No 16

98 5 4
                                    

💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                        💎💎💎

*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

                 *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

            *TUNATAR WA*
_Kamar yadda sallah take ibada ce ta ruhu, haka nan muka lura cewa wajen yin ta jikin yakan sami babban ƙarsashi saboda motsa shi da ake yi. Ƙwararrun masana wasannin motsa jiki sun yaba da abubuwan da sallah ta ƙunsa, harkokin nan daban-daban waɗanda ake nanata su a cikin raka'o'in Sallah. Wadannan harkoki ba su barin wata gaɓa a jikin mutum mai Sallah sai sun motsa ta. Watau dai, yadda musulmi suke samun ibada ta ruhu a cikin sallah, haka nan ma suna samun amfani babba na motsa jiki._
         _lada da fa'ida da mai yin Sallah zai samu kenan. Ina hukuncin wanda ya yi watsi da ita, ya ƙi bari ta zame masa garkuwa?_
         _Duk wanda ya juya wa sallah baya ya guje wa Musulunci, ya saɓi Ubangijin sa. Ya karya dokokin imanin sa, ya kuma kama hanyar halaka. Duk ayyukan sa na ƙwarai sun ɓalɓalce don kuwa ya kauce wa umarnin Ubangiji game da Sallah - duk wanda ya saɓa ma Allah tamkar ya ce ba shi ne ma, domin kuwa ai da ya amsa cewa akwai Allah ai ba shakka da ya bi umarnin sa, kamar dai yadda yace, a cikin Alƙur'ani mai tsarki:_
        *"Kuma ku tsayar da Sallah. Lalle sallah tana hanawa daga alfasha da abin ƙi"* _Suratul Ankabut, aya ta 45._
Allah yasa mu dace.








                             *NO_16*

             *WASHE GARI*
          MEEMA na cikin barci ta ji ana shafa mata face, tana buɗe idanuwan ta suka faɗa cikin na Sajjad dake durƙushe a gaban gadon ya tsira mata idanu, da sauri ta sake zaro idanun nata don sake gasgata shi ɗin ne a lokaci ɗaya tana me tashi zaune

"Good morning my love." Yayi maganar yana mata murmushin sa me kyau

Bata iya amsa wa ba kuma bata cire idanun ta a kan sa ba, sai ma tamke kyakykyawar fuskar ta da tayi tana mishi mugun kallo

Tashi yayi ya zauna a gefen ta, kana ya saka hannun sa zai riƙe nata

Tayi saurin daka masa tsawa tana janye hannayen nata, "don't touch me again".

"Why dear?" Yayi maganar kamar zai yi kuka

Tashi tayi daga kan gadon tayi hanyar Toilet ta shige

Da kallo ya bi ta kamar zai haɗiye ta tsaban yanda tayi masa kyau a cikin guntun rigan barcin nata, ko kaɗan ya kasa ɗauke ido a ƙofan har sanda ta fito

Ganin sa a zaune har yanzu sai ta ɗauke kai kawai tana sake haɗe fuska, wajen Trolly ɗin ta ta nufa ta ciro towel da abubuwan da zata buƙata ta sake shige wa Toilet ɗin

Sajjad buga tagumi kawai yayi still idanun sa a kan ƙofan ya ƙi ko gezau. A lokacin da ta fito ai sandare wa yayi ganin ta daga ita sai towel, gaba ɗaya santala-santalan cinyoyin ta a waje suke

Ita kanta bata yi tunanin zata sake ganin sa ba kasancewar ta ɓata lokaci a cikin Toilet ɗin, da sauri ta ja ta tsaya tana kallon sa cike da haushi, "I will prepare. Please Get out."

Numfashi ya sauke sabida jin daddaɗan muryan ta a kunnen sa, yanda yake ji a jikin sa bazai iya magana ba shiyasa a hankali ya taka ya fice a ɗakin har yana sake waigen ta, ji yake yi kamar ya koma ya haɗa jikin su wuri ɗaya tsaban feelings ɗin da yake ji

MEEMA FARUKHWhere stories live. Discover now