Directional

222 18 7
                                    

💠💠💠💠💠
©®2021.



                     *♡IN-LAWS¸.•💥*
       

Bʏ.
   *HAWWA MUH'D USMAN.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*WATTPAD LINK:-* https://www.wattpad.com/story/216211172?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=REAL-SMASHER&wp_originator=iDULEr4cbYBaNlbu1Jn%2Fk8DX2nZbRtRMTAcg2pxFMMfUGFk1z9aFc6%2Fd9W2e6A2RnIQZKGv9Ardrz4mEgzIHUGGWJPVZvHBymyNE3gmbgqze7v0Ckkh4LkBJdFvKDeF9
        
*FREE PAGE*

   '''Maa sha Allah laa ƙuwwata illa billah.. I'm back my people..'''

                               03-04

#Directional

*Flash back...*

         Ranar yau ya kasance rana mafi muhimmanci daga cikin ranakun rayuwata,kasancewar a yau muke saukar karatun Alqur'ani a makarantar islamiyyarmu (Umar bin kattab) wanda yake nan cikin unguwar sharaɗa,tare da ƴan uwana Mardiyya da Juwairiyya,shisa tun asubah a gidan babu wanda ya koma bacci ake ta aiki,ni kam sanda na zare jiki na gudu nayi kwanciyata saboda daren jiya bamu kwanta da wuri ba,na bar Aunty da su Yaa Waleed suna ta aiki,because Hjy Umma ba ta yarda ayi team work,ko da azumi haka nan kowa suke yin aikinsu,idan sallah ya yi ma Abba yayi mana layya tun daga waje ake raba nama kowa su ɗauki nasu su san yanda za suyi da shi,shisa duk irin abubuwan nan bama damuwa tunda akwai ƴan uwana,duk da maza ne su babu abunda basu iya ba na girki,wani lokacin kuma idan basa nan Aunty Fatima tana ɗan zuwa taya Aunty saboda ta mu ta zo ɗaya sosai,tun ina jaririya take sona har zuwa yanzu dana girma,mafi yawan lokaci ko unguwa za taje tana zuwa ta tambayi Aunty mu tafi tare,a dalilin yawan raɓarmu da take yi ita da Yaa Abbas yasa Hjy Umma take jin haushinsu,wani lokaci idan tana musu abu sai kayi tunanin ba ita ta haifesu ba. Shigowata ɗakin kenan babu jimawa na kai dubana kan madaidaicin wall clock dake maƙale a sama,here idanuna suka hango min ƙarfe 7:47am,cikin wani irin sauri da ban taɓa irinsa ba na shige bedroom,a saman mirror na ɗauki lotion,sanda ma zauna gefen bed a gaggauce na fara shafawa lallausar  fatar jikina,na shafa powder sai kajol dana sa a idona nayi lining zagayensa nasa light chapstick ban ɗauki wani lokaci mai tsayi ba na kammala,na miƙe na ɗauki atampha ɗaya,cikin sababbin kayan da Abba yayi mana na fara warwarewa,plain zani ne da babu adon komai a jikinsa sai free fitted mai V-neck da adon fulawoyi a jiki,ɗinkin simple babu wani tarkace a jikinsa,a hankali nake motsa bakina ina karanto addu'ar da Annabi (S.A.W) ya koyar damu yayin da muka zo sanya sababbin tufafi,ina gama sa riga kafin na  zuge zip na jiyo sallamar Umaimah,da sauri ta ƙarasa zugewa na ɗaura ɗankwalina,na ɗauki ƙaton hijab ɗina ash color dake kusa da kayan na saka na ɗaura niƙab ɗina na fesa turaruka masu sanyin daɗi,flat shoe ɗina ash colour nasa,ina gama shiryawa ban jira ƙarasowar Umaimah ba na fito daga cikin ɗakin na tarar da su a parlour suna gaisawa da su Yaa Umar da suke ƙarasa packaging kayan rabo,Yaa Mukhtar yana tsokanar Umaimah yana cewa "Allah yasa ba saukar dabino kuka yi ba,na tsakani da Allah ne,dan wannan makarantar ta ku ni ban yarda da saukar kun nan ba,duk shekara sai an yaye ɗalibai.." Umaimah tace "kai Yaa Mukhtar,ko kowa zai faɗi haka ai kai ka yi shiru ka rufa mana asiri" yace "in rufa muku asiri? Ai idan kinga na yi shiru tou interview na muku na tabbatar ba asaran kuɗi kuka sa su Abba ba" dariya nayi wanda ya bayyana jerarrun tooth ɗina,a hankali na tsuguna kaɗan cikin sanyayyar maganata ina janye niƙab ɗin daga fuskata nace "Aunty na gama shiryawa" Aunty ta ɗago fuskarta da sauri mai ɗauke da fara'a tana faɗin "yanzun nake shirin kiranki na ga har Umaimah ta shigo baki fito ba" sai naga ta yi shiru tana nuna da kallo saboda kyaun da taga only female child ɗin nata tayi,cike da farin ciki tana kallonmu duka mu biyun take furta "Maa sha Allah! Kunyi kyau sosai daughter,sai dai nace Allah ya bada sa'a,yasa karatun da aka yi yayi amfani duniya da lahira,yadda kuka sauke Alqur'ani,Allah yasa mu kasance cikin cetonsa ranar gobe ƙiyama.." Da ameen muka amsa,Aunty tana sakin murmushi take sake faɗin "Ubangiji yasa na tsoron Allah kuka yi" muka sake amsawa da "ameen" sanyayyan murmushi nayi da ya bayyanar da sihirtaccen kyaun da Allah yayi min,fararen idanuna na ƙifta cikin salon maganata mai kama da yanga na furta "Aunty baza kije gurin saukar ba?" Cikin wasa Aunty ta gyaɗa kai kamar ba'a son ranta ba tace "ku yi haƙuri Fadwah kinga har yanzu bamu kammala shirya kayan nan ba,idan na fita waye zai yi? Ban san lokacin da za'a gama taron saukar ba,dole na zauna kuma kinga ke da za ki taya ni bakya nan" na rausayar da kai cikin damuwa nace "shi kenan Aunty,bari mu tafi kada mu makara,kin ga 8:00 ɗin ya wuce kuma ance muje kafin lokacin" Aunty ta girgiza kai fuskarta cike da alhini tace "nima ba don kin koma baccin asarar nan naki ba ai kinga da yanzun mun jima da gamawa,ku wuce ku tafi kada ku sake makara,Allah ya tsare hanya ya bada sa'a" muka amsa Umaimah tana yi min dariya,hararta nayi tayi ƙwafa bata ce komai ba,za mu tafi Yaa Waleed yace "iyayen zumuɗi ku tsaya na muku hoto kafin ku tafi" sanda ya kashe mana pictures masu kyau da wayarsa then muka musu sallama muka tafi. Tafiyar mintuna ta kawo mu harabar makarantarmu,tun kafin mu ƙaraso bakin get sautin karatun Alqur'ani dake tashi a cikin surround sound ya sanar da mu tuni an kammala duk wasu shirye²,abunda ya rage a lokacin ba shi da yawa taron ya fara,kamar zan yi kuka na kalli Umaimah dake sanye da babban hijab kamar nawa da niƙab a fuskarta nace "ƙawata! Allah yasa malam Farouk baya bakin get" Umaimah tayi ajiyar zuciya tace "ameen ƙawata,ni kaina fargabar da nake yi kenan,idan kowa yayi shiru bai ce mana komai ba,shi kam sai yayi mana faɗan makarar da muka yi" a hankali nace "sanin hakan shi yasa nayi maganar nan,kalli yanda muke tafiya kamar wasu mahaukata sam babu nutsuwa.. Allah yasa ma da niƙab a fuskar mu" dariya Umaimah tayi dai² lokacin muna shiga get ɗin makarantar,nayi sanyayyar ajiyar zuciya ina lumshe idanuna ganin wanda muke magana a kansa ba ya gurin nace "Alhamdulillah! Ƙawata baya nan.." Ban gama faɗar abunda yake bakina ba na hangosa yana fitowa daga cikin office ɗin malamai,wani irin mugun faɗuwar da gabana yayi sai da ya janyo nayi tuntuɓe kaɗan ya rage ban kai ƙasa ba,Umaimah tayi saurin riƙoni tana faɗin "sannu ƙawata,baki ji ciwo ba?" Girgiza mata kai nayi cikin rawar murya mai cike da tsoro nace "ehh!" Umaimah tace "sannu!"  Amsawa nayi nace "thank u friend" duk abunda ya faru akan idon malaman dake zagaye a harabar makarantar,wannan dalilin yasa ko da muka ƙarasa babu wanda yayi mana faɗan mun makara,sai sannu da suka min while muna gaisar da Malaman,wani irin kallon da malamin yayi min yasa ƴaƴan cikina juyawa da sauri na sunkuyar da kai ina jan duk addu'ar da tazo bakina,cikin raɗa Umaimah tace "ƙawata ki daina kallonsa please kada kije ki faɗi mu shiga uku" kai na ɗan girgiza kaɗan nace "uhumn!" Daga haka ban sake kallonsa ba muka wuce ajin da aka tanada saboda dalibai irin mu da suke sauku  a karo na 17.  Tun da muka ratso za mu wuce ake kallonmu,even though akwai niƙab a fuskokinmu daga ni har Umaimah but waɗanda suka sanmu basu kasa gane mu ba,muna shiga cikin class ɗin da ƴan sauka suke ƙawayenmu suka saka ihun murna,a tare muka cire niƙabs ɗinmu,it was there muka fara ɗaukan pictures da ƴan class ɗinmu,banda Juwairiyya da Mardiyya da suka ware can gefe suna taɓe baki da jan tsaki saboda kishin yadda kowa yake son raɓar inda nake,su kam baƙin hali ma bai barsu sun shiga ba,ni kam da komai ya faru akan idona na daure ina sakin murmushi cikin sanyina,Umaimah ce ta ƙarasa kusa da su tace "Mardiyyah! Ku zo ayi mana hoto" da sauri Juwairiyya tace "no! Mun gode" sanda ta taɓe baki ta juyo muka haɗa ido nayi dariya,tana ƙarasowa inda nake ta kalleni tace "nima dai da shishshigi irin nawa na kama na kai kaina.. Ai ga shi nan sun gwasale ni" dariya muka sa duka ƙawayenmu,sanda nayi ƙasa da muryata nace "ai na san haka zai faru shisa ban ce musu suzo ayi mana ba" Umaimah tace "ni kuma gani nayi sun koma gefe sun raɓe shisa nace suzo muyi shi ne za su watsa min ƙasa a ido,ai gaba ta fi baya tsayi.." Dariya na dunga yi mata,lokacin wani Mlm Luqman ya leƙo cikin ajin yace "ku fito haka idan kun gama selfie'n" yana tafiya muka jero muka fito muna tafiya almost mu 35 ne mata sai maza 28,Umaimah tace "wai a ina za mu zauna ne?" Nace "tsakiya,kin san ba na son kallo" Umaimah tayi murmushi tace "ke dai kamar ƴar shaye² da an fara kallonki sai ki haɗe rai kina ƙananun maganganu" nace "tou me za'a kalla,halittar tawa daban take ne da za'a na kallon mutum ace bazai magana ba?" Dariya tayi tace "haba ƙawata ko ni da ban kaiki kyauba ake kallona bare ke? Kin ga yanda Allah ya halicce ki kuwa? Kin taɓa tsayawa kin kalli kanki?" Harararta nayi nace "dan Allah mu bar maganar kada ki ɓata min rai" tace "ke dai ba kya son gaskiya" nace "ehhh ba na so ɗin" saman manyan tarbaman da aka shimfiɗa muka zazzauna,gefe ɗaya manyan rumfuna ne da kujeru na alfarma wanda aka ajiye saboda manyan baƙi,sai wanda aka tanada saboda iyaye da ƴan uwanmu da za su halarci taron,not too long Mai martaba sarki ya ƙaraso da tawagarsa,here taron ya fara. Lokacin da ake kiran ɗalibai da za su buɗe taron da karatun Alqur'ani,sanda mutum biyu suka yi maza,ban yi zato ba na jiyo ana kiran suna na *FADWAH ZAKARIYYA WAKILI*,sanda gabana yayi mugun faɗuwa na hau rarraba idanunsa,Umaimah tace "hurry up friend" a hankali na tashi idona har wani rawa suke,na ƙarasa na amsa loud speaker,cikin sanyi na lumshe idanuna ina sauke ajiyar zuciya wanda ya bayyana cikin speaker ɗin hannuna,lokaci ɗaya gurin ya ɗauki shiru kamar wanda nayi commanding occupants ɗin gurin (wasalul isti'azhati wal-basmala) nayi then na fara rero *SURATUN-NISA'I* cikin zazzaƙar muryata mai cike da sanyi,zallar ƙira'ar hafs nake kwararowa,tajweed ɗina yana fita,ni nake karatun amma ina bitar abunda nake faɗa a raina,sanda nazo kan aya ta 3 da yake magana akan marayu da matan da aka ƙayyadewa mutum ya aura,inda Allah (S.W.T) yake cewa (kuma idan kun ji tsoron ba za ku yi aadalci ba a cikin marayu,to (akwai yadda za'a yi) ku auri abun da yayi muku daɗi daga mata;biyu-biyu,da uku-uku,da huɗu-huɗu.. Sannan idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba,to (ku auri) guda ko kuwa abun da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba.. Kuma ku bawa mata sadakokinsu da sauƙin bayarwa. Sannan idan suka yafe muku wani abu daga gare shi,da daɗin rai,to ku ci shi da jin daɗi da sauƙin haɗiya.. Kada ku bai wa wawaye dukiyarku,wadda Allah ya sanya ta a gare ku,kuna masu tsayuwa (ga gyaranta). Kuma ku ciyar da su a cikinta kuma ku tufatar da su,kuma ku gaya musu magana sananniya ta alheri.. Kuma ku jarraba marayu,har a lokacin da suka isa aure. To,idan kun lura da shiriya daga gare su,to ku miƙa musu dukiyoyinsu. Kada ku ci ta da ɓarna,kuma da gaggawa kafin su girma. Kuma wanda yake wadatacce,to ya kama kansa,kuma wanda yake faƙiri,to ya ci,gwargwadon yadda ya kamata. To,idan kun miƙa musu dukiyoyinsu,sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah ya isa ya zama mai bincike..) Sanda na kai aya ta 23 wanda yake magana akan waɗanda aka haramtawa mutum ya aura,ji nayi gurin ya sake yin wani irin shirun da tamkar ni kaɗai nake existing a gurin,a haka sanda na kai ƙarshe sannan nace "sadaƙallahul aziim.." Kabbara gaba ɗaya gurin ya ɗauka,a hankali² na fara buɗe idanuna da suke lumshe tun farkon da na fara karatun,na miƙawa presenter abun maganar,a nutse idanuna a ƙasa na koma na zauna kusa da Umaimah ina sauke numfashi nace "Maa sha Allahu laa ƙuwwata illa billah.." Umaimah ta kalleni fuskarta da murmushi tace "bravo ukutiiy.. Kin yi ƙorari sosai,almost 30+ verses kika karanta mana" murmushi kawai nayi sai dai ban ce komai ba,sanda mutum biyu suka sake yin karatu kafin aka fara gabatar da taron,bayan an raba mana alluna,anyi darasu,Mai martaba yayi jawabi tare da wasu manya daga ubannin makaranta da suka yi sharhi akan karatun da muka gabatar then aka raba mana kyaututtuka,lokacin da taron yazo ƙarshe bayan an yi mana hotuna da malaman mu,sauran ƴan sauka kowa ya wuce gurin family'nsa suna ɗaukan pictures,a hankali kamar zan yi kuka nace "Umaimah zo mu tafi gida" dariya Umaimah tayi tace "me yasa za mu tafi?" Nace "tunda basu zo ba me za mu tsaya yi a nan?" Tace "wa yace miki basu zo ba?" Ƙwalla tana taruwa idona nace "ai Aunty ta ce baza su zo ba" tace "kou?" Tsayawa nayi ina kallonta ba tare da na ce komai ba,ta ƙyalƙyale da dariya tace "turn around ki kalli wanda suke bayanki" jikina a sanyaye na waiga,yayyuna na gani su uku sun sha ankon shadda golden brown sai ƙyalli take,komai nasu iri ɗaya hatta karin hula,sanda nake kallonsu suna nufo mu suna min murmushi,ban san sanda hawaye suka fara sauka fuskata ba,Yaa Waleed yana girgiza min kai alamar kada nayi,Yaa Umar yayi tsaki yana hararata yace "ke dai kina da matsala wallahi,mene ne abun kuka kuma?" Yaa Mukhtar yayi murmushi yace "haba brother kaima dai kamar baka santa ba,me neman kuka ne fa aka jefesa da kashin awaki.. Kaga ai sai yaita yi ba mai cewa ina dalili?" Ɗaure fuska Yaa Waleed yayi yace "dan Allah ki yima mutane shiru ko yanzu mu koma inda muka fito" da sauri na riƙe masa riga ina bubbuga ƙafafuwana cike da shagwaɓa nace "ni dai Allah² baza ku tafi ba" dariya suka yi,Yaa Umar yana bubbuga ƙafarsa shima ya kwaikwayi maganata,gaba ɗaya muka sa dariya,ya harare ni yace "shagwaɓaɓɓiyar Aunty kawai.." Fuskata na ɓoye jikin Yaa Waleed ina dariya,da sauri yana zaro idanunsa yace "Waleed za ta goge maka kajol ɗin idonta a jikinka" da sauri Yaa Waleed yace "ke! Sake ni kada ki cukuikuye min kaya ki ɓata min kwalliya,idan zan yi budurwa kisa tace ba ta so na" ɓata fuska nayi nace "ni ɗin?" Yace "ke ɗin fa" nace "ni fa taka ce,kai nawa ne" murmushi yayi ya janyoni yace "kuma fa haka ne,zo a fara mana photon tarihi" here camera man da suka zo tare ya fara haska mu,muka shiga tsakiyar su ni da Umaimah,Yaa Waleed yace "su Aunty fa suna gurin nan" da sauri nace yaushe suka zo?" Yace "tun lokacin da kike karatu muka zo tare da su" ina buɗa idanuwa nace "really?" Yace "yeah!" Cikin zumuɗi nace "dan Allah muje gurinsu" Yaa Umar ya kalleni yace "dan Allah kalleta sai wani ɓarin jiki take" yana kwaikwayo na yace "dan Allah muje gurinsu" hannun Yaa Waleed na riƙe firmly ina turo baki nace "mu tafi Yaya" yace "okay!" Bamu tsaya jiransu ba muka wuce suka biyomu a baya,sanda muka ƙarasa gurin da su Aunty suke,muna gaisawa wani yaro yazo gurin yana kallon Yaa Waleed yace "wai wancan mutumin ya ce kaje" a tare muka juya muna kallon direction ɗin da yake pointing...

     *This book is not for free,it's #200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added in the paid group. Ƴan Niger za ba ku number da za ku tuntuɓa.*


#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

IN-LAWSWhere stories live. Discover now