page 05

95 7 0
                                    

DIYAH
{ Short story }

Labari  ne mai cike da ban tautsayi tare da  soyayya mai zafi

Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number 2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number 09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number 09066484295

©️♤♡ Zeesardaunerh

Free Page
        05

Shiru Haulat tayi domin ta lura Riyah tayi nisa kukan ne kawai zai gusar da kuncin da takeji a zuciyarta.
    
     kuka tasha sosai har yaso ya tada mata ciwonta saida likita ya duba ta sannan ya yi wa Haulat fadan abar bari tana shiga wannan halin if not za'a iya rasata gabadaya domin zuciyar ta gaf take da kamuwa da heart attack.

  Bayan likitan ya fita Haulat tayi zaune tana kallon Riyah tautsayin rayuwarta na kara ratsata duk da cewa itama rayuwarta abar tautsayin ce .

Sai bayan awa biyu Riyah ta farka,ruwa ta watsa sannan taci abinci kadan ko shi saida Haulat ta matsa mata fira suka dan taba domin debewa riyar kewa,suna cikin firar wayar Riyah tayi kara dubawa Haulat tayi sannan ta mikawa Riyah.Sunan Alhj. Mukhtar ne baro_baro kan wayar wata bugawa zuciyar Riyah tayi domin har ga Allah ita wannan bawan tsoron sa take tun asali ga wata tsantsar tsanarsa wacce ta zarce ta baya tana tasowa tare da kaiwa zuciyar ta ziyara har wayar ta tsinke Riyah bata daga ba , wani kiran ya sake shigowa amma takasa dagawa,cikin hanzari Haulat tace,

" Riyah kiyiwa Allah ki dauki kiran  nan kar kisa ya yi tunanin abu"

"Allah Haulat bazan dauka wannan kiran ba domin ji nake kamar na kasheshi"

Haulat batayi wata_wata ba ta karbi wayar tare daga kiran,gaisawa sukayi ya tambayeta ina Riyah ta gaya masa bacci take,

"Ok badamuwa idan ta farka ki gayamata ina mata ya jiki,then ku shirya nan da two days jirgin ku zai daga Dubai zuwa Nigeria ku kasance cikin shiri"

"amma ai bata ida jin sauki ba ?"

"Nayi magana da likitan kuma ya bata Sallama "

Cikin d'an razani tace,

"kayi magana da likitan?"

"Eh"
yace yana katse kiran.

"Innalillahi, Riyah wai kinji ya yi magana da likitan?"

d'auke kai Riyah tayi batace komi ba

"kina jina ina magana Riyah amma bakice komi ba "

"mi ki ke sone nace miki ne Haulat?"

"amma kin san idan har yaji ciwon dake damunki dole ne suyi bincike akan hakan"

"ta Allah ba tasu ba Haulat su suka sani sun dade basu yi duk abunda zasuyi ba msstwwwsss"

◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇
ABUJA
◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇

HON. MUKHTAR

Yana kammala waya da Haulat message ya shigo wayarsa,dubawa yayi sannan ya tada motarsa ya nufi wani haddadden park dake cikin garin Abuja,parking motarsa ya yi sannan yanufi wani VIP place wanda suke haduwa shida abokanan sa yan siyasa.

Hon. Mukhtar dogo ne wankan tarwada yana da matsakaicin kyau sannan kuma bayada muguwar kibar nan akalla zasuyi kusan sa'anni da mahaifin Raliya wato Governor Hameed Abubakar Matawalle.

Kyakkyawan wurin da abokanansa suke ya nufa wurin zagaye yake da kujeru guda shida amma mutum hudu ne a zaune,kujerar yaja ya zauna ya yinda suka cike su biyar.

  Gaisawa suka shiga yi da juna kafin wani bakin mutum daga cikin ya fara magana,sunjima suna tattaunawa gameda abubuwan da ni kaina ban fahimce su ba sannan suka dawo kan maganar Riyah.

Alhj. Sulaiman Adamu yace " wai ya ake ciki maganar binciken da ka tura matarka Raliya wurin yi ne"

Dariya dukkanin suka saka wani daga cikinsu yace,

"kaima Sulaiman da wani zance kake ai ko duniya za ta zagaye babu likitan da zaya iya gane mussabbin zubewar cikin nan ba"
ya karisa yana dariya.

"kasan Allah ni har tautsayi take bani" cewar wani daga cikinsu

Hon.Mukhtar yace,

"to kai Imran sanin Allahn kayi"

Dariya duka akwashewa Imran

Duban Hon. Mukhtar Imran yayi yana cewa niko nasan Allah don..."

bai idar da zancensa ba bakin mutum nan wanda suke kira da senator Abubakar(sir) ya tare numfashinsa da cewa,

"sanin kanka ne bamu tarayya da wanda zai dinga kiramuna Allah anan gurin (wal'iyazubillah)don haka kari ke sanin ka kanemi duniya yaso idan ka tsufa kayi retire daga kujerar sai ka nemi gafara daman ai Ubangiji gafurun raheem ne"

Hon.Mubarak yace

"hakane kuwa sir kafadi gasky,nifa naso ganin ranar da BABA zaya ce Imran ya bada dansa na farko kila har suma sai ya yi"

"Hhhhhhhh ai bazai ma fara ba, sanin kansa ne ba a yiwa BABA jayayya domin nasan bazai mance abunda ya faru ga tsohon gwamnan Kaduna ba sanadin kin yadda da abunda BABA yace masa yasa ya yi hasarar rayuwarsa, dukiyarsa,matarsa da kuma jinjirin cikinta dukansu ya zuke jinin su don haka kayi hattara,domin kowa nason samun magaji amma miye amfanin ya'yan ba arzikin kula dasu"

Hon. Mukhtar yace,

"ni shiyasa ma matan basa gabana  domin mace matsala ce Allah dafa kanasonta shikenan fa aiki ya sameka"

"Hhhhhhh lalaima Mukhtar dole kace hakan tunda ka samu yarinya dake samar maka kudi "

ta fawa Mukhtar sukayi da Alhj. Sa'id yace,

"ai shine amfaninta domin ni kasan  idan ba hakan ba bana harka da jinsin su"

Alhj.Sa'id yace,

"nikam sai da su idan basu duniya ba dadi kaima ka gwada harkar zakaji dadinta"

"la la barni a inda nafi kwari ni sam bana sha'awar mata ko kadan,dayar ma ni ta takuramin musamman kanwarta naga ta samin ido sosai sam bata sona ta ci arzikin mata basa gabana da sai na yi mata cin rashin imani"

Gov.Abdulmaleek yace

"nima akwai wani lokaci da na shiga kaduna wurin Hameed na ganta kuma gaskiya na hade wa yarinyar miyau amma so nake tazama mallakina na killace ta"

"kana gani zata amince ta aure wanda ya tsofewa gyatuminta?ina ma laifin kane mawa danka Azeez"

"aka bawa Mukhtar bare ni"

"Mukhtar kace ai ka girmeshi balle ma wannan yarinyar karamace batakai yayarta ba"

"ko dai ya ya ne zanbi hanyar da Mukhtar yabi har ya mallaki yayar wannan yarinyar "

"good Luck your Excellency , nidai na wuce sai next meeting "Cewar Hon. Mukhtar

"ka cigaba da sa ido akanta kar ta bamu matsala domin BABA ya jaddada mani hakan,I think akwai abinda ya gani"

Hon.Mukhtar

"ok Sir badamuwa zan cigaba da sa idon idan aka ga matsala kawai a shafe babin ta a aikata inda gyatumarta ta tafi..🖊️🖊️🖊️"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 16, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DIYAHWhere stories live. Discover now