EPISODE 10-TEARS AND PAIN

28 3 0
                                    

🔱🔱ṨÄQÄŔ ṨÖ🔱🔱
             ⚜️🗝️  ( _love cub_ ) 🗝️⚜️

Mallakin :Queen Nasmerh
Marubuciyar 👇
1:Ayisherh
2:Mrs Bilal
3:Mrs Bilal continuation
4:Barrister Muhammad
5:Wani hanin ga Allah
6: Fayroz
7:Hajna

And now 8:SAQAR SO.
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
EPISODE 10-TEARS AND PAIN
°°°°°°°°°°°°💗💗°°°°°°°°°°°°°

Gida su ka nufa, Aaftab da Leena da Ishtar a mota ɗaya, Pappy da Ummie da Zaina a mota ɗaya, driving Aaftab yake yi cikin tashin hankali, shi kaɗai yasan abunda ya ke ji, bazai iya jurar ganin Leesha a irin yanayin nan ba, a zahiri ya rasa me ya janyo wannan matsalar, a ɓangaren Pappy ma tunanin da ya ke yi kenan, gashi bazai iya gayawa su Ummie ba, amma yasan dole zasu sani lokacin da su ka koma asibiti idan ta farfaɗo.

    Kwana 7 Leesha ta ɗauka a yanayin rayuwa ko mutuwa da ƙyar aka samu ta dawo da numfashin ta, Aaftab tsaye a kanta lokacin da aka gama mata allura, Pappy kuwa ya je gida domin ya ɗauko su Ummie, dan a yanayin nan baya bari suyi driving, buɗe idonta ta fara yi a hankali har ta samu ta buɗe su duka, kallon saman ceiling take yi a hankali, ƙoƙarin tashi take yi amma ina, hannun ta a ɗaure yake, kuma ga ɗauri a kafaɗa, Aaftab ne ya kamata, kallon shi take yi dan ita bata ma san inda ta san shi ba, to me yake yi nan?, wanene shi?, to ma tsaya wacece ita? Abunda take tambayar kanta kenan, “Leesha kin tashi kenan, zaki ci wani abu? ", Aaftab ya faɗa, girgiza mishi kai tayi alamar a'a, su Ummie ne su ka, shigo, da sauri Leena ta matso inda take, “Leesha kin tashi", Leesha sai bin su take da kallo, wacece Leesha kuma miyasa su ke kiranta da Leesha, rungumeta Leena tayi tace “kiyi haƙuri kinji za'a gano wanda ya miki haka, kuma an sauke sojojin da suka kamaki, yaya Aaftab ne yayi...... "bata ƙarasa ba saboda yadda Leesha ta ture ta, tana ta zare-zaren ido, hawaye su ka zubo a kuncin Pappy, kenan da gaske Leesha ta rasa hankalinta, Leena ce ta ɗago tace “Leesha kina lafiya kuwa, miyasa zaki ture ni?", Ummie kallonta take yi, matsowa tayi tace“Leena wataƙila Leesha na fushi da ke ne saboda kin barta ita kaɗai" ta faɗa tana zama kan gadon da Leesha take, matsawa Leesha tayi gefe, Ummie tace “Leesha ya jiki? ", Leesha ta dafe kanta tace “wacece Leesha?, miyasa kuke damuna? , ku su waye dan Allah? , ina ne nan? ", hawaye ne su ka biyo kuncin Ummie tace “ke baki ma iya tunani ba, Leesha sunan naki kika manta ", Leena tace “Leesha ki tuna mana, ni ce gudan jininki fa, kar ki min haka, kiyi haƙuri idan na ɓata miki rai bazan sake zuwa gida ba, kinga kayana ma na ɗauko" ta faɗa tana nuna mata kayan, Pappy ya matso, Leena tace “Pappy ka mata magana, bana son wasa tayi haƙuri mana ", Pappy be iya furta ko kalma ɗaya ba, Zaina tazo da gudu “aunty Leesha kiyi haƙuri mana zamu kwana anan", Leesha tayi murmushi tace “ kina da kyau amma ni ba auntynki bace, ni ban san ku ba, dan Allah ku faɗa min ina ne nan ", Aaftab ne yayi ƙarfin hali yace “kuyi haƙuri Leesha ta rasa tunaninta bazata iya gane kowa ba", Ummie tace “Injiwa ya faɗa maka haka ", Pappy yace “likita", dai-dai lokacin likitan ya shigo, nan ya sake musu bayani Leesha kuwa sai zuba ido take yi kamar mazuru, takarda sallama aka basu kamar yadda Aaftab ya buƙata, Aaftab kawai ta yadda ya kamata, dan haka basu ja musu ba ya kamata ya saka a keken guragu(wheel chair) , shi yake tura ta, Ishtar, Leena da Zaina sai kuka su ke yi suna bin bayanshi, Leesha tace “kai wanene "murmushi yayi abun da Aaftab be saba yi ba yace “ni abokin ki ne" ɓata rai tayi tace “to kai miyasa baka kuka, su kuma waɗancen miyasa su ke kuka ", yace “kinga ni jarumi ne bazan yi kuka ba", Leesha tace “su ba jarumai ba ne? ", Aaftab yace “su ai suna sonki ne shiyasa su ke kuka", Leesha tace “kai baka so na? " murmushi yayi yace “sosai ma, ai nafi su sonki", “to a ina su ka sanni ", “yace waccan mamata ce, ki riƙa ce mata Ummie" ya nuna mata Ummie da ta wuce tare da Pappy, tace “to wanene kusa da ita ", yace “shi babana ne, ki riƙa ce mishi Pappy za su ji daɗi su daina kuka" murmushi tayi tace “to ni me zaka riƙa ce min? ",“Mie Amore" ya faɗa, dai-dai lokacin su ka iso gaban motar su, “oya ki bari Leena ta kama min ke mu saki a mota ", ya faɗa, kallon shi tayi tace “miyasa? Wacece ita?" ta tambaya tana cizon hannu, hannunshi ya ɗaura kan hannu da tasa a baki, a hankali ya cire hannun yace “kar ki ƙara sa hannu a baki in ba haka ba za mu ɓata kuma zan yi kuka ", “to" ta faɗa, yace “wannan itace ƙanwata ki riƙa ce mata Leena ko Other half kinji "ya faɗa, gaɗa kai tayi, sannan ta yadda Leena ta kamata su ka shiga mota.

    Gida su ka nufa kai tsaye inda suka sami ƴan jarida da mutane duk sun cika gidan, da sauri ƴan jarida suka fara ɗauka lokacin da aka fiddo da Leesha aka sata kan kujerar guragu, gabanta su ka iso, “shin zaki faɗa gaskiya game da abunda ya faru da ke da kuma abunda ya faru a Abeer global company? " wani ɗan jarida ya tambaya, Leesha turo bakinta tace “ wanene Abeer?, me ya same ni? , ku su waye?, ina ku ka sanni? ", “amma ai........ Ɗan jaridar zai yi magana Aaftab ya dakatar da su “duk wanda ya yi yunƙurin faɗa mata wani abu daya faru a baya zanyi ƙarar shi, bata hayyacinta, kuma ance idan wani ya faɗa mata wani abu da zai firgitata zata rasa tunaninta har abada, dan haka ku kiyaye " ya faɗa yana tura Leesha zuwa ciki, ƴan jaridar kuwa suka haɗa tarkacen su suka fita.

  “Miyasa su ke tambaya na?, su waye su? " Leesha ta tambaya, Pappy yace “yan shirin film ne ", dariya Leesha tayi tace “laaaaaaa dama na bari sun ɗauke ni kaga sai su sani a TV", murmushi Ummie tayi tace “a'a zasu ji miki ciwo, ai da hatsari sosai ", Leena kuwa da gudu ta haura sama, kan gado ta faɗa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya, maganar gaskiya tana cikin yanayin da bazata iya ko murmushi ba, yanzu Leesha bazata iya tuna kowa da komai ba, kuka kawai take yi.

Aaftab ne ya tura keken zuwa ɗakin Leesha, kan gado ya aje ta, inda aka jona komai na aikin asibiti a ɗakin, “Mie Amore ki kwanta kin ji"ya faɗa yana kwantar da ita kan gado, kallon shi tayi tace “bazaka kwanta ba ", girgiza kai yayi yace “bazai yuyu mu kwana tare ba, mace da namiji basa kwana tare", “miyasa to? " ta tambaya, Aaftab yace “haramun ne", Leesha tace “minene haramun ", Aaftab yace “saɓama Allah, kuma idan kika saɓa mishi zai ƙona ki da wuta", zare ido tayi tace “a'a ni bana so a ƙonani ", yace “yauwa kinga ni bazan kwana ba, amma Leena zata taya ki", “a'a ni bana so "ta faɗa, Aaftab yace “miyasa? ", Leesha tace “haramun ne fa", murmushi yayi yace “ai ita macece, ba haramun bane ", gaɗa kai tayi alamar ta fahimta, “to ki kwanta"ya faɗa, “to" ta faɗa tare da rufe idonta , har ya kusa fita ya juyo, buɗe idonta tayi a hankali, ai kuwa su ka haɗa ido da sauri ta rufe, dariya yayi yace “idan kika sake buɗe idon ki zan gane kuma bazan miki magana gobe ba, good night ", ya faɗa yana jan ƙofar, ai kuwa Leesha ta rufe idonta gam, taƙi buɗewa.

      Ɗakin Leena ya nufa, kwance take har yanzu bata daina kuka ba, “Leena" ya kira sunanta yana mai zama gefen gado, ɗagowa tayi ta sauke idonta da su ka kaɗa su ka yi ja tace “na'am", yace “kin fi kowa sanin yadda nake ji game da Leesha, amma yanzu ba lokacin kuka bane", Leena tace “amma kasan bazan iya ba, ina ji na kamar wata sakarya, miyasa na bari Leesha ta shiga wannan halin ". Aaftab yace “baki yadda da hukuncin ubangiji ba?", “na yadda "ta faɗa lokacin da hawaye ke sauko mata a kunci, jawota yayi jikin shi, domin ya bata kafaɗar da zata yi kuka, kuka tayi me isar ta, sannan ya bata handkerchief ta share hawayenta, “ki tashi ki je ɗakin Leesha ki taya ta kwana, kinga ba za'a bar mara lafiya shi kaɗai ba, sannan kar ki je can ki riƙa kuka, haka zai fara sa tana tunanin wani wani abu tayi mu ku kuke kuka, kinga ta fara magana, sannan kar ki faɗa mata komai da ita, ki nuna mata ni abokin ta ne, ke kuma da su Pappy da su Ishtar ƴan uwa na ne, a hankali ita zata dawo cikin hayyacinta ", “to shikenan" Leena ta faɗa tare da fitowa ta nufi ɗakin Leesha.

Anan zan dasa aya............ ✍️

Taku mai sonku da Alkhairi Queen Nasmerh.

Kar ku manta kuyi following Wattpad account ɗina ta link ɗin da ke sama.

ALQALAMINA✍️ YAFI KOWANE TAKOBI ⚔️KAIFI

🔱🔱ŚĂQĂŔ ŚŐ🔱🔱Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon