EPISODE 37- SCARED

13 2 0
                                    

🔱 ṨÄQÄŔ ṨÖ🔱🔱
              ⚜️🗝️  ( _love cub_ ) 🗝️⚜️

Mallakin :Queen Nasmerh
Marubuciyar 👇
1:Ayisherh
2:Mrs Bilal
3:Mrs Bilal continuation
4:Barrister Muhammad
5:Wani hanin ga Allah
6: Fayroz
7:Hajna

And now 8:SAQAR SO.
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
EPISODE 37: SCARED
°°°°°°°°💗💗°°°°°°°°

“Ahhhhhhhhhhhhhhhh! "ihu ne ya karaɗe ko ina na gida, Pappy ne ya yi saurin nufar ɗakin Leesha inda sautin ihu ke fitowa, tare da Ummie da Ishtar su ka isa ƙofar ɗakin, wanda shigowar su Ummie kenan su ka jiyo ihun, rigen-gen su ke yi wurin shiga ɗakin, Leesha da ke zaune tsakiyar gado tana kallon ko ina na ɗakin, duk zufa ta karyo mata, duk da AC da ke kunne, jin ƙarar buɗe ɗakin ya sa ta saurin rufe ido gam, kirjinta sai tashi sama ya ke yana ƙasa, da alama a firgice ta ke, da sauri Ummie ta ƙarasa ta riƙe ta gam, “Leesha ki buɗe idonki ", duk maganar da Ummie ke yi haka be hana zuciyarta bugawa da ƙarfi ba, “Leesha, ki buɗe idonki Pappy ne" wannan karon ta soma jin natsuwa, amma duk da haka bata buɗe idonta ba, haka kuma be hana zufa karyo mata a jiki ba, kamar wacce aka ma wanka da ruwa haka jikinta ya jiƙe, “Leesha mu ne fa, Pappy, Ummie da ni Ishtar ki buɗe idonki please, tell us what's happening (ki faɗa mana abunda ke faruwa) " Ishtar ta faɗa tana dafa kafaɗarta, da sauri ta buɗe idonta tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, “me ya same ki?" Ummie ta tambaya, duƙar da kanta tayi na minti biyu sannan ta ɗago da ƙarfi tana faɗin “Pappy Mie Amor, Zaina da Leena su na ina? " ta tambaya har yanzu a rikice, “Haba my dear Aaftab ya fita tun safe tare da Leena da Ishtar, kin san ta na shirin tafiya makaranta, shi ne zai raka gurin karɓo graduation gown ɗinta, Leena kuma ta wuce office, me ya faru?" Ummie ta faɗa, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, “mafarki ne kawai" Leesha ta furta, Pappy ya ce “mafarkin me? ", “Pappy bari na yi wanka ji yadda na jiƙa jikina, wallahi yau na yi mummunan mafarki, wai Pappy ƙarfe nawa ma", Ishtar ta kalli agogon wayarta “ƙarfe 11:30 na rana " ta faɗa tana maida dubanta ga Leesha, “oh Allah Ishtar Wallahi yau na yi barci ni fa ko sallah banyi ba, wai ni me na sha ne?" Leesha ta faɗa, murmushi Pappy ya yi ya ce “sannu da makara, ki yi sauri ki yi sallah to ", Ummie ta ce “lallai kam, ai makara ba halin Leesha ba ne zuwan abu ne yau, bari mu jira ki parlor a ba mu labarin wannan mafarki haka ", dariya kawai ta yi ta shige toilet.

Bayan ta yi sallah ne ta yi wanka, ta jira aka yi azahar, sannan ta sauka downs stairs, “yauwa ƴar lelena zo ki faɗa ma Pappy mafarkin da ki ka yi" Pappy ya faɗa, Ummie da ke gefe ta ce “sannu me ƴar lele ni ba za'a ce da ni ba ", Ishtar ta ce “nima nan na ƙagu na ji mafarkin da ya firgita Sisto", Ummie ta ce “ba Sisto ba wallahi alkubus ", dariya su ka sa gaba ɗaya, Leesha ta zauna ƙasan carpet ɗin, “mun jinki" su ka faɗa a tare, sai kuma su ka kwashe da dariya “tare mu ka faɗa" su ka sake faɗa a tare, yanzu ma dariya su ka ƙyalƙyale da ita, “yau dai nishaɗi ku ke ji, wallahi Pappy ni dariyar kawai na ke yi amma ba har zuci ba", ta faɗa sannan ta maida dubanta ga Ishtar ta ce “Ishii wai kin ji abunda na ji kuwa ", “ina fa zan ji, ai sai kin faɗa min" Ishtar ta faɗa, Ummie ta ce “ni fa kun dame ni, a faɗa min mana", Leesha ta ce “to Ummie mafarki na yi wai ɓarayi sun shigo gidan nan, kuma wai sun....... ", “a'uzubillahi ki ce dai mugun abu ki ka gani" Ummie ta faɗa, Pappy ya harare ta “daɗi na da ke katse hanzarin mutum, yanzu tai ki kana shiru " dubanshi ya mai da ga  Leesha ya ce “ mu je zuwa", Ishtar ta ce  “sai ka ce wani abu, ni dai sister tashi mu je ɗaki ki ban labari, this people will never let u rest ", Leesha kam sai kallonsu ta ke yi, ta na mamakin yadda su ke ta nishaɗi bayan ita mafarkin da ta yi suk ya gigita ta, “mu je zuwa mana" Pappy ya faɗa cikin nuna ƙaguwa, “wai kuma sun halbe Ishtar a kai, sun kashe Zaina, Mie Amore kuma baya da lafiya yana kwance saboda dukan da aka mishi, wai kun san the worst part of it shi ne wai sun min fyaɗe, Leena kuma ta su ma, abun dai ba kyan gani, oh Allah ni anya ma na yi addu'a da zan kwanta? ", Ummie ta ce “ki ce mun ga tashin hankali, ai dole ki rikice, Allah dai ya tsare", Pappy ya ce “ mumman mafarki daga shaiɗan ne Leesha, insha Allah babu abunda zai same mu ", murmushi ta ɗan yi sannan ta ce “Pappy har da su Adamu fa an halba wai amma duk basu mutu ba, ni fa ban ɗauka mafarki na ke yi ba, wai ka ga yadda abun ya faru", Ishtar ta ce “ki ce Adamu an je lahira an dawo", “bana son iskanci fa, Adamun nawa za ki tsokana Leesha ta faɗa, Ummie ta ce “yanzu dai malama tashi ki ci abinci ", tashi Leesha ta yi dan sai yanzu ta tuna bata ci komai ba.

🔱🔱ŚĂQĂŔ ŚŐ🔱🔱Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt