EPISODE 3:LOVE AT FIRST SIGHT

53 3 0
                                    

🔱🔱ṨÄQÄŔ ṨÖ🔱🔱
              ⚜️🗝️  ( _love cub_ ) 🗝️⚜️

Mallakin :Queen Nasmerh
Marubuciyar 👇
1:Ayisherh
2:Mrs Bilal
3:Mrs Bilal continuation
4:Barrister Muhammad
5:Wani hanin ga Allah
6: Fayroz
7:Hajna

And now 8:SAQAR SO.

QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT

Show me love and follow
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION 🌙🌙⭐✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم

_Assalamu alaikum Ma"abota karatun Littafan Hausa kama Daga Littafin Daya karkata kan Soyayyah ko ya karkata kan  Nishadantarwa ko ya karkata kan Fadakarwa,ko ya karkata kan Wa"azantarwa ko kuma ya karkata Wajen Ban Tsausayi da Rudani..Toh ku matso Kusa Nesa Tazo Kusa Ina Wadanda basu iya Juran karatu Saboda  Matsalan Ido kuma gajiya ko kuma ayyukan Gida na yau da kullum wanda baya basu Damar Lokacin karatu..? To ku kwantar da Hankalinku Kina Daga Dakinki kina aikin ki ko kuma kina Daga Zaunenki basai kin Wahala wajen karatu ba *DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV* Ba domin komai suka samar da wanman Channel din ba Sai Saboda Irinku masoya ma"abota Karatun Littafan hausa koma wani iri ne,Muna da Littafai ko wani iri kike Bukata wannan Channel Din ba iya littafan Hausa ya Tanadarmuku ba ya Tanadar muku Abubuwa Da yawa wadanda zaku karu dasu,Ga mai Bukatar kwasan garabansa Dake Cikin Wannan Channel Din zai iya Tafiya kai Tsaye Zuwa ga *YOUTUBE* Dinshi yayi Searching *DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV* Domin samun Duka Shiryan Shiryanmu akan Lokaci kada mutum ya Manta da Danna Mana *SUBSCRIBE* da kuma Allon kararrawan Sanarwa Domin ya sanar Daku da Zarar mun Dora muku wani Sabon Shiri In kuma kuna son Tafiya ne kai Tsaye zaku iya Shiga ta wannan Link din Batare da Bata Lokaci ba Zaku Tsinci kanku a   *DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV* sai kunzo muna Maraba Daku Masoyanmu..._👇🏻

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Mom Musayyid (lovely one) ❤️❤️, Zeesardauna❤️❤️ wannan shafin naku ne ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

EPISODE 3:LOVE AT FIRST SIGHT
°°°°°°°°°°°°°°💗💗°°°°°°°°°°°°°°
“Leesha! "Omar ya faɗa da ƙarfi, cikin taku da isa ta juyo dan ganin, wanene wannan mai mata kiran mafarauta, karaf suka haɗa ido da shi lokacin da ta juyo, idon ta a tsai-tsaye suke, sannan kai tsaye take kallon shi, jin yadda zuciyar ta ke bugawa har tana mata barazanar faɗowa ya za me mata sabon yanayi, takowa yake yi, ba alamar tsoro ko girgiza a tare da shi, cikin jajircewa da dakiya, amma kafin ya ƙaraso ta juya zata tafi, Anita ce ta tare ta da magana “ma he's the visitor that came here to meet u yesterday, and u ask him to come back today by 1:30"(ranki ya daɗe shine baƙon da ya zo jiya nan, kika ce ya dawo yau), Leesha tace “i don't have his time as usual "(bani da lokacin shi, kamar ko yaushe dai), cikin jin haushi Omar ya yo kanta, dan tun da suka fara magana yana ji, “ke wace irin mutum ce, wacce bata san darajar ɗan adam ba?", bata juyo ba kuma bata amsa shi ba, sai hannu ta saka cikin jakar ta, ta ɗauko bandir ɗin dubu-dubu har bandir biyu, wanda ya kama dubu ɗari, miƙa wa Anita kuɗin tayi sannan ta mata nuni da Omar, buɗe office ɗin tayi tare da rufe shi, ta ɗaura hannun ta akan ƙirjinta zuciyarta na matuƙar bugawa, fuskar Omar kawai take gani, wani yanayi take ji da bata taɓa ji ba, murmushi tayi a hankali ta furta “ i love his boldness ", guri ta zauna tana aiki.

  A ɓangaren Omar, Anita ce ta nufo shi da kuɗi, miƙa mishi tayi, cikin takaici ya karɓa, tare ƙudurtawa a ranshi har abada bazai sake dawowa nan ba, yanzun ma ya karɓi kuɗin ne saboda lafiyar Farrah, autar gidan su kenan, Leesha kuwa aikin ma gagarar ta yayi, haka yasa ta haɗa kayan ta, da takaddun ta, ta nufi mota, Adamu ya ja mota, har su ka isa bata ce komai ba, idon ta a rufe yake tana tunanin Omar, tafiyar shi da yadda ya ke da taurin rai sune suka fi burge ta, gida suka nufa, a mota Adamu sai zuba surutu yake yi, wani bin ta amsa shi, wani bin tayi murmushi, wani gurin kuma ta gwashale shi, a haka har suka isa.

🔱🔱ŚĂQĂŔ ŚŐ🔱🔱Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum