Throw back

194 24 11
                                    

💠💠💠💠💠
©®2021.


                     *♡IN-LAWS¸.•💥*
       

Bʏ.
   *HAWWA MUH'D USMAN.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*WATTPAD LINK:-* https://www.wattpad.com/story/216211172?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=REAL-SMASHER&wp_originator=iDULEr4cbYBaNlbu1Jn%2Fk8DX2nZbRtRMTAcg2pxFMMfUGFk1z9aFc6%2Fd9W2e6A2RnIQZKGv9Ardrz4mEgzIHUGGWJPVZvHBymyNE3gmbgqze7v0Ckkh4LkBJdFvKDeF9

         🎊🎁 *MY AREEF IS 1*🎈🎉
   
      '''Happy Birthday to the coolest kid in town,u rock! Hope it's a really special day for ya..''' 🎂🥂

 
                               02

#Throw back

         Saurin dafa bed nayi wasu irin hawaye suna zubowa idanuwana da ƙarfi na furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Allahumma ajirnii fii musibatii wa'aklufnii khaiiran minha.." Hawaye sai zubowa suke uncontrollable,sanda nayi mai isata nayi shiru sai ajiyar zuciya nake saukewa,Mardiyya ta shigo babu ko sallama tana daga tsaye tace "wai kizo Abba yana kiranki" sanin da Aunty take yasa ban ɗaga kai na kalleta ba,Aunty ta shi ta nufi ƙofa za ta fita sai kuma ta juyo a hankali tace "ki tashi kiyi wanka,yanzu baƙi za su fara zuwa" a hankali na gyaɗa kaina zuciyata cike da rauni,bayan fitar Aunty daga ɗakin na tashi,na shiga bathroom na kunna heater,then na fito na cire kayana nasa ƙaramin hijab saboda ban sani ba ko wani zai shigo,sanda na shiga toilet ɗinmu dake nan cikin ɗaki,a gaggauce na fara wanke banɗakin na kunna tap,sai da yayi min dai² yanda nake so sannan na kashe na kulle ƙofar na cire kayana,ban wani jima ba sosai na fito,ina cikin shiryawa Aunty ta shigo ɗauke da Baby'n gurin Aunty Fatima tana share hawaye ta zauna saman gado tayi shiru sai kallon yarinyar take sympathetically,a hankali na ƙarasa saka rigata,ban ɗaura ɗankwali ba na ƙaraso kusa da ita na zauna ina leƙen fuskar Baby'n dake ta bacci abunta,tausayinta da ƙaunarta yasa hawaye suka cika min idanu,na jinginar da kaina jikin shoulder Aunty ina kallon Baby'n muna hawaye tare,can muna ta zaune Abba yayi sallama,ganin babu kowa parlour ya shigo,da sauri Aunty ta share fuskarta ta amsa,dattijon mai kimanin 75yrs kyakkyawan bafulatani dogo ya ƙaraso,da kallo ya bimu sanda ya zauna yana kallon Aunty dake haɗiye kukanta yace "me kenan haka Asiya? Kin sa ƴarki da jikarki gaba kina kuka" fashewa da kuka Aunty ta sake yi mara sauti,Abba ya zuba mana idanu kawai yana kallonmu,can da yaga ba mu da niyyar yin shiru yace "tou ki bawa Fadwah yarinyar ki taso,Abbas ya ce suna hanya sun taho da gawar yanzu" gabana ne ya sake faɗuwa na juya ina kallon Abbanmu kamar zan yi magana,underneath nake tambayar kaina "da gaske yanzu Aunty Fatima ta rasu kenan?" Abba ya tashi ya nufi ƙofa ya fita,almost 5 minutes sannan Aunty ta tashi muryarta har ya dishe ta miƙo min Baby'n tace "ki goyata Fadwah kuje gidan su Umaimah,idan ta tashi kuma akwai madararta yana nan a parlour na bar kayan,ki dama mata sai ki bata" na gyaɗa kai a hankali saboda na san yanda ake yi a gurin wata maƙociyar Aunty Fatima duk na koya lokacin da ta haihu babu ruwan nono ake bawa jaririn madara,Aunty tana fita na ɗauki Baby'n na goyata na rufeta da ƙaton towel ɗinta nasa hijab ɗina har ƙasa,da sauri na fita parlour zan ɗauko kayan da Aunty tace,ƙaton leda da luggage trolley na gani,sanda na kaisu ɗaki na buɗe na ɗauko kayanta da Pampers,na ɗauki feeder na zuba madara a ciki na rufe na ɗauki kayan na fita,ƙofar parlon mu naja na rufe sannan na nufi get,sanda na fara leƙawa naga babu kowa a ƙofar gidan da sauri na ƙarasa fita,gidan da yake jikin namu daga right hand side na nufa,dai² ƙofar shiga muka kusa karo da Maman su Umaimah,nayi saurin matsawa baya nace "kiyi haƙuri Mama ban san kin taho ba" sai naga ta tsaya cikin soron gidan idanunta sun kaɗa sun yi jaa tace "babu komai,shigo Fadwah" na ƙarasa shiga idanuwana suna ciccikowa da ƙwalla,na ɗan sunkuya nace "ina kwana?" Ta amsa "lafiya lao,ya ƙarin haƙurinmu?" Kasa amsawa nayi sai hawayen da nake sharewa,tana girgiza kai tace "haƙuri za muyi,Ubangijin da ya halicci Fatima ya fimu sonta shisa ya karɓe abarsa,Allah yasa can ta fiye mata nan" na dunga gyaɗa kai ina cewa "ameen" tace "bari naje gidan naku zan shiga dama,Aunty ta aiko an sanar min" da ƙyar na haɗiye kukana nace "toh a dawo lafiya" har za ta fita ta waigo tace "me kika goya? Ko jaririyar ce a bayanki?" Na gyaɗa kai nace "ehhh itace" tace "Allah sarki mu ganta" da kanta ta ɗaga hijab ɗina da towel da na rufeta da shi,Mama ta leƙa fuskarta tace "maa sha Allah! Allah rayaki,ya yiwa rayuwarki albarka" na amsa "ameen" sannan Mama ta rufeta tace "shiga ciki Umaimah tana nan kuyi zamanku can hayaniya zai iya sawa ta tashi" nace "toh Mama" daga haka ta fita ni kuma na ƙarasa shiga cikin gidan nayi sallama a ɗan madaidaicin tsakar gidan,Umaimah ta leƙo daga kitchen ɗinsu tace "bari na fito ƙawata ki shiga parlor ina zuwa" ban yi magana ba na shiga,parlon babba ne babu laifi,saman armchair na zauna irin masu buttons ɗin nan manya maroon colour ina sauke ajiyar zuciya,Umaimah ta shigo da tray a hannunta ta ajiye ƙasa kan rug tace "sannu ƙawata!" Na gyaɗa mata kai kaɗai ina lumshe idanuwana da nake jin kamar an cika min su da ƙasa,tace "ya ƙarin haƙurinmu?" Ina jan ajiyar zuciya nace "alhamdulillah!" Tace "Allah ya mata rahama,ya raya abunda ta bari" nace "ameen yaa arhamar-rahimiiyn" muka yi shiru kowa da tunanin da yake,na sauke hijab ɗina na kwanto Baby'n dake bacci daga bayana,da sauri Umaimah ta matso kusa da mu tana leƙen fuskarta tace "Allah sarki! Allah raya mana ke Baby,ya jiƙan mahaifiyarki yayi mata rahama" na amsa da "ameen.." Umaimah ta kalleni tace "sauko muyi breakfast ƙawata na san baki ci komai ba yanzu kam" ban yi mata musu ba saboda tun jiya a hospital da muka ci tare da su Ihsan,here na samu na ɗan ci dankalin na sha tea,bamu jima da gamawa ba muka fara jiyo hayaniya da yake akwai irin small window na can saman ɗaki a nan parlon wanda ya fita waje kuma a buɗe yake,Umaimah ta kalleni tace "ina jin an kawo gawar kou?" Na gyaɗa mata kai,ina rungume da Baby'n ni dai na kasa tashi daga gurin har Baby'n ta farka,Umaimah ta haɗa mata madarar ta bata,sanda ta koma bacci ta goyata,sai da aka gama shirya Aunty Fatima sannan aka aiko kirana,muka fita tare da Umaimah ina duƙunƙune da Baby'n,cike muka samu ƙofar gidanmu da maza,a haka muka samu hanya kawunanmu a ƙasa muka shiga,nan muka tarar da gidan a cike da ɓaki ƴan uwanmu,family'n Abbanmu da na Hjy Umma na kusa²,sai family'n su Yaa Shaheed,Mamarsa da ƙannensa duka,nan muka tarar da su a parlorn mu,muka ƙarasa ciki a hankali muka gaisar da Hjy Maimuna mahaifiyar Yaa Shaheed ta mana gaisuwa,muka gaisa da su Ihsan,Hjy Maimuna ta karɓi Baby'n tana kallon ta sympathetically,nan muka fita zuwa parlon Abbanmu da yake a can aka shiryata,ina shiga na tarar da Aunty da su Mardiyya a zazzaune sun saka gawar Aunty Fatima a gaba suna sharɓan hawaye,a sanyaye na ƙarasa shiga na zauna kusa da Aunty ina kallon makaran da aka kwantar da ita hawaye suka kawo idanuna,a haka na mata addu'ah hawaye sun ƙi tsayawa fuskata,ina gamawa na tashi zan fita Hjy Umma tace "ina jariyayar take?" Na juya ina kallonta nace "tana gurin Mamar Yaa Shaheed" tace "karɓota suyi bankwana da uwarta" na amsa na fita,not too long na dawo ɗauke da ita,Hjy Umma ta karɓeta ta matsa kusa da gawar Aunty Fatima ta ɗorata a jikinta,mu dai duk mun tsaya kallon ikon Allah,sai ga Abba da Yaa Shaheed da su Yaa Safwan,babban Yayanmu Yaa Abbas,da yayyena da muke uwa ɗaya maza har uku sun shigo,Yaa Umar shi ne babban ɗan Aunty sai Yaa Mukhtar,sai Yaa Waleed sai ni Auta,su Yaa Abbas ma su biyar ne gurin Hjy Umma,shi ne Babba sai Aunty Fatima,sai Aunty Salma da ta rasu,sai Juwairiyya da Mardiyya,banda wanda ta haifa suka mutu kafin Yaa Abbas,bayan an mata addu'o'i sannan su Yaa Abbas suka fita da gawar,a babban filin ƙofar gidanmu aka mata sallah,daga cikin gida muna jiyo kabbarorin al'ummar annabi da suka halarci jana'izar,sannan aka shiga motoci aka tafi rakata makwancinta,kafin a dawo daga kaita muka fito za mu koma gidansu Umaimah tare da Ihsan,nan muka tarar an fara sauke manyan runfuna ana kafawa. Ranar har dare muna gidan sai idan Baby'n ta farka ko ta yi kuka a dama mata madara a bata,cikin yinin gaba ɗaya jikin kowa a sanyaye yake,sai dare sannan su Ihsan suka tafi,nima na koma gida,kwana uku akayi ana zaman makoki,gaba ɗaya tunda akayi mutuwar,sau ɗaya naga Yaa Shaheed har nayi masa gaisuwa,daga nan kuwa ban sake ganinsa ba,bayan addu'ar uku baƙi suka fara tafiya ya rage sai mu ƴan gida,sai kuma ƴan gidan su Yaa Shaheed da kullum sai sun zo,kasancewar a nan ake zaman makokin,here nake samun labarin ko kaɗan Yaa Shaheed bai yi kuka ba da akayi mutuwar,sannan an mayarwa Baby'n sunan Aunty Fatima amma za ana kiranta (DINA). Ranar ana kwana shida da mutuwar Aunty Fatima da dare Abba ya tattara mu dukanmu ƴaƴnsa a parlonsa,bayan addu'o'in da yasa Yaa Abbas yayi then yayi gyaran murya yana kallonmu ya fara magana kamar haka "ba wani abu yasa na tattara ku a nan ba,face ina son sanar da ku,in Allah ya kaimu gobe akayi addu'ar bakwai za'a ɗaura auren Fadwah da Shaheed" wani mugun faɗuwa gabana yayi a rikice na ɗago jikina banda ɓari babu abunda yake,hawaye kuwa ban san ko liter nawa ne suka makala ba,kafin kowa yayi magana hamshaƙiya mandiya Hjy Umma ta yi saurin cewa "Fadwah kuma Alh?" Abba ya gyaɗa kai yace "in sha Allah!" "Tabɗijan.." Was the first word da ya fara escaping daga bakin Hjy Umma,hakan yasa dukanmu kallonta with suspicion,sai dai babu wanda yace mata ci kanki,Abba ya kalleta yace "Ummuhani'in! Ko kina da matsala da wannan haɗin ne?" Ranta a ɓace tace "haba Alh yanzu tsakani da Allah dan Fatima ta rasu sai a rasa wanda za'a bawa mijinta idan musanye za'a masa sai ace Fadwah,ina laifin ma a basa Juwairiyya.." Ɗaga kai kawai Aunty tayi tana kallonta bata ce komai ba,Yaa Abbas yace "haba Umma! Yanzu Fadwah da Juwairiyya ba ɗaya bane,dan ba'a bashi Juwairiyya ba an bashi Fadwah hakan ai ba wani matsala bane" tsawa Hjy Umma ta yiwa Yaa Abbas tace "kai dallah tafi can jakin banza sallamamme,idan ana magana da mutane ka daina sa baki saboda kai dama can ba amfanine da kai ba,mutumin da ya fifita wata matar akan uwar da ta kawosa duniya,ina dama za'a sa masa ran zai yi wani abun arziki.." A hankali Yaa Abbas ya sunkuyar da kansa ƙasa yace "Allah ya baki haƙuri.." A fusace tace "ameen.. nace Ameen" kaf ɗinmu idan aka cire Hjy Umma,Juwairiyya da Mardiyya babu wanda Yaa Abbas bai bawa tausayi ba,Abba ya girgiza kai yana kallon Hjy Umma yace "kin gama?" Tace "tou Alh ai maganar Allah fa kenan,kuma idan gaskiya za'a bi kaima da kanka ai ya kamata ace ka duba ka ga abunda ya dace,ta ina yayye basu yi aure ba za'a ɗauko ƴar ƙaramar ciki ace za'a mata aure,ai salon ta raina ƴan uwanta ne wannan" Abba dai kallonta kawai yake yace "kin gama nace? Ni ban tambayeki wani dogon labari ba?" Ta gyaɗa masa kai,ya gyaɗa kai shima yana kallonmu yace "i repeat myself in Allah ya kaimu gobe ɗaurin auren Shaheed da Fadwah bayan addu'ar bakwai,ku tashi kuje na sallame ku.." A kaikaice Hjy Umma ke kallon Abba tace "wallahi bazai yiwu ba Alh,ta ina za'ayi haka?" Abba ya kalleta yana gyaɗa kai yace "kiyi duk abinda za kiyi,idan kin isa sai ki hana Allah ikonsa" cikin masifa tace "tabbas kuwa zan nuna maka na isa.. Za mu gani" yace "muga alkhairi.." Sanda ya juyo yana kallonmu yaga babu wanda ya motsa daga gurin a fusace yace "nace kuje na sallameku me kuke jira kuma?" Aunty ta sauke wani ajiyar zuciya tace "ina da magana Alh" Abba yayi mata wani kallo yace "ina jinki" a hankali Aunty tace "dan Allah Alh idan har al'amarin nan zai kawo wani fitina,ka taimaka kayi haƙuri ka janye maganar nan daga kan Fadwah,a mayar da shi kan Juwairiyya,a ganina ita tafi dacewa ta maye gurbin ƴar uwarta.." Da sauri Abba yace "dakata min Asiya.." Da sauri Aunty tace "dan Allah Alh ka duba masalaha.." Abba yace "wane masalaha kuma zan duba bayan wanda na duba? Ko so kuke na tauye zuciyar ɗan mutane? Shin kin manta wancan lokacin? Ko kina sane da abunda ya faru shekara ɗaya baya?" Aunty ta gyaɗa kai tace "na sani Alh" yace "kin sani kike min wannan maganar Asiya?" Aunty tayi shiru bata ce komai ba,Abba yace "matuƙar kuka ga na canja maganar nan sai dai idan ɗaya cikin  Shaheed ko Fadwah wani ya rasu kafin gobe" daga haka bai sake cewa komai ba,a fusace Hjy Umma dake zaune ta miƙe tana kallon Abba tace "ai kai dama tun tuni aka shanyeka shisa kake ɗabi'u irin haka,kafiyar bala'i da taurin kai dai babu inda suke kai mutum sai mahallaka.." Abba yayi murmushi yace "Allah ya kyauta" angrily Hjy Umma tace "ya kyauta abunda yafi haka" daga haka ta nufi hanyar fita ta bar parlon,Yaa Abbas ya kalli Abba a hankali yace "kayi haƙuri Abba" Abba ya gyaɗa masa kai yace "jeka babu komai" Yaa Umar sarkin zuciya shi ya fara tashi ya fita sai Yaa Mukhtar,lokacin na fito ina share hawaye Juwairiyya da Mardiyya suka fito suka kalleni sukayi tsaki,ban kulasu ba na wuce ɗakinmu,ina shiga Yaa Umar ya juyo yace "ke kukan me kike?" Jikina yana ɓari nace "I'm scared Yaa Umar.. Dan Allah ka bawa Abba haƙuri,ya janye maganar nan,Hjy Umma da su Juwairiyya za su.." Wani kallo ya min yace "idan kika ƙarasa sai kin ci uwarki,ɓace kada ki ɓata min rai na ɓallaki" da gudu nayi hanyar ɗakinmu ina fashewa da kuka,Yaa Waleed ya shigo dai² lokacin,bai cewa Yaa Umar komai ba ya biyo bayana cikin ɗaki,a kwance ya tarar da ni ina kuka,ya ƙaraso a hankali ya zauna yace "Fadwah! Tashi muyi magana" da sauri na tashi ina share fuskata nace "Yaa Waleed dan Allah muje ka bawa Abba haƙuri,ka faɗa masa ba na son aurensa.." Kallona ya tsaya yi sai da na gama yace "do u know what?" Nayi saurin girgiza masa kai,yace "i just want u to calm urself down,kinsan tunda Abba yayi maganar nan babu fashi ko?" Ban ce komai ba sai hawayen da nake sharewa,da yaga na ƙi yin shiru yace "it's ok! Tunda baki yarda ba,yanzu ki yi alwala kiyi istirakara,idan kika ga abun nan ya tabbata ba'a fasa ba,ubangiji kawai ya san abunda ya ɓoye" shawarwari sosai ya bani,sanda yaga hankalina ya kwanta kafin ya fita ya barni,Yaa Umar kuwa har lokacin yana tsaye parlour yana zarya jira kawai yake Aunty ta shigo,after few minutes Aunty ta shigo da sallama,ko amsawa bai ba ya nufeta da sauri yace "Aunty! Yanzu fisabilillhi haka za'a sakawa matar nan ido ai ta tafiya a haka a gidan nan,Abba yana kallon abunda take amma bazai ɗauki mataki ba? Wannan adalci ne?" Ɗaga masa hannu tayi tace "ka ga ba na son shirme,idan baza ka iya zubawa wutar dake son kunnuwa ruwa ka kashe ba,kada ka ƙara masa petrol a ciki.. Ni ba na son fitina,kada ka janyo abunda zai haɗoni da mahaifinku.." Yace "amma Aunty" sake ɗaga masa hannu tayi da sauri tace "i said count me out.. Idan za kayi shirmenka kada ka ƙara sako ni a ciki,maza kaga hanya nan,fita ka ba ni guri kada ka janyo min wani masifar.." A zuciye ya juya ya fita yana cewa "duk haƙurin kin nan ne ya janyo muke fuskantar matsaloli a gidan nan,da kin bari tuni na yi maganar matar nan wallahi.." Aunty ta bisa da kallo baki sake,sanda ya fita tace "anya yaron nan kansa ɗaya ba shaye² ya fara ba kuwa?" Kamar yanda Yaa Waleed yace min nayi bayan fitarsa na tashi na shiga bathroom nayi wanka na ɗauro alwala,sanda na fito na shimfiɗa pray mat,bayan na shirya na saka kayan baccina riga da wando,na kabbarta sallah,raka'a biyu nayi nayi addu'o'i,sanda na idar na tashi na cire hijab na haura saman gado na kwanta,haka nan jikina yayi sanyi,a hankali na lumshe idanuna,tunanin al'amarin da ya faru 1 year ago ya dawo min fresh a cikin ƙwaƙwalwata kaman yanzu yake faruwa...

*Flash back...*

   '''#Ranakun posting every Saturday & Sunday.'''

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

IN-LAWSTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang