Possibility

122 16 5
                                    

💠💠💠💠💠
©®2021.


                     *♡IN-LAWS¸.•💥*
       

Bʏ.
   *HAWWA MUH'D USMAN.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*TELEGRAM:* https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA
      
*FREE PAGE*

                               09-10

#Possibility

       Gently ya ɗago kansa yana kallona da idanuwansa da ya ƙanƙance yace "kin hora ni kuma na horu My Jewel" nace "what have i done to u?" Kallona yake yace "are u really asking me?" Na gyaɗa masa kai nace "ehh!" Yace "uhmn! Yarinyar nan kin mayar da ni abun wasan ki" ɗauke kai nayi ina dariya ƙasa² nace "ni ban wani rainaka ba" yace "ai shi yasa naga har dariya kika samu damar yi" da sauri na ƙunshe bakina nace "ehyahh! Bafa ka gani da kyau ba" ya harare ni kaɗan yace "kiyi son ranki,soon zan yi maganin ki" nace "Allah ya nuna mana" yace "ameen.. Kin gane abunda nake nufi?" Nace "a'a na kusa" yace "i mean if we get married" shyly na sunkuyar da kaina ina fidgeting fingers,yana kallona yayi wani murmushi,kafin na gaishesa nace "ina yini?" Yace "lafiya lau! Ya kike?" Nace "alhmdllh,ya aiki da mutanen gida?" Yace "duk suna lafiya,suna gaisheki.. Ya Aunty da su Yaa Farouk?" Nace "suna nan lafiya" yace "how about ur exams?" Sanda na sauke wani numfashi nace "alhmdllh!" Yace "maa sha Allah! May him makes u get better results with a flying colors" ina murmushi na amsa da "ameen.." Muka yi shiru,can ya fara breaking silence ɗin yace "Abba fa? I mean yana nan?" Na gyaɗa kai nace "ehh! Ai idan akayi sallah gida yake dawowa" yace "okay! Ina son magana da shi dama,so ina tunanin ko baya nan" nayi ɗan murmushi a hankali na ɗago kaina muka haɗa ido,sanda na kalli cup ɗin da na zuba masa lemon naga bai sha ba,na kalleshi a shagwaɓe nace "tou ka sha mana" yayi wani murnushi,then ya ɗauki cup ɗin ya kai bakinsa,sanda ya sha ya ajiye cup ɗin yace "thanks my Jewel.." Hira sosai muka yi,duk yana kula da time,to 9:15pm yace "i'm going my Jewel" nayi shiru ban ce masa komai ba,ya kalleni da kyau yace "ko ba kya so ne?" Fuskata ɗaure na gyaɗa masa kai kamar zan yi kuka,yayi murmushi mai sauti yace "ohh no! Kwana nawa suka rage mu fara rayuwa tare?" Da sauri na ɗaga idanuwana na kalleshi,ya gyaɗa min kai cike da tabbatar da maganarsa yace "yanzu haka maganar ki ya je wajen Daddy,so ina son yiwa Abba magana na shawarcesa akan lokacin da ya kamata na turo magabata na.. Kafin wani shaiɗanin ya zo ya maki khuɗuba ki daina so na" dariya na fara nace "anya kuwa?" Yace "sosai ma! Lokacin da za'ayi Shaheed bazai sani ba,sai daga baya yaji an masa sakiyar da babu ruwa" na ɗago kaɗan na kalleshi ina lumshe idanuwa nace "kasa a ranka in dai wannan Fadwan ce babu wanda ya isa rabaka da ita,sai dai idan Allah ya hukunta wani al'amari daban akanmu" saurin girgiza min kai yayi yace "babu ma abunda zai faru,kada ki mana baki" nayi murmushi nace "kace in sha Allah" yace "if Allah wills! Ba ki da miji sai ni" nace "Allah ya amsa" ya amsa da "ameen.." Da zai tafi lokacin yace "yau banga friend ba,na kira wayarsa a kashe" nace "Yaa Waleed wai?" Yace "da wa kike tunanin zan tambaya?" Nayi murmushi nace "ayyah! Yaa Waleed yana hostel,sun fara exam ne,shisa baza ka same shi ba" yace "me yasa?" Nace "ai haka yake yi,idan zai karatu sai ya kashe wayar saboda kada a kirashi,amma nan da 10pm zai iya buɗe wayar" ya gyaɗa min kai yace "okay! I understand.. Tashi muje ki rakani" na ɗago ina kallonsa naga shima ni yake kallo,a hankali nace "yau kuma sai na maka rakiya?" Yace "yeah!" A hankali nace "ni dai kayi tafiyarka babu wani rakakan da zan yi" yace "da gaske?" Nace "ehh!" Yace "zan kama hannunki kuma dole ki raka ni" nace "idan naƙi fa?" Yana min wani kallo yace "ban san mene ne zan iya yi ba" ɗaga girori na nayi nace "da gaske?" Murmushi yayi yace "taso please kada dare yayi min" maƙe kafaɗa nayi nace "ni dai bazan je ba" yace "please mana" na sake maƙe kafaɗa,slowly ya miƙe ya ɗauki car keys ɗinsa da wayoyinsa yace "okay! Thanks" daga haka ya juya zai tafi,yanda naga yanayinsa yasa jikina a sanyaya nace "wait please!" Bai juyo ba yace "no! Yi zamanki na gode" nace "ka bari na raka ka" tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba yace "na ga ba kya son zuwa" nace "a'a ba haka bane" juyowa yayi yana min wani kallo,sanda yayi folding hannuwansa yace "uhmn!" Yana ɗage girorinsa,slowly na tashi nace "da wasa fa nake maka" yace "really?" Da wani murya,na gyaɗa masa kai,ya lumshe idanuwa ya buɗe,a hankali yace "any ways! Zo muje ki raka ni" walking slowly na ƙaraso inda yake,ganin ya tsaya a ɗan shagwaɓe nace "let's go" na yi gaba kenan zan wucesa naji an fizgoni,da sauri na buɗe baki zan ƙwalla ƙara,yayi sauri ya rufe min baki da nasa,wani irin kiss ɗin da yake min passionately,gaba ɗaya nayi suman tsaye,i never experience such thing sai a gurinsa,sai kuma a labari or some films,within seconds komai ya faru,sanda ya sake ni kasa kallonsa nayi,jikina ko ina ɓari yake tsabar shock,he give me first kiss of my life,a single lip kiss,hawaye kam bazan iya cewa komai akansu ba,dan tuni sun fara ɗiɗɗiga,a tsorace yayi baya yana kallona yace "kiyi haƙuri Fadwahh! I'm really sorry" durƙushewa nayi a gurin a tsorace na toshe bakina ina kukan da ban san ko na mene ne ba,ya durƙusa a rikice zai taɓa ni,da sauri nayi baya ina girgiza kaina,yace "for the sake of Allah ki yi haƙuri ki daina kuka,forgive me please Jewel" ina sheshsheƙa na fara goge hawaye da sauri²,yana durƙushe har sannan a gabana yana ta ba ni haƙuri,ban kulashi ba na tashi na ɗauki tray na wuce zan fita,da sauri ya riƙe min veil yana sassauta muryarsa kamar zai yi kuka yace "Please! Jewel.. Kada kije kina kuka,idan aka tambayeki me za ki ce?" Wasu hawayen naji sun kawo idona,nayi saurin whipping ɗinsu,ina jan ajiyar zuciya na juya na kallesa,da muryar kuka nace "koma me nace ba damuwarka bane ai" da sauri ya matso yace "kiyi haƙuri Jewel in sha Allah haka bazai sake faruwa ba,na miki alƙawari" banda ajiyar zuciya babu abunda nake,yace "kin haƙura?" Na masa banza ban tankasa ba,yace "please!" A hankali na gyaɗa masa kai ina turo baki,da sauri yace "thank u.. Kije gida sai mun yi waya?" Na gyaɗa masa kai na wuce,sanda ya fita kasa tafiya yayi sai da yaji na kulle ƙofofin biyu na shiga then ya juya ya tafi. A tsakar gida naga Hjy Umma,ban kalli inda take ba na wuce hanyar ɗakinmu,ta bini da wani kallo tace "ehh! Ba shakka fa" clearly na jita sai dai ban ko waiga ba na ƙarasa shigewa,ina shiga na yi tunanin zan samu Aunty a parlour,sai ban ga kowa ba,na shiga da sauri because i was super scared,ina ƙoƙarin ajiye tray Aunty ta fito ɗaki,ban ji motsinta ba sam tace "har ya tafi?" A firgice na saki tray,cup ɗin kai da plate ya faɗi nan take ya tarwatse,da kallo Aunty ta bini tace "ke lafiyarki daga maki magana ki fasa min kaya" a ruɗe nace "kiyi haƙuri Aunty,ban san kin fito ba" na wuce da sauri na ɗauko parker da tsintsiya na tattare broken glass ɗin,Aunty ta bini da wani kallo,sanda na zubar a trash kaina a ƙasa na wuce ɗaki,ina shiga wayata dake gaban madubi ya fara ring,na ƙarasa na ɗauka na kai wayar kunne nayi shiru,Yaa Shaseed yace "Jewel kina fushi da ni har yanzu?" Zaunawa nayi bakin bed ban ce komai ba,yace "ban san yanda zan baki haƙuri ba Jewel" ajiyar zuciya nayi nace "na haƙura ai" yace "thank u Jewel.." Muka yi shiru,sai can yace "idan naje gida zan kiraki please" nace "uhmn! Allah ya tsare" ya amsa min. 2 days tsakani Abba ya kira Hjy Umma da Aunty,suna zaune shiru² suna jiranta sannan ta shigo,Abba ya kalleta bai ce komai ba har ta zauna,bata cewa Aunty ba itama bata ce mata komai ba,Hjy Umma tace "Alh akace kana kira?" Yace "ehh! Akwai maganar da nake son sanar muku,so kada kiji labari rana ɗaya kice an maki rashin adalci.." Hjy Umma tace "tou! Allah yasa alkhairi ne" Abba yace "in sha Allah" Hjy Umma tace "tou! Wane magana ne Alh? Muna sauraron ka" Abba ya gyara zama yace "so ba wani magana bane mai nisa,na kiraku ne na sanar maku,magabatan Shaheed suna son aikowa cikin satin nan" Hjy Umma tace "suna son aikowa kamar ya? Ban gane ba Alh?" Abba yace "ehh tou! Na san dama ba lallai ki gane ba idan ba bayani nayi miki ba" Hjy Umma tace "haka ne,ban san kan maganar ba kam" Abba yace "maganar neman auren ƴarki ne ya taso" baki Hjy Umma ta washe tace "kaii maa sha Allahu.. Wacce daga ciki?" Abba yana murmushi shima yace "Fadwah!" Take fara'ar dake fuskarta ya ɗauke tana kallonsa tace "Fadwah kuma? Wace Fadwan?" Abba ya mata wani kallo yace "wace Fadwah kika sani bayan ƴarki?" Kicin² tayi tace "Alh dan Allah mu bar wasa" yace "na taɓa maki magana irin wannan da wasa?" Ta girgiza kai tace "a'a" yace "tou! Yau baza mu fara ba" shiru Hjy Umma tayi tana kallon Abba in a bit shock tace "Fadwah fa Alh" Abba yace "kina da matsala da hakan ne?" Girgiza kai tayi tace "a'a! Kawai dai na ga har nawa Fadwan take da ba'ayi maganar yayyenta ba sai ita.. Haba Alh itace fa ƙarama a gidan gaba ɗaya" not only Abba hatta Aunty kallonta take sai dai bata ce komai ba,Abba yace "in sha Allah maganar aurenta yana nan tunda ta samu mijin da zai barta tayi karatu,matsayin uba bazan tauye ƴata ba muddin tana sonsa" Hjy Umma banda kallon Abba babu abunda take yi tace "haba Alh! Yanzu fisabilillahi kai sai ka karɓi maganar auren Fadwah,bayan ga babbar yayarsu nan a gida" Abba yace "sai kuma kiyi" a fusace tace "zanyi kam,za kuma kace na faɗa maka" Abba ya gyaɗa kai ya juya yana kallon Aunty da bata ce komai ba yace "Asiya baki ce komai ba" Aunty tace "me zance Alh da ya wuce nace Allah ya kaimu lokacin ya ara mana tsayin rai" Abba yayi wani murmushi yace "ameen yaa Allah" a fusace Hjy Umma ta miƙe tana kallonsu tayi ƙwafa mai ciwo,daga Abba har Aunty babu wanda ya kalli inda take,ta juya ta fita kamar za ta tashi,Aunty ta taɓe baki,sanda ta wuce ɗakinta zarya ta dunga yi wall to wall,gumin tsantsar tashin hankali yana saukowa fuskarta  tace "idan na bari al'amarin nan ya tabbata shegiya uwata ta haife ni,ko zan yi tafiya tsirara wallahi² sai na san yanda nayi aka fasa.. Ƙaryarki ta sha ƙarya Asiya,ki aure min miji sannan yanzu ina kallo in bari ƴarki tayi aure ta bar min nawa a gida muna goga kafaɗa da su,wallahi bazai yiwu ba.." In the meantime gidan sam babu daɗi,though dama ba wai shiga harkar juna ake ba,cikin kwanakin da suka biyo baya sosai al'amura suka sake lalacewa,ranar ana gobe iyayen Yaa Shaheed za su zo neman masa aure na,tun da safe da na tashi haka kawai nake jin haushin kowa,abu kaɗan aka min sai naji raina ya ɓaci,sai ban ɗauki hakan as matsala ba da zai iya faruwa anytime,na barshi matsayin kawai mood swings ne,saboda ina irin haka time to time,na ci gaba da harkokina,gaba ɗaya ranar kuma sai bamu yi waya da Yaa Shaheed ba,abunda zauna gari banza sai muyi waya a yini ya fi sau 5,amma ranar har akayi maghreb babu wanda ya kira wani tsakanin mu,lokacin ana kiran sallar isha ya gaji da jiran na kirasa ya kira ni,sanda na kalli wayar kamar bazan ɗauka ba saboda haushinsa da nake ji,na kuma rasa dalili,can na daure nayi answering na kai wayar kunnena,a fusace ko sallamar da nayi bai amsa min ba yace "wane irin wulaƙanci ne wannan?" Na daure ina haɗiye wasu terrified salivas nace "a ina?" A fusace yace "ban sani ba,ni za ki rainawa hankali?" Ji nayi zuciyata ta yi wani yunƙurowa kamar zan yi amanta ta baki nace "dan Allah Malam dakata,akan me za ka rufe ni da faɗa,me na maka ne?" Zaro idanuwa yayi yace "ni kike faɗawa haka Fadwah? Saboda kin raina ni,ni kike cema na dakata?" A masife nace "akan me tou daga kirana za ka kama yi min faɗa,ba sai ka sanar da ni ba idan na maka wani laifi" ƙwafa yayi yace "kin kyauta na gode" daga haka ya katse kiran,siririn tsaki nayi na ɗaga shoulders nace "kai ka sani.. Rainin hankalin banza da wofi kawai,za ka wani kirani sai kace ƴarka ka kama yi min faɗa" haka nan tunda muka gama wayar duk zuciyoyinmu suka yi mana babu daɗi,can ya kasa haƙuri ya sake kirana,na ɗauka kafin nayi magana yayi calming muryarsa yace "My Jewel ina son zuwa na ganki" taɓe baki nayi nace "ohh! Ka gama fushin?" Kamar mai jira yace "ban gane na gama fushi ba? Wai wane irin magana ne kike kwaɓa min?" Taɓe baki na sake yi nace "kamar ya nake kwaɓa maka? Naga dai kai ka kira ka kama min faɗa kou?" Yayi ƙwafa yace "kinga mubar maganar nan please ina hanyar zuwa yanzu" nace "Allah ya kawo ka lafiya.." Bai amsa ba ya katse kiran. Ina zaune har sanda ya ƙaraso,da ya kira yace min ya zo,sai da na shafe 10 minutes kafin na ɗauki veil na fita,na sameshi zaune cikin motarsa ƙiran chevrolet,na ƙarasa ganin glasses ɗin a rufe yasa nayi knocking,banza yai min sai da na ɗauki almost 10 minutes tsaye a gurin,abun haushin kuma duk da glasses ɗin was tinted ina hango hasken wayarsa,sanda na gama fusata kawai nayi wucewa ta gida,ina shiga ya kirani,ban ɗauka ba sai da yai min missed call 3,then na ɗauka na kai wayar kunnena,a zuciye yace "dan walaƙanci shi ne za ki koma ki barni ina jiran ki?" A masife na hayayyaƙo masa nace "tun yaushe na fito kana kallona kai min banza" yace "ohoo! Ashe babu daɗi,ni kika sa naita jiranki,ko an faɗa maki ban da aikin yi ne sai na ki da za ki shanyani?" A tsiwace nace "nima ai baka ji na faɗa maka haka ba bare kace" yace "ni kike faɗa ma magana?" Nace "da baka fara ba nima babu yanda za'a yi na gaya maka,saboda kowa ya san ba halina bane yiwa na gaba dani rashin kunya" yace "ni ai halina ne" nace "wa ya sani" a fusace yace "kinga dakata,ki daina wani ɓoye² na ga sai wani jin kanki kike,ki fito fili ki sanar min abunda yake ranki,idan wannan halin za ki ci gaba da gwada min,ai babu dole sai a haƙura" kafin ya ƙarasa nace "tou a haƙuran mana sai me,ko ka ji na ce maka lallai sai da kai zan rayu? Dan ka barni akace maka bazan ci gaba da rayuwa bane?" Yace "haka kika ce?" Nace "na faɗa ɗin,ko ance maka kai ne autan maza? Ka barnin mana sai me?" Kansa kawai ya girgiza ya katse kiran,nayi tsaki ban kuma bi ta kansa ba na shiga uzorori na.....

     *This book is not for free,it's #200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added in the paid group. Ƴan Niger za ku iya tuntuɓar wannan number +22770766074.*

   

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

IN-LAWSDonde viven las historias. Descúbrelo ahora