DIYAH
{ Short story}Labari ne mai cike da ban tautsayi tare da soyayya mai zafi
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku iya turo katin MTN ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Free Page
01Abiey please!,"rufe min baki *Diyah* na riga na yanke hukunci dole ki bi abunda nake so,nace ki zabi duk kasar da kike so ki ci gaba da karatunki amma baza kije wanchan garin ba,in banda childish irin naki kamar ni *_Excellency Hameed Abubakar Matawalle_* ne zan bari y'ata ta cigaba da Karatu a Nigeria?this is bad,idan ma zaki chanza mind dinki ki chanza it's better for you,na baki nan da three days naji kasar da kika zaba tsakanin Paris, U.k India,Dubai,Malaysia da sauransu"
yana gama fadin haka ya fice daga Parlon bodyguard suka take masa baya ya yin da wannan kyakkyawar matashiryar yarinyar ta fashe da kuka mai cin rai cike da kunar zuciya.Ta shafe awa ďaya ta na kukan,sai da ta gaji Dan kanta ta mike domin ba wanda za ya lallasheta bare har ya share mata hawayenta.
Kyakkyawa ce ajin Karshe tanada matukar kyau mai daukar hankali ga diri kwata_kwata baza ta wuce 18 or 19years ba, fara ce domin farin nata har ya surka da yellow a kallon farko zakace buzuwa ce domin tana yana yi dasu amma idan kadan jima kana kallonta zaka gane cewa bafulatana ce, duk yadda akayi ruwa biyu ce tagama alaka da buzaye.misilta muku kyawun fallon bata lokaci ne amma ku misilta da kanku ya haduwar Palon Gwamna zai kasance.
Fita tayi daga pallon mahaifin nata tabar part din ma gabaɗaya ta wuce part dinta,haske ne a ko ina tamkar rana kamar ba dare ba, ko ina ta gifta ma'aikata ne da sojoji sai rankwafawa suke suna mika gaisuwa.
Bedroom dinta ta shige tare da fadawa saman makeken royal bed dinta(gadonta) ta fashe da kuka da ya kasance aboki a gareta, tana jin kewar Ummieynta da kuma y'ar uwarta.
Idan kana cikin part dinta zaka dauka ba'a Nigeria ka ke ba,kudi sun koka a wannan wurin fiye da tsammani.
Bata jin akwai ranar da hawayenta zasu daina zuba matukar mahaifinta yaki yarda da bukatar ta,rayuwar ma gabaɗaya ta fitar mata akai tanajin komi ya isheta a rayuwa.
Miye amfanin rayuwar da ba farin ciki aciki?Dama haka mulki yake?Da sauri tayi istigfari ganin tana kokarin kauce hanya.
Bathroom (toilet) da ke cikin dakin ta shiga tare da dauro alwala,ko shi kanshi bathroom din abun kallo ne haduwarsa ya zarce misali.Sallar nafila ta kabarta,bayan ta idar ta dauko Al_qur'ani ta fara karatun Suratul_Baqra domin hakan shine zai rage mata kuncin dake cikin zuciyarta.
Ta dau dogon lokaci tana karatun Al_qur'ani kafin tayi addu'a hawaye na sauka saman fuskarta ta kaiwa Allah kukanta,tasan cewa Allah bai manta da ita ba yana sane da halin da take ciki kuma zai mata magani.
Tashi tayi daga kan sallayar ta shiga toilet ta wasa ruwa ta saka kayan bacci ta haye saman makeken gadon tare da lulube kafafuwanta da wani lallausan bargo.
Bata jin zata iya sakawa cikinta wani abu a halin da take duk da cewa tana jin yunwa sosai, ko da yake wazai damu idan taci ko bata ci ba? tuna hakan yasa idanuwanta kawo kwalla amma ta maidasu,ta saka hannu ta jawo wani karamin frame dake gefen gadon ta manna saman kirjinta tana sauke ajiyar zuciya tana karanta Addu'o'in bacci har ya seceta ta na kuďunďune da wannan photon.This is the beginning, siye naki kar a baki labari Naira #300 ne kachal
YOU ARE READING
DIYAH
Short StoryDIYAH Na tashi cikin gata da soyayya,ban rasa komi ba a rayuwata bangaren dukiya ko wani abu na kyale-kyalen rayuwa amma hakan baisa na kasance cikin farin ciki ba. Ada ina rayuwa cikin farinciki da soyayyar Ahali,cikin kankanen lokaci kaddara ta gi...