No 49

105 8 3
                                    

💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
💎💎💎

*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻‍

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._











*NO_49*

Daƙyar ta samu ta ƙwace bakinta ta kurma uban ihu cikin tsananin firgici da tsantsan ruɗewa, ihu take zubawa kawai tana kokawa dashi da ƙarfin tsiya tana son ƙwace jikinta

Hakan yasa ya sake ta da sauri ya sauka daga kan gadon jin motsin Yusra wacce itama ta farka ɗin a tsorace tana kuka. Da gudu ya bar ɗakin

But ita MEEMA tsaban ruɗewa bata san ma ya fita ba, tuni ta faɗo ƙasa a garin guduwa ta ci takai tana ta kurma ihu

Ihun nata ne har ƙasa wanda yasa Umar Farouk shi da Luwaira suka fito a guje suka yo ɗakin nata. Suna shigowa ya nemi makunnin ɗakin ya kunna, a nan ya ganta a kwance tana ta zuba ihu duk ta gama firgicewa gashin kanta ya wargaje ta cure waje ɗaya, ita kuma Yusra tana kan gadon itama tana kuka

Da sauri ta taso tunda ta ƙyalla idanu ta gansu ta faɗa jikin sa a rikice tana kuka

Shima ya rikice ɗin a yanda ya ganta, nan ya soma rarrashin ta yana ƙoƙarin kama mata gashinta wajen buɗe mata fuska. "Lafiya MEEMA me ya faru ne? What's wrong?" Tambayoyi yake ta jero mata ya kasa tsayawa

Itama kuma sai kuka take yi tana sake shigewa jikinsa, yayinda bakinta ke motsi but ta kasa furta komai

Hakan yasa ya sake rungume ta sosai a jikin sa domin ya gane ta tsorata ne ainun. Kallon Luwaira da ke bayansa yayi yace, "Ki je ki rarrashi Yusra mana kin tsaya a nan, kina jinta kuma tana kuka?"

Takawa tayi kawai ta wuce kan gadon zuciyarta kamar zata ƙone don haushi, ita gani take yi babu abinda ke faruwa kawai duk makircin MEEMA ce, ya za'a yi ta tashe su da tsakar dare tana musu hauka a gida? Tsaki ta ja a zuciyarta yayinda take rarrashin Yusran. Har sai da ta ga tayi shiru ta koma barcin sannan ta tashi ta fice kasancewar shi Umar Faruk tuni ya ja MEEMA sun fita falo

Suna zaune a falo yana ta faman rarrashin ta har yanzu ya gaza shawo kanta

Daƙyar a yanzu ɗin ta buɗe baki take sanar mishi, "wani ne ya shigo mata ɗaki, da idanunta ta ganshi ya kwanta mata a jiki, ita baza ta iya kwana a nan ba a tsorace take zai dawo mata."

Sosai zuciyar Umar Farouk ta buga da jin zancen ta, nan da nan idanun sa suka soma sauyawa har sun soma tara ruwan hawaye. "wani kuma? Wani ya shigo mishi gida?" Yayi maganar a zuciya cike da tsananin tashin hankali

Ita kanta Luwaira wacce ta fito ta tsinkayi maganar MEEMAN sai ta tsaya kawai a wajen tana kallon su, wlh rainin wayau ne taya wani zai shigo gidan nan idan ba makirci irin nata ba? Tayi hakan ne kawai don ta ɓata mata darenta ta ɓata mata jin daɗin ta, ta kula MEEMA babban makira ce na bugawa a jarida, makirci ne wannan babu yanda za'a yi wani ya shigo gidan nan. Shiyasa gaba ɗaya taji ranta ya sake ɓaci ainun, sai ta saka ƙafa kawai ta fice kamar zata kifa

Umar Farouk be ma san ta fita ba saboda a halin da yake ciki, ga kuma yanda MEEMAN ta hana shi saƙat sai kuka take mishi, hakan yasa hankalinsa yayi matuƙar tashi nan da nan har kanshi ya soma ciwo, zuciyarsa zafi take masa sosai hakan yasa ya ci gaba da lallaɓa ta yana faɗa mata, "babu wanda ya shigo, sai dai ko mafarki take yi, maybe a mafarki ne taji kamar Mutum ya shigo mata." Shi kansa yana faɗar maganar ne domin yana so zuciyarsa ta yarda da gasken mafarki tayi, ba ya fata ace wani ne da gaske ya shigo mishi gida har kan gadon Matarsa yake neman ta

MEEMA FARUKHWhere stories live. Discover now