Magnanimous

132 18 9
                                    

💠💠💠💠💠
©®2021.



                     *♡IN-LAWS¸.•💥*
       

Bʏ.
   *HAWWA MUH'D USMAN.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
        
*FREE PAGE*

                               05-06

#Magnanimous

   *Wanda basa cikin ko wane group nawa,kuma suna neman inda za su dunga ganin update na novels ɗina,za ku iya joining link ɗin dake ƙasa,kai tsaye zai kai ku inda za ku dunga samun update nan take.*
    https://chat.whatsapp.com/LBB3KAJf4pQK0JxfvrweOM

💕
        Wani irin faɗuwa gabana yayi sanda idanunmu suka yi merging,yana tsaye nesa da mu,cikin wani dakakkiyar shaddarsa light ash,kyakykyawan saurayi ne da bazai wuce 32yrs ba,skin ɗinsa mai ɗan duhu irin na ƴaƴan hutu,tun daga sama har ƙasa colour ɗin dake jikinsa kenan,da sauri na juya ina ɗan taɓa baki,sakin hannuna Yaa Waleed yayi yace "i'm coming twiny" nayi masa murmushin yaƙe ina langaɓar da kaina nace "kada ka daɗe tou" cheecks ɗina yaja yace "kin cika fi'ili kamar wata budurwata har wani commanding ɗina kike" nayi fari da idanuna nace "ehh ɗin.. Ai matar ma sai wanda na yarda za ka aura,ƙarewa ma ni zan nemo maka" dariya ya fashe da shi yace "llallaima yarinyar nan.. Wallahi kin raina ni da yawa,but kada kiga ina ce miki twiny kiyi tunanin tare aka haife mu,good 3 yrs ne tsakanina dake.." Nace "ai na sani.. Dan Allah jeka ka dawo ni dai" juyawa yayi yace yanzu kuwa" yana tafiya Abbanmu suka ƙaraso gurin da muke tare da Abban Umaimah,da sauri na karɓe allona da gifts ɗina a hannun Yaa Umar na miƙa masa ina ta murmushi,sanda Abba yake duba certificate ɗina a gurin grade yaga *A* boldly yayi wani murmushi yana gyaɗa kai yace "maa sha Allah! Allah ya sanya albarka.. Ashe dai ban yi asaran kuɗina ba duka" cikin jin daɗi nace "ameen Abba.." Ya karɓi na Umaimah ma ya duba yaga itama *A* ne da ita,yayi saurin kallonmu yana girgiza kai yace "Fadwah! Ya akayi na ƴan uwanki grade ɗinsu C?" Kafin nayi magana Yaa Umar yace "Abba ai ba ƙoƙarin su ɗaya ba.. Kuma ko bayan haka mu gadon ƙoƙari muka yi gurin Aunty'nmu" wani murmushi Abba yayi yana kallon Aunty dake murmushi yace "kada ka zugata da yawa Farouk" Yaa Umar yayi dariya yace "ai ko ban faɗa ba Abba,wanda suka santa sun san she's talented" Abba ya gyaɗa kai yace "cikin wanda za su bada shaidar kuwa har da ni ma" muka yi dariya dukanmu,Abban Umaimah ya karɓa shima yana sanya mana albarka,a nan camera man yayi mana pictures,Abba suna ƙoƙarin tafiya na shagwaɓe nace "Abba ba'a yi mana da Yaa Waleed ba za ka tafi" Abba ya waiga² bai ganshi ba yace "ina Waleed ɗin ya tafi?" Ina turo baki nace "ga shi can wancan mutumin ya kirasa tun ɗazun,ko me ma yake ce masa ohoo.." Abba yace "Mukhtar je ka yi masa magana sauri nake zan tafi" Yaa Mukhtar yace tou Abba ya tafi kiran Yaa Waleed. Lokacin da Yaa Waleed ya ƙarasa kusa da shi yayi masa sallama,calmly ya amsa yana kallon Yaa Waleed ya lumshe idanuwansa ya buɗe sanda ya amsa ya miƙawa Yaa Waleed hannu suka yi musabaha,Yaa Waleed yana kallonsa da rashin sani yace "kai kace ayi min magana?" Yana gyaɗa kai yace "yeah!" Yaa Waleed ya gyara tsaiwarsa yace "Allah yasa lafiya dai" sanyayyan murmushi yayi masa yace "lafiya lau.. Sai alkhairi" Yaa Waleed yayi murmushi shima yace "Okay! Ina saurarenka" calmly yace "suna na Muhammad Shaheed Mahmoud Tafeeda.. I'm the first born of my Dad,ni ɗan Tafeedan Kano ne" Gyaɗa kai Yaa Waleed yayi yana masa murmushi yace "Okay! How may i help u?" Wani kallo ya yiwa Yaa Waleed jin abunda ya faɗa,kafin yace "sorry.. I'm just want to know something,wace ce wanda na ganku tare? I mean ya kuke da ita?" Kamar Yaa Waleed bai gane tambayar ba yace "think i did'nt get u.. Who's she? Wa kake magana akanta?" Yace "the girl da kuke snapping pictures there" murmushi yayi yace "think baka ga dai² ba,ai su biyu ne muke tare,wacce kake magana akanta?" Shaheed yace "the one da ka riƙema hannu" murmushin da ya bayyana tooth ɗinsa Yaa Waleed yayi yace "oops! I'm sorry,she's my sister" murmushin shima yayi yana ɗan ƙanƙantar da idanunsa yace "thank u.. But zan iya sanin wasu bayanai a kanta?" Yaa Waleed yace "bayanai kamar na me fa?" Yace "i mean ko kun yi mata miji a gida?" Dariya sosai Yaa Waleed yayi yace "miji? Wannan abar za mu yiwa miji? Yarinya ce fa ƙarama,duka ko 18 yrs bata kai ba.. Yanzun ne take final year a secondary" da mamaki a fuskar Shaheed yace "u want me to agree?" Yaa Waleed yace "why not? Tunda na faɗa maka ai ya kamata ka yarda,same parent muke,daga ni sai ita,ka ga ai bazan faɗa maka karya ba" Shaheed yayi murmushinsa mai kyau yana sake kallon Yaa Waleed,underneath mamaki yake da Yaa Waleed yace daga shi sai ita,yanda yake wani gabjeje a tsaye ga faɗi kamar wani basamude sai kayi zaton shi ne babba tsakanin shi da su Yaa Umar yace "Okay! I agreed,but i love her,za ku ba ni ita?" Dariya sosai Yaa Waleed yake yi cike da barkwanci yace "mu baka kuma kamar wani kayan siyarwa?" Shaheed yace "yeah! Da gaske ina sonta and ba da wasa nake ba.. Aurenta nake son yi in dai za ku ba ni" Yaa Waleed ya ga abunda ya fi ƙarfinsa yana dariya yace "a'a! Sai dai muje na kaika gurin Abban mu kuyi magana.." Shaheed yana lumshe idanu yace "oohhh! Thanks alot brother,but ka bani digit ɗinka zan kiraka idan zanzo,because yanzu ina sauri za mu tafi,tare da Daddy muke and ba ya son jira" Yaa Waleed yace "Okay! No worries.." Suka yi exchanging digit,Shaheed ya miƙa masa hannu fuskarsa da wani yalwataccen murmushi yace "thanks alot brother for ur help.." Yaa Waleed yace "pleasures are mine brother.." Suka yi sallama,yana tafiya Yaa Waleed ya juya zai tafi shima dai² nan Yaa Mukhtar ya iso yana kallon Yaa Waleed yace "waye kuke tsaye tare da shi?" Yaa Waleed yayi dariya yace "walata jasassu akhiiy.." Dundu Yaa Mukhtar ya ɗuma masa yace "kai ni sa'anka ne?" Yaa Waleed ya fashe da dariya yace "idan aka kallemu ni da kai waye za'a ce gaba da wani?" Yaa Mukhtar yace "kai mu bar maganar nan,Abba ne yake kiranka za kuyi photo sauri yake za su tafi" Yaa Waleed yace "Okay! Let's go" suka nufo inda muke,sanda muka yi hotuna tare da Abba da yayyuna aka mana ni da Abba da Aunty,har inda muke Yaa Abbas,babban Yayanmu da Aunty Fatima suka zo suka min Allah ya sanya alkhairi suka yiwa Aunty ma,mai photon da Yaa Umar ya ɗaukar min yayi mana hotuna tare da su mukayi da su Aunty,sannan muka yi da ƙawayenmu,haka Umaimah ma da yayyenta da suka zo kasancewar dukansu mata ne su 4,kuma daga gidajensu suka zo,sanda muka gama ɗauke²n hotuna,Aunty tasa su Yaa Waleed suka ɗauki kayan da muka zo da su suka bayar a makaranta sannan muka tafi gida. Da yamma sanda za mu yi walima,ni da Umaimah komai namu a haɗe yake guri ɗaya,su Juwairiyya ma sun ware ko magana basa mana,ni kam dama ba na kulasu saboda gudun wulaƙanci,after asr sanda muka sake yin wanka muka shirya cikin wani lace da Yaa Umar yayi mana ni da Umaimah,Yaa Waleed ya karɓo key ɗin mota gurin Abba ya kaimu wani make-up parlour aka yi mana saboda ƙawayenmu na islamiyya da na school da muka gayyato,kamar ana bikinmu haka muka dawo mun sha make-up,tun da Aunty ta ganmu take faɗin "maa sha Allah.. Ƴan matana sun yi kyau" Aunty Fatima ta kallemu tace "kai ƙanwata wannan kwalliyar fa haka kamar ana bikinki? Gaskiya kun yi kyau babu hassada" nayi murmushi nace "mun gode Aunty.." Sanda colleagues ɗinmu suka fara zuwa,ƙofar gida muka fita mukaita ɗaukan hotuna,sai da akayi maghreb sannan taron ya tashi. Lokacin na idar da sallah kenan,ina zaune parlour,Yaa Umar da Yaa Mukhtar ne kawai,sai ga Yaa Waleed ya shigo ɗauke da manyan cartoons ɗin lemo a both hannuwansa,sanda ya ajiye muka bishi da kallo sai dai babu wanda yace masa komai,ya fita ya sake shigo da wasu,sanda ya jera 20 cartoons na lemo da ruwa,ya faɗa saman kujera yana faɗin "washh! I'm too tied up wallahi.. Dama idan na kwanta baza a tashe ni ba sai gobe irin around 10am ɗin nan" Yaa Umar dake zaune yana cin abinci da shirt a jikinsa irin na sojoji ya masa wani kallo yace "sallah kuma fa? Sai a bari sai lokacin da kaga dama ka tashi kayi?" Dariya yayi yace "ehh wallahi" ɗauke kai yayi yana ci gaba da cin fried rice with chicken dake gabansa yace "saboda kana haila kou?" Gaba ɗaya muka fashe da dariya,Yaa Waleed yayi sauri ya tashi yace "bari nayi gaba kafin nayi magana ka zane ni.. Ku dama militant ɗin nan abu kaɗan kuke jira" murmushi Yaa Umar yayi yace "ai kaima jira nake ka kammala school na nema maka aiki a gidan soja,masu irin ƙiran jikinka dama ake so a gurin,wanda ganinku kawai mai laifi yayi zai tsorata" wani zaro idanuwa Yaa Waleed yayi yace "kaiiii Yaya! Wane mutum,a'a wallahi ka dai nemarwa Yaa Mukhtar" dariya Yaa Mukhtar yayi yace "saboda ni ne marainin wayonka kou?" Da sauri Yaa Waleed ya fice yana dariya yace "ai da akace ni shiru naga ka yi saboda ka gaji dani.. Haka kawai na shiga gidan soja lokaci na baiba wata rana gurin yaƙi a alburushe ni.. Shi Kenan fa tawa ta ƙare tun ban ajiye masu min addu'ah ba" yana fita Aunty ta fito ɗaki tana kallona tace "idan kin idar da sallan ki tashi dama kije ki kwashe min kayanki daga kan gadona,bai zama jaki ba bare ki mayar min shi loundry ɗinki" murmushi nayi nace "tou Aunty zan kwashe" tace "sai yaushe?" Ina langaɓar da kai nace "da abinci zan ci sai naje na ɗauke" wani kallo tayi min tace "tashi ki wuce ki bani guri kafin na falla maki mari,idan ma baza ki zauna ki naɗesu ba ni dai ki sauke min su daga gado na,dama kuma ki san inda za ki kaisu daga nan,kada ki kuskura ki sa min su cikin press a haka" kamar zanyi kuka na tashi na wuce,Aunty ta zauna tana kallon cartoons ɗin lemo dake ajiye ta kalli Yaa Mukhtar dake danna wayarsa tace "wannan kuma na waye? Wa ya shigo da su nan?" Yaa Mukhtar yace "Waleed ne" tace "ina yake?" Yace "ya fita yanzu" ta gyaɗa kai tace "bai muku bayanin wanda ya aikosa ba?" Yaa Mukhtar yace "kawai ajiyewa yayi ya fita" tace "okay! Zai shigo ya min bayani.." Daga haka bata sake cewa komai ba. Yaa Waleed yana fita ya samu Shaheed a cikin mota ƙiran hyundai veloster white colour,yayi knocking glass ɗin Shaheed dake zaune ciki ya buɗe motar ya sauko da ƙafarsa ɗaya waje yana kallon Yaa Waleed yayi murmushi,a hankali Yaa Waleed yace "yana fitowa yanzu" gyaɗa masa kai Shaheed yayi yace "thank u" then ya ƙarasa buɗe motar ya fito,suna tsaye suna hira Abba ya fito,Yaa Waleed ya kalli Saheed yace "bari na shiga ciki kafin ku gama" Shaheed yayi masa godiya,sanda ya wuce Abba ya ƙaraso,har ƙasa Shaheed ya durƙusa ya gaishesa,Abba ya amsa yace "kai ne kake magana?" Shaheed yayi murmushi yace "ehh Abba" Abba yana kallonsa yace "tou mu ƙarasa ciki" Shaheed yace "tou Abba,na gode" Abba ya wuce forefront ya bisa a baya,parlon baƙi wanda ƙofarsa yake nan ta waje sannan akwai wani ta cikin gida Abba ya buɗe musu suka shiga,sanda suka zauna Abba ya danna wayarsa yakai kunne,sanda aka ɗauka yace "kisa a kawo ruwa parlon baƙi yanzu.. I've a guest" then ya katse kiran ya ajiye yana kallon Shaheed yayi murmushi yace "afuwaan! Na zaunar da kai kuma ina waya" Shaheed yayi murmushi yace "babu komai Abba" suka sake gaisawa then Abba yace "samari daga ina? Ban gane ka ba?" Calmly kan Shaheed a ƙasa yace "Abba! Da farko dai ni suna na Muhammad Shaheed Mahmud Tafeeda" Abba yana kallonsa da kyau yace "kai ɗan wajen Alh Mahmoud Tafeeda ne?" Shaheed ya gyaɗa kai yace "ehh Abba,ni ne babban ɗansa" Abba yayi wani murmushi yace "Allah sarki.. Ai kai ɗa ne a gurina,tare da mahaifinka muka yi secondary school,a nan Rumfa College,daga can muka sake tafiya ABU Zaria,tare muka ya karatu har masters department ɗaya muka yi,sai dai rashin zumunci yasa bama haɗuwa sosai kamar da" Shaheed yayi murmushi yace "Allah sarki" Abba yace "maa sha Allah,ya mahaifan naka suke? Suna lafiya?" Shaheed yace "suna lafiya" Abba yace "maa sha Allah.." A cikin gida sanda Yaa Waleed ya shigo ya zauna saman armchair,Aunty tana masa wani kallo tace "kai yallaɓai wa ya aikoka da wannan kayan ka ajiye min su nan?" Yaa Waleed ya kalli abunda take nuna masa yayi murmushi,sanda ya kalli su Yaa Umar da suke kallonsa suna jiran suji me zai ce,ya ɗauke kai yace "baƙon da Abbanmu yayi ne" Aunty tace "baƙon Abbanku?" Ya gyaɗa kai yana murmusawa,Aunty ta ɗauke kai bata sake ce masa komai ba,lokacin na fito ɗaki bayan na naɗe kayana da barbaza saman gado,Abba ya kira Aunty a waya,sanda ta gama saurarensa tana kallona tace "Fadwah!" Da sauri na juyo nace "na'am!" Tace "ki ɗau ruwa ki kai parlon Abbanku ya yi baƙo" amsawa nayi na ajiye plate ɗin hannuna,na tafi na buɗe fridge na ɗauki bottle water da lemo na ɗora kan madaidaicin tray na ɗora  glass cup ɗaya,sanda na ɗauki hijab ɗina har ƙasa then na ɗauka na fita,ta ƙofar cikin gida nayi knocking,Abba yace "shigo a buɗe ƙofar yake" na murɗa handle ɗin na shiga da sallama,suka amsa min,na ƙarasa na ajiye ban ɗago ba nace "ina yini?" Tunda na shigo yake kallona,calmly ya amsa min,na tashi zan tafi na ɗago muka haɗa ido,gabana yayi wani mahaukacin faɗuwa da sauri na wuce na fita ya bini da kallo,Abba yace "ga ruwa nan ka sha" yace "na gode Abba.. But wani alfarma ne ya kawo ni gurinka" Abba yace "tou alfarmar mene ne? Allah yasa ina da iko akansa" Shaheed yayi murmushi,sanda ya gyara zamansa calmly yace "Abba! Dama ɗazu a gurin sauka ne na ga wata yarinya,tou lokacin ko da nayi bincike akanta,sai na gano a nan gidan take,kamar yanda Waleed ya sanar min,saboda da shi muka yi maganar ta,shi ne na yanke nazo na nemi izini gurinka,kafin na jema Daddy da maganar" tunda ya fara magana Abba yake jinjina kai kafin yace "wace ce a ciki? Ƴaƴana mata huɗu ne,ban san wacce kake magana ba" kan Shaheed a ƙasa yace "wanda ta fita yanzu" kallonsa kawai Abba ya tsaya yi da mamaki ya kasa cewa komai,jikin Shaheed a sanyaye ya ɗago kai jin Abba bai ce komai ba calmly yace "dan Allah Abba kada kace baza ka bani ita ba,wallahi da gaske nake aurenta nake son yi,idan ka amince min a yau zan sanarma Daddy,sai yazo kuyi magana..."

     *This book is not for free,it's #200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added in the paid group. Ƴan Niger za ku iya tuntuɓar wannan number +22770766074.*

    _Alhamdulillah alaa kulli halin.. I'm done with the promos saura free page shima ina kusa da gamasa in sha Allah,and i also fulfilled my promise kamar yanda na ɗauka wa mutane biyar,gamai son both novels ɗina zai biya #500 ne via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,Access Bank,idan ɗaya kike so kuma za ki biya kuɗinsu kamar yanda yake,idan ba kya son group,za ki biya 1k for both,idan ɗaya kike so za ki biya #500,via same account,masu both da SP if u don't have an account ki je gurin masu POS su tura. My sisters and manyan hajiyoyi idan kin shirya maza kije ki biya naki,because idan na kammala free page za mu ci gaba ne babu tsayawa in sha Allah. Na gode._
   

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

IN-LAWSWhere stories live. Discover now