DIYAH
{ Short story }Labari ne mai cike da ban tautsayi tare da soyayya mai zafi
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number 2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number 09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Free Page
03"Lah lah lah wa nake gani kamar Halimatus_Sadiyah?
"ni ce momy,ina wuni "
"lafiya lau Diyah ya gida ya mahaifin naki"
"lafiya lau yake"
"mashaallah ,amma dai yau b'atan hanya ki kayi ko? "
"aa momy kawai dai nazo na gaidake ne"
"mashaallah Allah ya yi miki Albarka "
"Ameen "
Marwa cikin kwaikwayon muryar Diyah tace "dubeta don Allah wai kawai nazo na gaidake ne,momy tare da wa ki ka ganta"
"tare dake"
"don haka nice na jawo miki ita bata yi niyar shigowa ba"
takare fada tana yiwa Diyah dariyaDiyah ta dubeta tare da cewa,"marwa ittakillaha karya ba kyau"
"Allah ba karya bane momy ba karya ba ne"
"Leave her my daughter ko ya ya ne ai nayi farin cikin ganin ki"
Murmushi Diyah tayi tare da yiwa marwa gwalo,b'ata fuska Marwa tayi tana bubbuga kafafu kasa ita ala dole momy ta b'ata red card.
Dakin marwa suka shiga ya hadu sosai amma bai kai na Diyah ba saman gadon Diyah ta fada ta na fadin,
" wash Allah na wlh na gaji"Tashi tayi zaune ta dubi marwa da niyar yin magana sai taga marwa ta hade fuska tana kallon wani gefe,juyawa tayi taga me marwa ke kallo idanunta suka sauka a kan tufafin marwa dake watse,gaba daya an zubar dasu a kasa daga cikin wadrop.
Kwafa marwa tayi tana cewa,
"Wlh sai na ci kaniyar Safna bari nayi sallah sai naji ubanda ya sakata zubarmun da tufafi kasa"
Takarasa fada tana shigewa cikin bathroom domin dauro alwala.
Murmushi Diyah tayii tana tuna wani lokaci ciki rayuwarta da ya wuce,
Flash back
Sanye take cikin rigar da Wando masu matukar kyau rigar iyakar ta cibi tana dauke da photon teddy an rubuta mata { baby doll } wandon kuma iya karsa guiwarta sunyi bala'in yi mata kyau da gudu ta taho tare da boye wa bayan wata kamilalliyar mata tana fadin
"Ummiey ! Ummiey !! kinga didi ko?"
"na'am Diyah lafiya?mi didinki ta miki "
Kyakkyawar matar dake zaune saman royal chairs tafadi hakan,da kallo daya zaka gane cewar ita ce mahaifiyar Diyah domin kamarsu daya kamar an tsaga kara sai dai Diyah tafi wannan matar hasken fata.
Kafin Diyah tayi magana wata kyakkyawar budurwa ta shigo Palon sanye da doguwar riga wadda tayi mata kyau ba kadan ba itama tana da kyau sosai amma bata kai Diyah ba kuma Diyah ta fita hasken fata kallon mahaifiyarsu tayi tare da cewa,
"Allah UMMIEY yau duk Diyah bata gyara mun kayana ba mai raba ni da ita sai Allah"
"mi tayiwa kayan naki?"
"zubarwa fa tayi akasa Ummiey kuma wlh yanzunnan uwani ta kammala goge su ko awa ba'ayi ba "
Juyowa Ummiey tayi ta dubi Diyah wacce ta boye a bayanta tana leken fuskar riyah tace,
" Sadiya miyasa ki ka zubar mata da tufafi"
turo baki Diyah tayi tana cewa,
"Ummiey bada gangan bane fa kawai naje ne na dubawa teddy na rigarta da na bawa uwani ta yi ironing dinta shine fa kayan suka zube bada gangan ba""ok oya bata hakuri"
"sorry didi"
"sorry for your self,domin next time ni da ke ne"
gwalo Diyah tayi mata tare motsa bakinta ciki ciki take cewa,
"bazan dai gyara kayan ba.."
"Ummiey kinga gwalo fa take min?"
"wai Raliyah yaushe zaki san kin girma ki bar biyewa Sadiyah ne"
"lokacin da tayi hankali Ummiey "
tafadi hakan tana dariya ya yin da Diyah ta b'ata fuska.
tabata marwa tayi firgigit ta dawo daga tunanin da ta lula,marwa tace,
"lafiyar ki kuwa tun d'azu nake miki magana kinyi shiru"
"Nothing "
tafada tare da mikewa tayi cikin bathroom,alwalla ta yi tazo ta kabbarta sallah bayan ta kammala ne marwa ta jata suka wuce dining room suka ci abinci suka koma wurin Ummiey suka haw fira ta jima sosai a gidan sai bayan karfe biyar sannan ta wuce gida.
Bayan takammala duk abunda zatayi ta kwanta tana tunanin miya sami wayar Addarta take kira since shekaran jiya bata shiga,hakan ya zama bakon al'amari gareta domin basu awa biyar ba suyi waya ba.
Washe gari bayan tayi breakfast tana zaune tana kallon cartoon ta gwada kiran Didi bata samu ba ta gwada kiran mijinta,cikin sa'a aka daga kiran,muryar Alh.Muktar ce taji yana amsa Sallamar da take yi,gaidashi tayi ya amsa cikin fara'a,tsaki taja kasa_kasa sam ita bata kaunar mijin didinta kwata_kwata Allah bai hada jinin su ba duk da ya kasance abokin mahaifinta,
"ina son yin magana da didi"
"bana tare da ita,tana Dubai bata jin dadi ne"
cikin razana Diyah tace "what? mine ne ya sameta? "
"Calm down Diyah kawai bari ne ta yi fa shine na kaita chan a duba lafiyarta,bari na turomiki number ta "
Ya karisa fada yana katse kiran batare da ya tsaya yaji abunda zatace ba,sosai hankalin Diyah ya tashi aranta tana tautsayin yar uwarta wannan ne karo na hudu tana bari da ta samu ciki bai zaunawa sai ya fita likitoci sun kasa gano inda matsalar take.Number da ya turo mata ta dannawa kira ringing biyu aka d'aga tare da Sallama,sabanin muryar Riyah taji gaisawa sukayi da juna matar tace,
kina magana da Haulat Muhammad Al'amin kefa"
"suna na Halimatus_Sadiya Hameed Abubukar Matawalle "don Allah ina mai wayar"
"tana bathroom,ni kawar tace kuma matar abokin mijinta amma ke kanwar Riyah ce ko?"
Jinjina kai Diyah tayi cikin ranta take cewa wannan matar badai surutu ba amma a fili sai tace,
'Eh"
"haba gaske, muryar ku ma kamar the same, kece Diyah ko ?"
"Eh nice lafiya....
YOU ARE READING
DIYAH
Short StoryDIYAH Na tashi cikin gata da soyayya,ban rasa komi ba a rayuwata bangaren dukiya ko wani abu na kyale-kyalen rayuwa amma hakan baisa na kasance cikin farin ciki ba. Ada ina rayuwa cikin farinciki da soyayyar Ahali,cikin kankanen lokaci kaddara ta gi...