chapter 5&6

119 3 4
                                    

_*SOLDIERS BARRACK*_
              _*(BARIKIN SOJOJI)*_

    
                  *NA*

_*FARIDA ABDULLAHI IBRAHIM*_

               _ *(FEEDYN BASH)*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Page 5&6

Asiya na fita bata zame ko ina ba sai dakin saurayinta maza ne sojoji zaune, gefe ga wasu karuwai da suka dakko daga waje cikin bacin rai ta kalli Kamal cikin bacin rai "meyasa kake san zama cikin wayannan dirty people din, kasan bana san kana mu'amala da matan waje ko?" Kallonta yai cikin  murmushi "ki dena ce musu dirty people suma haka suke kallonki,  dan haka kiyi rayuwarki suyi tasu tunda ba a kanki suke ba hasalima ba wajena suka zo ba yan matansu James ne." Ranta yai masifar baci irin rainin wayon da yai mata a cikinsu suna zaune suna buga ludo suna maita kallon shekeke su yammatan, hakan ya kuma tunzura zuciyarta cikin fushi ta juya zata bar dakin yasa hannunsa ya jawota jikinsa, kwalla ta taru a idonta fal sai yaji ba dadi ko banza ai ita yar maigidansa ce.
       Daya daga cikin yammatan ta taso jikinta wandon sojoji tasa ga dukkan alamu n Kamal ne. Cikin fushi ta hankade Asiya daga jininsa wanda sai da kanta ya bugu da bango, tuni ta durkushe a wajen tana kukan sangarta hakan ba karamin bata ran Kamal yai ba, ko banza Asiya ta fisu amfani a wajensa idan bukatarsa ta tashi kafin suzo Asiya ta biya masa. Cikin salon rangwada take magana "Kamal kasan ni macece mai kishi wace karya ce wannan da zaka kawota inda nake, kuma kai ka gayan baka da kowa sai ni amma tun kan tafiya tai nisa zaka gwadan halin naku na karnanci, tunda ku kuda ne baku haram muddin zaku gani sai kun latsa mtsww!" Taja tsaki maganganunta sun matukar fusata shi, cikin fushi ya gaura mata mari wanda sai da bakinta ya fashe, ya dakko belt dinsa ya fara tafkarsu daga ita har kawayenta ihu suka fara na neman dauki, su James ganin haka suka mike suna bashi hakuri ko kllonsu bai ba da kyar suka janye shi waje yana huci hannun Asiya yaja sukai dakin James.

       Amma fa yammatan sun daku matuka jikinsu duk ya farfashe ranar suka fara nadamar iskanci, sunyi nadamar sanin Soja a rayuwarsi matuka. Cikin kuka dayar take cewa "Allah ya isan mu wallahi duk kece kika janyo mana shegen surutunki da san gwada ke wata tsiya ce, an gaya miki anaiwa sojoji haka? Ai gashinan a kokarinki na burgewa kin janyo mana cin uban duka a hannunsa, kinga ba zancen ki zuba iskancin ki ki dare a waje saboda kina da saurayi Soja Allah ya sakamana." Gaba daya yammatan uku kuka suke suna saka kayansu domin jikinsu duk ya farfashe belt ce mai karafuna a jikinta cikin azaba suke shiryawa su James na taimaka musu suna basu hakuri, amma ko kallonsu basa yi domin shima haushinsa suke ji suna kallo ai aka jibgesu amma sun kasa rama musu.

Dakin James ya shiga da ita tana kuka sosai yake jin ba dadi kukan nata cikin bacin rai yace "enough Asiya! kina kallon hukuncin da nai musu saboda ke hakan bai isheki ba? Ko wani abu kikeso kuma?" Cikin shawaba tace "ni so nake su bar dakin kar su kara zuwa nan." Murmushi yai "ai tafiya zasiyi kema kin sani James ne dama ya kawosu sorry Aseena." Nan ya din gai mata wasa harta saki jikinta suka lula duniyar tasu da suka saba bai barta ba sai da tai laushi tasa kuka, yana jin dadin tarayya da ita saboda tana dauke masa bukatunsa matuka.

****************

Jawaheer ce ta shirya tsaf cikin wani blue black din jeans, tasa white top ta dakko dan ziririn mayafi ta dora, murna take da farin-ciki da doki, bata da burin daya fi ta kasance da Aalim, tana ji dadin hirar da sukai jiya ko kallonta kai nishadinta na daban ne. Cikin sauri ta fito tace "Maa! Zanje gidansu Asiya na dubota tace mun bata da lafiya." "Eyya ki gaida ta kicewa mamanta ina gaisheta nima ina mata sannu, kin san babanki ba zai bari ba da naje dubata." Gabanta ne ya fadi kar karyar da tai a gane "no Momy ki zamanki kawai dan ciwon kai ne kadan ne."

      Fit ta fice tana dan tsalle a hankali take tafiya ta wajen block dinsu tabi, ba kowa hakan ya sosa ranta sosai cigaba tai da tafiya ta ji tai an rungumota ta baya cikin tsoro ta saki kara juyo da ita yai suka hada ido. Wani kallo ta watsa masa da sauri ya saketa ya kama kunnensa "sorry my dear nayi kuskure bazan kara ba, wasa nai miki bansan hakan zai firgita kiba." Wani kallo ta watsa masa ta kuma hade fuska "malamina na Islamiyya ya gaya mun hakan ba soyayya bane haramun ne, domin duk mai aikata hakan Allah zai kona shi a wuta, kuma idan kuna hakan da sunan soyayya da saurayi tabbas baya sanka baya kishinka yaudararka zai yi domin idan ya sabama wani saurayin yazo shima za kai masa, kuma yace koda auren mutum kai zai na zarginka." Kallonta kawai yake yi ya kasa dauke idonsa daga kanta wani mugun shaukin kaunarta da soyayyarta me zafi ke ratsa shi. Tambayar kansa yake anya ko wannan yarinyar rainon barrack ce? Yaran da sam basu da tarbiyya komai na rayuwarsu a sake, abunda ke kara bashi mamaki mahaifinta yafi kowa lalata da mata, ikon Allah haka Allah yake ya fitar da rayayye daga jikin matacce. Katse masa tunani tai "ko ba haka ba Aalim?"
      Numfashi ya sauke "haka ne Jawaheer! Dole nai wa Allah roki Allah ya mallaka mun ke a matsayin mata, domin ke din wata baiwace mu zauna a can." Wani dutse ya nuna mata suka karasa suka zauna. "Jawaheer Allah da kansa yace kar mu kusanci Zina ina kyamar zina matuka da gaske, bana layin sojoji masu lalata rayuwar mata, kece ke daukar hankalina saboda yanayin yadda kike shiga, ina so kidena dan Allah hakan zai kara nesanta ni da ita, kinsan a kaf duniya zan iyai miki ittikafin masu aikin force munfi kowa neman mata, masu take mana baya drivers ne kin san dalili?" Girgiza kai tai "hmmm! Mu sojoji muna iya tafiya wani gari mu shekara biyu uku mafi karanci shi ne daya ba tare da iyalanmu ba, gashi dare da rana muna aiki muna ganin mata kala-kala musamman da daddare kuma mu ba ice ba, y'an adam masu tsananin sha'awa tayaya ba zamu aikata haka ba?" Kallonsa take kawai tabbas maganarsa hakane, domin tana yawan ji babanta da mamanta suna fada akan mamanta tana ya kamata wasu sojojin su dawo gida saboda hakkin iyalansu amma yace ba zasu dawo ba, dama saboda hakane sai sannan ta gane akan me suke magana. Su kuma driver suma kusan hakan ne koda yaushe suna titina suna ganin mata kala-kala karuwai na dauke musu hankali fiye da matansu."

      Horn ne mai karfi ya dawo dasu hayyacinsu Cornel Shu'aib ne cikin fushi ya fito daga motar ya wankawa Jawaheer mari ya hankada mota ya rufe, ya juya ya kalli Aalim da gaba daya ya firgice saboda tsananin tsoron ogan nasu yasan mutum ne shi mara imani bare tausayi, akan hakan sai yai masa muguwar azaba.
    "Kai ka saurareni da kyau idan na kuma ganinka da yata wallahi sai na sa an saka a guard room anci ubanka." Fuuu yaja mota yai gida fincikota yai har ciki ya watsawa uwarta ita "wallahi tallahi na kuma ganinta a waje daga ke har ita sai ranku yai mugun baci, soyayyar dana ke nuna mata ba zai hana na hukunta taba." y
Ya juya ya fice cikin kunar rai.

   Comment din ku shi zai tabbatar da cigaban wannan labari.

                  *feedyn bash*

Pls
Share
Comment

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 01, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BARRACK SOLDIERS LABARINE AKAN RAYUWAR YAMMATA DA MATAN AURE A BARRACKSWhere stories live. Discover now