DIYAH
{ Short story}Labari ne mai cike da ban tautsayi tare da soyayya mai zafi
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku iya turo katin MTN ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Free Page
02Da safe bayan ta kammala shiryawa ta fito falo,dining table ta nufa wanda aka kawata shi da royal chairs ta zauna kalolin kayan breakfast ne birjik a wurin amma tea kawai ta hada ta sha ta koma cikin Palon.
Saman kujera mai zaman mutum uku ta kwanta tana tinanin Rayuwa.
Abubuwa da dama sai su chanza a lokacin da bakayi zato ba,kamar dai yadda rayuwarta ta juye daga farin ciki zuwa wata kalar Rayuwa ta kadaici,karar wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula sunan marwa taga yana yawo a screen din wayar ta iPhone 12 pro max bata samu damar dauka ba har wayar ta tsinke a ka sake kira ta daga tare da karawa a kunnenta sun jima suna waya kafin su gama.
WhatsApp ta shiga tana duba messages wasu tayi reply wasu kuma ta share,wata number na ga tayi searching Didi amma bata online kiranta tayi har so uku amma ba'a dauka ba fuskarta ta nuna alamun rashin jin dadi.Group dinsu na makaranta ta shiga suka cigaba da charting da friends dinta har ta gaji ta aje wayar.
Ga badaya ta gaji da zaman gidan bata saba zaman kadaici irin haka ba Ummieynta bata koya mata irin wannan rayuwar ba,ako da yaushe cikin farin ciki suke ita Ummieynta da kuma Didi wani lokacin ma harda Abbiey amma lokaci guda rayuwa tayi mata juyin waina,Ummiey ta tafi inda ba'a dawowa Abbiey ya sauya sis Riyah(Didi) kuma ta yi mata nisa ya kuwa zata saba da wannan a Rayuwa.
Batasan zubar hawaye ba sai da mahaifiyarta ta mutu batasan zafin rabuwa ba sai Riyah ta mata nisa gashi kuma mahaifinta ba ya da ma lokacin ta ya zatayi.
mikewa tayi ta shiga bedroom dinta ta sauya tufafi,riga doguwa baka ta saka mai adon fararen duwar_watsu tayi rolling da gyalen rigar ba karamin kyau ta yi ba hand bag dinta ta dauka tare da saka ATM dinta ciki ta saka flat shoes farare ta fito rike da mukullin motarta.
Farfajiyar gidan ta nufa wurin da ake parking din motoci ta shiga cikin farar mota Kirar matrix ta tuka tare da fita gate na farko zata fita na biyu taga motocin sojoji biyu suna mara mata baya,kwata_kwata bata son hakan fita tayi ta musu magana duk da cewa sun riga sun san batason hakan,dawowa tayi ta shiga cikin motar ta.
Abu guda ta fuskanta duk abunda take so mahaifinta baya sonsa gaba daya hallayarsu sun sha banban.
Wayar ta tadauka tayi dialing number marwa ta saka handsfree ta ajiyeta,tana dauka tace mata "mu hadu wurin da muka saba haduwa"
"Diyah why not kizo gidanmu"
"No marwa just came out if your free"
"ok no problem but ki biyo ki daukeni domin I can't drive now"
"Badamuwa,ina jiranki kar ki bata min lokaci ta katse kiran"
Dai-dai gidan su marwa tayi parking tare da zuge glass din motar mai gadi na ganinta ya taso ya zo ya na gaisheta tare da sa mata albarka yana godiyar aikin da tasa aka bashi murmushi tayi ta amsa tana tambayarsa mai jiki yace "da sauki"
"Allah ya kara sauki"
Yace "ameen "Wata matashiyar budurwa chocolate colour ce ta fito daga cikin gidan sanye da riga da siket na atampha ba laifi tayi kyau sosai, bude gambun motar ta yi ta shiga Diyah tayi Reverse suka dau hanya.
mai gadi ya dube wani mutum da suke tare mai bawa Flowers ruwa wanda ya fito wajen gate din yanzu ya nuna masa motar da su Diyah ke ciki yace "Salisu wannan da tazo itace yarinyar da nake baka labarinta itace wacce tasa aka daukeni aiki a gidannan kuma ta biyawa matata kudi akayi mata tiyata"
YOU ARE READING
DIYAH
Short StoryDIYAH Na tashi cikin gata da soyayya,ban rasa komi ba a rayuwata bangaren dukiya ko wani abu na kyale-kyalen rayuwa amma hakan baisa na kasance cikin farin ciki ba. Ada ina rayuwa cikin farinciki da soyayyar Ahali,cikin kankanen lokaci kaddara ta gi...