren wuta na jiki
Turaren wuta na tsugunno mai matse mace taciki da waje*Kuna ina amarya uwar gida kai harda y'an mata ma don k'amshi shine mace muna saida d'aya d'aya muna bada sari akan farashi mai sau'ki uwargida amarya karku bari abaku labari zaku iya tuntu'ban mu akan wannan no 07017296839 koda kud'in ka saida rabon ka*
*TWENTY NINE AND THIRTY*
Sallama yafarayi Mama dake d'aki ta amsa tana fad'in "Hamza shigo mana saikace ba'ko" tafad'a tana mik'ewa tashimfid'a mai sallaya yashiga d'akin kanshi aduk'e yazauna akan sallaya,
Murya asanyaye yace "Maama mun same ku lafiya ya taro yatashi?"
Sai taji wani iri da'kyar tak'ak'alo fara'a tace "Alhamdulillah"
Shiru ne yaratsa kowa na k'ok'arin magana amma kuma yakasa da'kyar Mama tace
"Saikuma kaji sa'ko wajen Maman ka KO?"
Bata jira cewar saba tace "kayi ha'kuri da abunda kaji kasa ma ranka haka Allah yatsara komai mu'kaddari ne daga Allah"
Muryan shi amugun sanyaye yace "to Maama amma kince ba'a mata mijiba hasali ma kince da tana da miji tare za'a had'a su da Salma amma tunda bata da tsayayye shine ba'a had'a ba please Maama kifad'a min duk abunda kike so zanyi indai zaki mallaka min Haulat dan Allah"
Sosai yabata tausayi harta kasa magana ta k'ura mai idanu while zuciyar ta na tursasa ta tagaya mai gaskiya watak'il zai ha'kura ahankali tace "Hamza!"
D'agowa yayi yana kallon k'ofa ya amsa da na'am,
"Inaso kayi ha'kuri da abunda zan gaya maka agame da d'an k'anwar mahaifiyar ka da ita kanta k'anwar mahaifiyar taka xan so katsaya kaji labarin nan anatse sannan kayanke hukuncin gaskiya akan *WAYE SANADI!?* tsakanin Haulat da Aliyu dakuma mahaifiyar sa"
Jikin shine yayi mugun sanyi kenan dama sun san juna zuciyar shice tafara bugawa yana ro'kon Allah yasa kar Maama tafad'a mai abunda yafi k'arfin kwakwalwar sa murya na cracking yace "kigaya min Maama ina jinki"
Ajiyar zuciya tasauke tagyara zaman ta tafara bashi labarin Haulat da Aliyu tundaga sanda aka haife ta har kaita makarantar da yayi tatsaya tashare hawayen daya zubo mata tana kallon Hamza da fuskar shi tayi jajir jijiyar kanshi tawani mi'ke tana ta harbawa yak'ura ma waje d'aya idanu kamar me counting d'in wani abu ahankali taci gaba da cewa "Aliyu sai yaci amanata ya yaudari Haulat har yamata ciki aka kore ta amakaranta tundaga lokacin komai na Haulat yatsaya dukkanin farin cikin ta yayi kaura kwatsam saiga Aliyu yasake dawo wa gareta bayan shekara biyu yana k'ok'arin sake yaaudarar ta amma duk yanda naso karta yarda dashi takasa gane abunda nake nufi takasa gane waye samarin shaho Aliyu yasake yaudaran Haulat karo na biyu mahaifiyar shi har nan tazo tacimmin mutunci akan Aliyu tundaga ranar Aliyu bai sake waiwayarta ba har yau kimanin wattani biyu kenan bana tunanin KO awaya ya'kara kiranta yacuci Haulat yabarta da mummunan tabon dana kasa gane *WAYE SANADI!?* atsakanin ita da shi domin tabbas k'arfe d'aya baya amo, abu d'aya nake tsoro shine idan tayi aure karta wula'kanta shiyasa nad'auka d'amarar sanar ma kowaye zata aura kaddarar data afka mata domin babu wanda ya wuce kaddara saidai akan canza tane da k'arfin addu'a tazamo mai sau'ki dan haka ne yasa nak'i amuncewa da maganar dan gudun abunda zai biyo baya amma idan har kaji ka gani to k'ofa abud'e take kaje kama mahaifiyar ka bayanin komai idan ta amince nima na amince katuro magabatan ka ayi abunda yadace awuce wajen" ta'karisa maganar tana kauda fuskanta daga garesa dakuma jiran hukuncin sa a game da labarin dan tasan Zuwaira ta cuccusa musu maganganu marasa dad'i,
Tsaban tashin hankalin daya shiga baya misaltuwa dan yanda zuciyar shi take bugawa inkana kusa dashi zakaji yanda take bugawa fast fast idanun shi sun kad'a sunyi jawur dan kana iya hango hawaye akwance acikin su kanshi wani azababben ciwo yakemai gaba d'aya labarin da Maama tabashi yasa shi cikin wani yanayi da'kyar yafara jan hasbunallahu wa ni'emal wakeem tabbas ayanzu idan yaga Aliyu zai iya kashe shi murus amma kuma abun dubawa shin da yardar ta yayi komai KO kuwa yaudarar ta yayi gaba d'aya yarasa abunda yake mai dad'i murya adake yace "Maama Haulat nake so ba jikin taba kuma koda karuwanci tayi xan aure ta matu'kar tayi taubatan nasuha lada zan samu ayanxu nashirya auran Haulat kuma zanje infuskan ci Mommaa na da zancen cikin fahimta kuma insha Allah zata amince ni"
Cike da tausayin shi Mama tace "Allah yamaka albarka Hamza Allah yashige mana gaba cikin lamarin"
Kanshi a'kasa ya amsa da "amin ya Allah"
Yami'ke yace "Mama zan koma dan inada training da k'arfe 5 insha Allah nima zuwa jibi zan koma Ilorin kamar yanda nagaya miki cost nazo to na kammala gobe zan amsa saka mako nakoma"
Murmushi Mama tayi tace "masha Allah to Allah yasa kaga alkhairi bara naturo maka Haulat d'in"
Dasauri yace "no Maama gobe zan shigo saimuyi sallama" yafad'a yana futa ad'akin dan baya son ganin Haulat ayanzu da zuciyar shi take sama cikin sassarfa yabar gidan yafuta waje kafun ya isa motar shi har anbud'e yana zama yalumshe idanun shi yana tsine ma Aliyu,
Haulat na d'aki duk abunda suka tattauna tanaji taci kuka ta k'oshi ta gode Allah tana ganin abu mawuyaci ne Hamza ya waiwaiye ta watak'il shikenan bazata k'ara ganin shiba kan katifa takwan ta cike da tausayin kanta tabbas Aliyu da Dija sun cuceta sun kaita sun baro koda Mama tashigo d'akin saitayi kamar barci take hakan yasa Mama tasauke ajiyar zuciya tafuta ita kanta yanzu hankalin ta atashe yake da yanda auren Haulat d'in zaizo dan ba kowa zai d'auki wannan abun da yasame ta amatsayin kaddara ba.
Koda yakoma ba training d'in dayaje kawai ya guje ma ganin Haulat d'in ne dan ba'karamin haushin ta yajiba amma kuma yana son jin exactly what's really happen sabida yasan *WAYE SANADI!?* acikin su dan tabbas zai aura Haulat sabida son dayake mata amma kuma sai yagasa ta akan abunda ta aikata na bud'e ma wani k'afa har yamata ciki wata zuciyar ne tace kasani KO dad'in baki yamata iska yakaima naushi cikin fushi yace "Aliyu kashiga gonar da bataka ba kuma zaka d'an d'ana azaba fiye da dad'in da kaji alokacin da ka b'ata rayuwar Haulat" wani irin huci yake kawai yafara jifa da kayan dake d'akin kafun kace me tuni yafara farfasa duk wani abunda yakasance na k'arau ne ga hannun shi yanata zuban jini kan gadon yakwanta yalumshe idanu yana furta "Allahumma ajirnee sabran ya Allah karage min wannan masifaffen kishin" yafad'a yana tattaune halshen shi cikin wani irin yanayi yafurta "Aliyu wallahi daga kai har Ammi dakuka cuci marainiyar Allah saikunyi nadama alokacin da nadamar bata da amafani agareku"
Har aka kira sallar magrib surutai kawai yakeyi gaba d'aya kwakwalwar shi ta hargitse da'kyar yayi sallar magrib acikin d'aki yajima yana addu'a kafun yashafa yanajin zuciyar shi tana sanyi ahankali ahankali waya yakira yace aturo mai nurse da maid ba jimawa akai nocking maid ya tattara wajen nurse d'in yayi treating wajen yabashi magani yatafi,
Gado yahau tunani yace salamu alaikum daya rufe idanu Haulat yake gani ita da Aliyu zaune yatashi cikin rashin sanin abun yi wayar shi yajawo yakira Mommaa suka gaisa shiru yabiyo baya kamun yace "Mommaa you know what?"
Daga can Mommaa tayi shiru saikuma tace "Nasani ta tsuniyar gizo bata wuce ta kok'i Haulat KO?"
Idanu ya lumshe sannan yaja ajiyar zuciya yace "Na binciko komai akan rayuwar Haulat but ban san yazaki d'auki abun ba but am really sure Mommaa na tana da kyakkyawan fahimta"
Murmushi tayi tace "gaya min menene yafaru Major General"
Ajiyar zuciya yasake sauke wa yace "Aliyu shine silar lalacewar rayuwar Haulat"
Nan yabata labari kaf abunda Mama tace mai,
Shiru tayi kamar bazata tanka ba saikuma tace "Hamza kenan kana tunanin wad'annan sun isa hujja ne bazai yiwwu ka aura Haulat ba dan mahaifiyar ta tace ammata miji kuma koba hakaba bata da future mai kyau da za'a so had'a zuri'a da ita k'yan d'an maciji ne gareta ka kiyayi kanka bana son kasake min maganar Haulat"
Cikin wani sabon tashin hankali yace "Mommaa dan me yarinyar nan jarbata ce tafad'a mata sannan dakuma kaddarar rayuwa bawa bai isa ya kauce ma kaddarar saba yanzu ace kina da yarinya haka yafaru da ita wata tahana d'an ta ya aure ta yaxakiji?"
Cikin takaici tace "Hamza kai yarone bazaka gane abunda nake nufiba sai nan gaba kad'an kamance maganar Haulat ariga anbada ita koba'a bada itaba bazaka aure taba dan haka karka kuskura ka k'ara min maganan ta this is the last warning!"
Gaba d'aya sai yaji duniyar tana jujjuyawa dashi har bai san sanda Mommaa ta yanke wayar ba shin meyake shirin faruwa dashi daren ranan barci kaurace mai yayi yanda yaga safiya haka yaga dare.
Washe gari da yamma yazo gwammaja bai shiga ba ya aika aka kira mai Haulat gaba d'aya yace escort d'in su shiga mota shi kad'ai ne a motan yana zaune idanun shi ak'ofar gidan.
Haulat kuwa wunin ranan sukuku tayi shi bata da kuzari KO kad'an abinci ma saida Mama ta matsa mata sannan taci da yammacin ranar ne tayi wanka dan zuwa gidan Aunty Salma tagama shiryawa kenan yaro yagaya mata sa'kon atunanin ta Ahmad ne hakan yasa tama Mama sallama tafuta Mama tamata gargad'i dakarta kai dare takuma kula dakanta ta'kara mata da addu'a futa tayi tana weaving d'in Maman kamar wata k'aramar yarinya lokacin data fito tayi arba da motocin sojojin dasuke fake ba'karamin bugawa zuciyar ta tayiba juyawa tayi tafara tafiya kamar bataga motocin ba cikin natsuwa take tafiya ahankali ba zato ba tammani motocin suka sha gaban ta tsayawa tayi tana d'an rolling idanun ta gamida kallon wani gefe daban wani soja ne yazo gaban ta cikin girmawa yace "Madam Oga yana magana"
Murya asanyaye tace "OK"
Gaba yayi tabishi suka k'arisa yabud'e mata motar shiga tayi kanta a'kasa dasauri yakulle motar yatsaya yanata maxurai gaba d'aya duk sojojin suna zagaye da wajen dan bada tsaro aiko nan da nan y'an layin suka natsu aka koma inuwa ana kallon ikon Allah yayin da wasu suketa k'ananun maganganu,
Kallon ta yayi k'asa k'asa murya a'kasan mak'oshi yace "Ina zakije da yammacin nan?"
Kanta a'kasa tace "wajen Aunty Salma"
Kallon ta yayi sosai yace "dare yayi ki koma gobe zan turo akai ki"
Baki tad'an turo tana satan kallon shi tace "na gaya mata zanxo fa tun d'azun take tamin waya kuma kace na koma uhm"
D'an zaro idanun shi yayi yace "bazaki koma ba kenan?"
Dasauri tace "to yazanyi nagaya mata zanje fa"
Baki yad'an cije yakalleta dakyau saikuma yakauda kai yace "address?"
Fad'a mai tayi yagyad'a kai kawai ta waya yatura ma driver text saigashi yashigo kusan two minutes motocin suka fara moving ahankali suka bar layin saida suka hau kwalta sosai yakalleta yaga tana ta wasa da fingers d'in ta kanta a'kasa murya can k'asan makoshi yace "Baby gobe zan tafi"
Wani irin kallon gefen idanu tamai jin yakirata da Baby baki tad'an tab'e cikin KO inkula tace "oh Allah yatsare"
Tsura mata idanu yayi yace "gaya min zakiyi missing d'ina?"
Wani irin bugawa zuciyar ta tayi tad'ago kanta aiko karaf idanun su suka sark'afe kusan one minute suna kallon ido cikin ido kafun takauda fuskan ta zuwa glass tana kallon titi,
Shiko cikin shau'ki yawani lumshe idanun shi yace "Haulat ina sonki this is the second time dazan koma soyayya ada nayi amanna nadaina soyayya saigashi kaddarar auren ki takuma hadamu Haulat kitaimaka zuciya ganin naxo gareki da k'ok'on bara ki amince da soyayya ta kimanta da duk abunda yafaru abaya kirungumi rayuwar ki ta yanzu dan babu wanda ya isa yatsara makansa rayuwa sai abunda Allah yatsara maka tunkan kaxo duniya mukan canza kaddarar mune da k'arfin addu'a saita zo mana asauk'ak'e"
Tunda yafara magana hawaye ke roiling afuskarta gaba d'aya sai takejin ta wani iri yanzu aya yake kallon ta shikenan Aliyu yagama da rayuwar ta ya cuce ta wani irin fashewa da kuka tayi,
Ajiyar zuciya yasauke yanajin dama shine yake kukan nan daya rage kaso tamanin na k'uncin da zuciyar shi take hankie yami'ka mata cikin lallashi yace
"Baby sorry ban san maganganu na zasuyi hot d'in kiba da ban fad'i ba am sorry once again gashi kishare fuskar ki"
Ba musu ta amsa hankie d'in tashare hawayen daya gama b'ata cute face d'in ta,
Murya asanyaye kamar me rad'a yace "kece zab'in raina babu wata bayan ke insha Allah zaki zama matata mallakina Haulat tell me do you luv me?"
Wani irin kallon shi tayi zuciyar ta na bugawa tafara k'ifa idanu kamar zata sake yin wani kukan,
Kanshi yalangwab'ar yace "Haulat am in luv with you tun daga ranar dana fara ganin ki Haulat kin zama bugun numfashi na kece tunani na kece mafarkina kuma kece nake gani azahiri Haulat ban san iya adadin son da zuciya da ruhi na suke miki ba kuma tabbas baki da wani miji bayan ni domin ke tawa ce nima nakine kisa hakan aranki komai daren dad'ewa saimun mallaki juna domin ruhina da naki tare aka halicce su kitausaya min ki amshi soyayya ta mugina rayuwa mai tsafta" ya'karisa maganar yana kallon ta,
Yanda zuciyar tane take bugawa yatilasta mata rufe idanun ta gaba d'aya jinta take tana yawo cikin gajimare tabbas Hamza shine yadace da rayuwar ta amma kuma bazatai saurin sakin jiki da shiba,
Idanun shi yakauda ganin kamar maganganun sun mata wani iri yace "Kiyi tunani daga nan zuwa lokacin dakika shirya amsan soyayya ta koda yake nasan kina sona right?"
Bata san sanda ta bud'e idanu ta watsa mai wani shegen kalloba ta tura bakin ta tana maganganu kad'an kad'an wanda bayajin su,
Murmushi kawai yayi yashare ta yana kallon titi babu wanda ya sake magana harsuka iso unguwar su salma adaidai gidan sukai parking dan har number gidan ta gaya mai kallon ta yayi saikuma yakalli driver ta mirro dasauri yafuta waje,
Murya can k'asan makoshi yace "kishiga ki futo namaida ke gida akwai maganar da zamuyi mai muhimmanci dake"
Kanta taduk'ar tace "tom bazaka shiga ba?"
Kallon fuskar ta yayi yana sakin murmushin gefen baki yace "kibari saita haihu nanda nine months kinga lokacin kema kin kusan haihuwa saimu shiga tare ko"
Dasauri tab'alle murfun motar tafuta tana zare idanu wani soja ne yabita abaya yabud'e mata get tashiga gidan shiru kamar babu kowa da gudu ta'karisa tundaga compound take ta fad'in "Aunty Salma Aunty Salma kifito kitare ni kobakiyi missing d'ina ba?"
Ta'karisa maganar daidai tana shiga palourn wani irin komawa da baya tayi tana zazzaro many'an idanun ta tace "kai" saikuma tafashe da dariya Sulaiman ne yace "Sister shigo mana kika koma"
Hararan k'ofar tayi tace "uhm" tashiga this time babu Salma a palour sai Sulaiman d'in kad'ai zama tayi tagaishe shi ya amsa yanata tsokanan ta itakuma tana ta murmushin dole,
Salma ne tafuto sanye da k'aton hijab har k'asa tazauna cike da kunyar k'anwar nata suka gaisa sai tami'ke tace "bara natafi nakatse muku soyayyar ku sainan da two weeks zan sake zuwa"
Dariya Sulaiman yayi yace "A'ah futa zanyi koma kixauna" yafad'a yana mik'ewa,
Baki tad'an tab'e aranta tace gulma afili tace "A'ah tare da Yaya Hamza naxo yana jirana........✍🏼🔥🔥 *FITATTU* 🔥🔥
*CARBIN ƘWAI*
'''Mai wuyar janyuwa'''
&
*VALENTINE DAY*
'''Ranar masoya'''Dajin sunayen books d'in kasan zasu bada citta salon na daban ne da sauran pure Rimantic and Romance story dan haka ku hanxarta siya karku bari abaku labari y'ar uwa zaki k'aru da abubuwa masu matu'kar muhimmanci acikin litattafan nan biyu dan bana yarwa acikin su duk wacce tashirya zata tura kud'in ta ta 4210014214 Lawal Shamsiyya Eco bank shaidar biya ta 07017296839 normal
*VALENTINE DAY* paid 300 vip 500
*CARBIN ƘWAI*
normal paid 400
Vip 700
duka normal paid 500 vip 1000
Akwai special group inda zamu dinga posting biyu duk sati akan matsalolin ma'aurata tare da bonos d'in litafina guda d'aya 1,000 kacal amarya uwar gida kudaure kushiga special group domin ajine na musamman daza'a dinga program biyu masu matu'kar amfani agareki da mijin ki dakuma lafiyar ki dakuma shawarwari akan zaman takewar auren mu Allah yasa mudace!#Follow me wattpad Bintubaby
#Vote
#Comments
#Share it fisabilillah dan soyayyar ki da fiyayyen halitta just 2group

BINABASA MO ANG
WAYE SANADI!?√√ BOOK ONE
RomanceThe first time they fall in love they are too young to know what it all means, they are force a part by tragedy and enjoy. he goes to United kingdom and becomes a star journalist while she remain in Nigeria fighting poverty trying to survive. but de...