Intermission

195 16 5
                                    

💠💠💠💠💠
©®2021.


                     *♡IN-LAWS¸.•💥*
       

Bʏ.
   *HAWWA MUH'D USMAN.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*TELEGRAM:* https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA
      

*LAST FREE PAGE*

'''Yaa rabb grant her shifaa..🤲'''

                               11-12

#Intermission

      A ɓangaren Yaa Shaheed sosai abunda nayi ya ɓata masa rai,sanda ya ƙarasa gida direct bedroom ɗin Mom ɗinsa ya wuce,Hjy Maimuna tana zaune ya shigo,a ciki² yayi sallama,ta ɗago ta bisa da kallo sanda ya zauna saman sofa,fuskar nan a ɗaure as if he didn't know how to laugh,Hjy Maimuna tace "kai lafiyar ka za ka shigo min haka saƙam² babu magana?" Yayi ƙwafa a hankali yana gyaɗa kai yace "i'm sorry Mom" ta bisa da kallo tace "lafiya?" Shiru yayi sai da ya mula dan kansa yace "Mom dan Allah ina so kice ma Daddy a dakata da maganar kai kuɗin nan" kallonsa ta dunga yi with suspicions tace "ko saboda me?" Yace "haka kawai" girgiza kai tayi tace "no son! Tell me if there is a problem" gyara zama yayi yace "Mom ban san me yake damun yarinyar nan ba,idan wani ta gani da ya fini ai sai ta fito ta sanar min,amma dan walaƙanci na je gurinta ta shanyani,ƙarshe da ta fito ma komawa tayi.. So ni dai na yanke shawarar haƙura kawai.." Banda kallonsa babu abunda Hjy Maimuna maimuna keyi,tace "kuma babu wani abun da ya haɗaku?" Girgiza kai yayi yace "babu" ta sauke numfashi tace "ka san Dardy'nku bazai taɓa amincewa da maganar nan ba kou?" Yace "please Mom" tace "shi kenan zan sanar masa,amma kasan Allah babu ruwan,zancen kace ka fasa ma bai taso ba,ka bari dai ko tambayar tane ayi aji,but kaje kaita addu'ah" amsawa kawai yayi da "tou!" But not because he wanted to,ya tashi fuska ɗaure yace "good night Mom" tace "Allah ya tashe mu lafiya" yace "ameen.." Yayi waje bai ko tsaya ba. Sanda Hjy Maimuna take sanar da Daddy maganar da suka yi da Yaa Shaheed,Alh Mahmoud ya tsaya kallonta sanda ta kai ƙarshe yace "ni zai mayar ƙaramin mutum?" Hjy Maimuna tace "tou ni dai ranka ya daɗe na kasa gane kan al'amarin nan,na dai ce masa yaje yayi addu'ah" Alh Mahmoud yace "it's better for him,amma zancen yasa ni dakatawa bai taso ba,gobe idan Allah ya amince za muje mukai kuɗin gaisuwa,ko ya mayar da hankalinsa jikinsa ko kuma za musa ƙafar wando ɗaya da shi" daga haka yaci gaba da abunda yake. Washe gari da safen around 10am Abba ya shirya tare da Abban Umaimah,sai Yaa Abbas da Yaa Umar,sai ƙaninsa ɗaya Uncle Haroun,to 11am iyayen Yaa Shaheed suka ƙaraso,Daddy'nsa with few of his friends,bayan sun gama gaisawa kafin a karɓi kuɗin,Abba ya kalli Yaa Umar yace "Farouk!" Yaa Umar yace "na'am Abba" Abba yace "zo na aike ka gurin Aunty'nku" Yaa Umar ya tashi ya matsa kusa da Abba,raɗa Abba yayi masa a kunne,Yaa Umar ya tashi yace "tou Abba" ya shiga cikin gida,sanda ya shigo ɗakinmu ya tarar da Aunty a parlor tare da Yaa Mukhtar suna hira,Yaa Umar yayi sallama,sanda suka amsa kallon Aunty yace "Aunty Abba sent me" Aunty tace "wai me?" Yace "he said ki tambayi Fadwah kafin a amshi kuɗin gaisuwar da suka kawo,idan tana sonsa aje a sanar masa" Aunty tayi murmushi tace "okay" ta tashi ta wuce bedroom,ina kwance lokacin kan bed ina chat,Aunty tayi sallama ta shigo,na ɗago kaina ma amsa,bakin gadon Aunty ta zauna tana kallona tace "Fadwah!" Da sauri nace "na'am" gabana yana faɗuwa,tace "get up and sit down,i want to talk to u" nace "tou" na tashi na zauna nayi backlight ɗin wayar,kaina a ƙasa ina fidgeting fingers,a hankali Aunty tace "kina ji na?" Na gyaɗa kai nace "Mmmm!" Tace "Abbanku ya aiko yanzu to ask if u really love Shaheed,za su karɓi kuɗin gaisuwar da suka kawo" saurin ɗago kai nayi ƙirjina yana bugawa da ƙarfin gaske na girgiza kai nace "no Aunty" kallona ta dunga yi tace "kamar ya a'a? What do u mean?" Nace "i just don't like him" mamaki ne ya hana Aunty magana sai kallona take tace "Fadwah! Ki faɗa min gaskiya.. Are u serious?" Na sake girgiza kai nace "da gaske ba na sonsa" Aunty tace "ba kya sonsa?" Na gyaɗa kai,ta sauke numfashi tace "wani abu ya haɗa ku ne? Ko Shaheed ɗin ya yi maki wani abu da kika ji bakya sonsa kuma?" Nan ma na girgiza kai nace "a'a ni dai haka nan naji ba na sonsa yanzu" kasa magana Aunty tayi,sanda tayi juyin duniya na sanar mata nace babu,ta tashi ta fita ɗakin,ta samu Yaa Umar zaune suna magana da Yaa Mukhtar tana kallonsa fuskarta babu walwala tace "Umar je kama Abba magana" da sauri yace "akwai matsala ne Aunty?" Tace "kirashi dai yazo,na kasa gane abunda yake son faruwa" Yaa Umar ya tashi ya fita,not too long suka shigo tare da Abba,zuwa lokacin hankalin Aunty sam ba ya jikinta,Abba yace "lafiya Asiya akace kina magana?" Aunty tace "Alh akwai matsala" yace "wane irin matsala kuma?" Tace "wallahi na kasa gane kan Fadwah,na tambayeta kamar yanda kace,amma wai tana ce mun ba ta sonsa,dan Allah ka tambayeta ta sanar maka idan ma wani abu ya haɗa su" shiru Abba yayi yana sauraren Aunty,Yaa Umar da Yaa Mukhtar kansu they were in shock,Abba yace "ina take?" Aunty tace "tana nan a ɗaki" wucewa Abba yayi ɗakin yayi sallama,a hankali na amsa na tashi na zauna ina sunkuyar da kai,ya zauna gefen gado inda Aunty ta tashi,yana kallona a hankali yace "Fadwah!" Na amsa,yace "what's going on? Wani abu ya haɗaku ke da Shaheed?" Kai na kaɗa nace "a'a" yace "tou me ya faru kika ce ba kya sonsa?" A hankali nace "babu komai" duk yanda Abba yaso na sanar masa abunda yake faruwa "nothing" was the only answer da nake bashi,daga ƙarshe sanda ya girgiza kai yace "tunda babu abunda ya haɗa ku,kuma iyayensa sun ruga sun zo sai dai kiyi haƙuri kiyi ta addu'ah,amma babu abunda zai sa a fasa karɓan gaisuwar da suka kawo,ya rage naku ku shirya kanku,amma aure babu fashi.." Daga haka ya fita ɗakin,fashewa da kuka nayi mai cin rai,har zuciyata nake jin ƙiyayyarsa,na kwanta ina kuka can wata zuciyar tace ki kirashi,a zabure na tashi na ɗauki wayata na kira number sa,yana ɗauka cikin kuka nace "wallahi ba na sonka,bazan aureka ba" a fusace yace "tou ni ɗin ance maki zan aureki ne?" Nace "ohoo! Ai shi yasa naga ka dage ka turo iyayenka gidanmu,na rantse da Allah aka takura min kan aurenka zan gudu na bar gida" tsaki yayi yace "akan me iyayena za su zo,bayan na sanar na fasa?" Cikin ƙaraji nace "ehh! Ka fasa ɗin ne su kuma suka dage sai da suka zo,yanzu aka sa ni gaba ana min tambayar ina son ka?" Da sauri ya katse ni yace "wait.. Yaushe suka zo?" Nace "ban sani ba,sai kaje ka tambaya" nayi tsaki na kashe wayar,ransa idan ya yi dubu ya ɓaci,a rayuwarsa idan akwai abunda ya tsanana bai wuce ayi masa tsaki ba,a fusace ya fito flat ɗinsu shi da kannensa maza ya wuce apartment ɗin iyayen dake ɗauke da tambarin sarauta,yana shiga ya samu Mom a parlor tare da su Ihsan,fuskarsa yana nuna tsantsar tashin hankali yace "Mom! Ina Daddy ya tafi?" Bata kalleshi ba tace "sunje karɓar maka aure" a tsorace yayi baya yace "whattt?" Sai lokacin ta ɗago ta kalleshi ta gyaɗa masa kai tace "Yes!" A hargitse yace "Mom! Didn't u tell him na fasa?" Tace "ya ce baza ka mayar da shi ƙaramin mutum ba,so ina ga kayi haƙuri idan ba wani matsala ne babba a tsakaninku ba kaje ku sasanta,zai fi maka akan kaita jayayyar nan" juyawa kawai yayi ya fita ba tare da ya ce komai ba,da sassarfa ya nufi parking spot dake ɗauke da luxury cars,ya buɗe wani Prado ya shiga,da mugun gudu ya bar gidan,yana zuwa ƙofar gidanmu yayi parking ya fito,sanye da ƙananan kaya jikinsa,seeing that ƙofar sitting room ɗin Abba a buɗe,ya ƙarasa gurin fuskarsa cike da matsanancin tashin hankali yayi sallama,Alh Mahmoud ya ɗago yana kallonsa yace "Hey! Mr Man? What are u doing here? Didn't u wait for me to come back?" Yaa Shaheed yace "please Daddy i want talk to u" Alh Mahmoud yace "wane magana ne da baza ka jira na dawo gida ba?" He knelt down a gaban mahaifin nasa idanunsa sun kaɗa sun yi wani mugun sauyawa yace "please Daddy kayi min rai,wallahi² ba na jin sonta a raina,dan Allah ka yi haƙuri ka barni na kawo wata" kallonsa Alh Mahmoud ya dunga yi ransa a ɓace yayi masa wani tsawa,Yaa Shaheed yace "dan Allah Daddy kayi haƙuri a dakatar da maganar" kyakykyawan mari Alh Mahmoud ya ɗauke Yaa Shaheed da shi cikin ɓacin rai yana nunasa yace "ni za ka tozarta Shaheed? Ni za ka mayar ƙaramin mutum?" Uncle ne yayi saurin intervening yace "ashha! Alh Mahmoud it's better for u to listen to him,bai kamata ka tauyesa ba,yana da kyau kaji dalilin da yasa yace ya fasa" Alh Mahmoud cikin ɓacin rai yace "babu wani uzurin da zan tambaye shi,iskanci ne kawai ya cika masa kai,tun yaushe nake bin yaron nan ya fito da mata ya tsaya wasa,yau kuma yazo yana ce min a dakata,uwarsa za'a tsaya jira?" Uncle da abokan Alh Mahmoud sai haƙuri suke bashi amma bai saurara ba,ya buɗewa Yaa Shaheed wuta sai faɗa yake masa,a haka Abbanmu ya shigo ya samesu,yana kallon Yaa Shaheed da mamaki,jin irin faɗan da Alh Mahmoud yake yasa Abba cewa "lafiya? Did anything happened?" Alh Mahmoud yace "banda yaron nan da hauka,he just come yana kallona direct in the eye yana ce min wai ya fasa a dakata" girgiza kai Abba yayi yace "subhanallah! Tou nima dai na kasa gane me yake faruwa,yanzu na shiga gida mahaifiyar yarinyar tana sanar min itama yarinyar ta ce ba ta so,wane irin al'amari ne wannan?" Kaf occupants ɗin gurin tsayawa kallon Abba suka yi with suspicion,duk yanda muka yi ya sanar musu,shiru duka occupants ɗin suka yi,gaba ɗaya Alh Mahmoud was speechless,Abba yayi ajiyar zuciya yace "it would be better for us mu dakata,since both of them said they don't want to,i think we should just be patient with this,akan muyi ta dagewa" Alh Mahmoud dai ya yi shiru bai sake magana ba,amma kallo ɗaya za ka masa kasan ransa ya kai ƙololuwa gurin ɓaci,wani abokin Abbanmu ne yayi gyaran murya yana sauke numfashi yace "if u don't mind,i've a suggestion" Abba yace "akan mene ne?" Alh Luƙman yace "tunda Allah ya sa duk kunyi niyyar ƙarfafa zumunci ta hanyar haɗa aure,why not tunda Allah ya sa kana da wasu ƴaƴan mata ya duba a ciki idan da wacce tayi masa?" Abba yayi shiru yana kallon abokin nasa ya kasa cewa komai,Abban Umaimah ya gyaɗa kai yace "haka ne Alh,we should look at Alh Luƙman's advice if possible me zai hana ayi hakan" Abba yayi murmurshin ƙarfin hali saboda kada abokin nasa yace ya gwalesa sai dai bai ce komai ba,wani friend ɗin Alh Mahmoud da suka zo tare ya kalleshi yace "Alh Mahmoud baka ce komai ba" cikin ɓaci rai Alh Mahmoud yace "me zan ce akai Alh Ahmad? Ni zan sake yin magana ne ya kunyata ni?" Yaa Shaheed dake zaune gaban Daddy'n nasa yayi ƙasa da kai,Alh Ahmad ya girgiza kai yace "alright! Bari nayi magana da shi tunda kai baza ka iya ba" ya kalli Yaa Shaheed yace "Shaheed taso muje" a hankali Yaa Shaheed ya tashi yabi abokin mahaifin nasa suka fita,jikin mota suka tsaya yana kallonsa yace "ka ji abunda akace ai?" Ya gyaɗa kai yace "ehh Abba" Alh Ahmad yace "tou me kake gani? A jira har ka duba ɗin ko kuwa kana nan kan bakanka?" Jikin Yaa Shaheed a sanyaye yace "a'a Abba,ba sai na duba ba,duk wacce aka ga ta dace a cikinsu shi kenan" Alh Ahmad yace "ka tabbata?" Yace "sure Abba" Alh Ahmad ya gyaɗa kai yace "then go home and wait for us to come back" yace "tou Abba,thank u" daga haka ya wuce ya shiga mota,Alh Ahmad ya koma parlon ya tarar duk occupants ɗin sun yi shiru kowanne fuskarsa tana nuna damuwa,Alh Ahmad ya zauna yana kallon Abba yace "Alh Zakariyya ina ga tunda ka san halin ƴaƴan ka duka,za mu baka zaɓi a cikin sauran ka zaɓar masa wacce ta dace" Abba yayi shiru bai ce komai ba,Alh Ahmad yace "na yi magana da shi ya ce ko wace ce a bashi" Abba ya numfasa yace "tou! Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi" Uncle da yayi shiru yana nazari yace "tou amma ina ganin sai dai ko a bashi Fatima,dan itace halayensu yake kusan iri ɗaya da Fadwah" Yaa Abbas yayi saurin ɗago kai ya kalli Uncle,a hankali yayi masa alamar yana son fita,Uncle ya gyaɗa masa kai,ya tashi ya shiga gida,ƙofar ɗakin Aunty yaje yayi sallama,su Aunty dake zaune parlon abun duniya ya gama isarsu ta amsa,ya ɗaga curtain ya shigo a hankali ransa duk babu daɗi,sanda ya zauna yana kallon Aunty yace "Aunty akwai matsala fa" Aunty tace "matsalar mene ne Yaya?" Yaa Abbas yace "yanzu Shaheed yazo yace da Abbansa ya fasa shima" "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" was the first kalmar da yazo bakinsu,Yaa Abbas yace "and duk ba ma wannan ne tashin hankalin ba,maganar da ake yanzu na za'a bashi wata cikin su Juwairiyya ne,tunda ya ce ba ya sonta mene ne kuma na cewa a bashi wata?" Kallonsa Aunty ta dunga yi a bit shock tace "shi ya nemi ayi hakan?" Yaa Abbas yace "a'a! Wani abokinsu Abbanmu ne yace ko ayi masa mucanje da wata,kuma ya amsa ya ce a bashi ko wace ce" Yaa Umar da tun ɗazu bai koma ba yana kallon babban Yayan namu yace "Yaa Abbas Abba ya amsa ne?" Yaa Abbas yace "shi ne ban sani ba,na fito na barsu" shiru Aunty tayi ta kasa magana,hankalinta gaba ɗaya ba ya jikinta,dan ko maganar da su Yaa Abbas suke yi ma ba ta ji. Ni kuwa tun shigowar Yaa Abbas parlon na taso na tsaya jikin curtain ɗin ɗakinmu na kasa kunne ina sauraron maganar da suke yi,sanda naji Yaa Abbas yana cewa Yaa Shaheed ya zo da kansa ya sanarwa su Abba ya fasa na lumshe idanuwa ina sauke ajiyar zuciya,lokacin da yake sanar musu wai za'a canjawa Yaa Shaheed da wata cikin su Juwairiyya,take gabana ya yi mugun faɗuwa,na dafe ƙirjina da sauri na juya na koma can ƙarshen bed na zubawa ƙofa idanu,lokaci ɗaya na rasa duka nutsuwata,it was there na fara addu'ar Allah yasa kada haka ya faru. Not too long sai ga Abbanmu ya yi sallama,da sauri na sauko kan gadon na tsaya bakin ƙofa ina sauraren abunda yake sanarwa Aunty na karɓar kuɗin da akayi,Yaa Umar yana zaune ya yi shiru,Aunty tace "Abba wa aka bashi kuma?" Abba yace "Fatimah!" Aunty tayi ajiyar zuciya tana sauke numfashi tace "Allah yasa haka shi ne mafi alkhairi.." Abba ya amsa daga haka ya fita,kuka na fara daga inda nake tsaye,zuciyata tana min wani irin ƙaiƙayin da na rasa gane ko na mene ne,a hankali na koma bakin gado na zauna ina sheshsheƙar kuka,Aunty ta shigo ɗakin ta same ni ina share hawaye,sanda ta zauna next to me,calmly tace "Fadwah! Kukan me kuke?" Da sauri na share hawaye nace "babu komai" tana kallona da kyau tace "yanzu baza ki iya sanar min abunda yasa kika ce ba kaya son Shaheed ba? Nice fa mahaifiyarki,duk duniyar nan akwai wanda za ki iya faɗawa damuwarki bayan ni?" Kwanciya nayi jikinta na sake fashewa da kuka mai tsuma rai,nace "ban sani ba Aunty" tace "ko dai ya yi maki wani abu kika kasa fitowa ki faɗa?" Da sauri na kaɗa mata kai nace "a'a" tace "tou why the sudden change? Na san kina son Shaheed yana sonki,amma haka nan rana ɗaya duk kuce ba kwa son juna,me yake faruwa?" Kuka sosai nake yi har da sheshsheƙa nace "Aunty! U know what?" Tace "a'a sai idan kin sanar min" da sauri na tashi na zauna ina ci gaba da kuka nace "ban mesa nake jin ba na sonsa ba,kuma bai min komai ba,amma haka kawai nake jin na tsaneshi,har ji nake kamar idan aka takura ya aureni zan iya kashe shi" shiru Aunty tayi tana saurarona sanda na gama magana ta gyaɗa kai tace "anya Fadwah kina azkarus'sabah wal-masa'a?" Shiru nayi ban yi magana ba,tace "ba kya addu'ah right?" A hankali nace "ina yi" ta girgiza min kai tace "ba kya yi,da kina addu'ah babu abunda zai same ki" cikin sanyi nace "kwana biyu ne fa kawai ban yi ba na manta" kallona ta dunga yi kamar idan na sake magana za ta rufe ni da duka,nayi fuskar kuka nace "kiyi haƙuri Aunty" wani kallo tai min ta tashi tace "ai shi kenan kin huta,koma mene ne ya faru dake kiyi ke kika janyoma kanki,sakacinki ya janyo har maƙiya sun samu galaba akanki" daga haka ta juya ta fita ɗakin ta barni ina tunanin maganganun da ta faɗa. Direct sanda ta fita parlon Abba ta wuce tana shiga ta sameshi tare da Uncle,sanda suka gaisa Uncle yayi mata Allah ya sanya alkhairi ta amsa,tana kallon Abbanmu tace "Abba magana ya kawo ni gurinka" Abba yace "akan me?" Tace "gaskiya ina tunanin akwai matsala tattare da Fadwah" Abba yana kallonta yace "wane irin matsala Asiya?" Aunty tace "abubuwan nan da suke faruwa tabbas ina ganin there's something behind" Abba yace "ban fahimceki ba Asiya" Aunty tace "tabbas wani ya mata wani abu taji ba ta don Shaheed,amma zan iya rantsuwa da Alqur'ani ba har ranta tace ba ta son Shaheed ba,ni da ƴan uwanta mun isa shaida akan irin son da suke ma junansu" Abba yayi shiru yana tunani,sanda ya gyara zamansa yana girgiza kai,Uncle da shima maganar Aunty yake saurare yace "tabbas wannan maganar ta ki abun dubawa ne Asiya,ni kaina al'amarin nan ya ba ni mamaki da naga Yaron ya zo da kansa yana sanarwa uban ya fasa aurenta" Abbanmu dake saurarensu ya numfasa yana gyaɗa kai,yace "Allah ya kyauta na gaba,wannan kam ya ruga ya faru.." Aunty ta amsa,Abba yace "amma akwai wanda kike zargi ne ta ɓangaren ki?" Aunty ta girgiza kai tace "a'a" though har ranta akwai wanda take jin bata aminta da shi ba,but tana jin da kunya kai tsaye ta fito tace da Abba ga wanda take zargi,sanda suka gama magana Abba yace "in sha Allah zai ma limamin ungurwarmu magana idan ya fita sallah yaji if there's anything,Aunty ta yiwa Uncle sallama ta fita,a tsakar gida sanda za ta wuce parlor,Hjy Umma ta fito parlonta ta rangaɗa wani guɗa,lokaci ɗaya Aunty ta juya tana kallonta.....

     *This book is not for free,it's #200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added in the paid group. Ƴan Niger za ku iya tuntuɓar wannan number +22770766074.*

  
       _#Alhamdulillah alaa kulli halin.. My peoples i'm done with free pages of IN-LAWS,saura KALLO YA KOMA SAMA! In sha Allah,wanda suke jira na kammala free pages da wanda suke neman ci gaban In-laws mu haɗu a paid group,idan duka kike so za ki biya #500,idan ɗaya kike so kuma za ki biya kuɗinsu kamar yanda yake a sama,ga wanda ba sa son group,za su biya 1k for both,idan ɗaya kike so kuma za ki biya #500,Via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,Access bank,na gode._

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 28, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

IN-LAWSWhere stories live. Discover now