EPISODE 47-DISAPPOINTED

12 0 0
                                    

🔱 ṨÄQÄŔ ṨÖ🔱🔱
⚜️🗝️ ( _love cub_ ) 🗝️⚜️

Mallakin :Queen Nasmerh
Marubuciyar 👇
1:Ayisherh
2:Mrs Bilal
3:Mrs Bilal continuation
4:Barrister Muhammad
5:Wani hanin ga Allah
6: Fayroz
7:Hajna

And now 8:SAQAR SO.
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
EPISODE 47- DISAPPOINTED
°°°°°°°°°°°°💗💗°°°°°°°°°°°°°
Na sadaukar da wannan shafin gare ki Ameena Musa danko, I can't love u less my friend, Allah ya nuna mana bikinki mu ci ƙosai mu dad-daga yaji.

WASHE GARI DA SAFE

Kiɗe-kiɗe ta ke ji ta ko ina mamakin waye ya zo da su ta ke yi, fitowa ta yi daga ɗakin har ta na sarƙe ƙafafuwanta tsabar sauri, Mr Gaffar ne ya shigo dai-dai lokacin da ta fito, "barka da sabuwar rayuwa An nur " ya faɗa ya na rungume ta, murmushi ta mishi, "ki na azumi ne?" ya tambaya, kallonshi ta yi irin ban gane ba, ganin ta na kallonshi yasa shi riƙe ƙugu, ya na jujjuya ido ya ce "azumin magana na ke nufi ", "umhmm" ta ja dogon numfashi, "mu je waje ki gani " ya faɗa ya na jan ta.

Waje su ka nufa, inda ake ta kaɗe-kaɗe, ana bushe-bushe kamar masarauta, wasu yara ta gani guda biyar daga wani gefe, kamar Gaffar ya yi kaki, daga wani gefe kuma wata mata ce da shekarunta baza su wuce 27 ba, idonta ta juyar zuwa ɗayan gefen, nan ma wata matar ce kusan tsara da wadda ta gani, sai kuma wata daga gefenta da shekarunta baza su wuce 23 zuwa da 24 a duniya ba, kallon gidan ta ke yi amma ta kasa gane komai na gida, can gefen mota ta ga wasu yara guda uku, sai kuma yara biyu kan mota, duk cikin yaran babu wanda baya kama da Gaffar, ikon Allah, ɗaya daga cikin ɓangaroran gidan ta kai idonta kai wata tsohuwa ce da bazata gaza shekaru 60 a duniya ba ,sai wani tsoho da bazai wuce shekara 68 zuwa 69 ba, tsohon ya yi mugun kama da Gaffar.

Kallon Mr Gaffar ta yi da alamar tambaya, ita kam ta kasa gane su waye waɗannan, da alama family house ne wannan, dan har yanzu akwai wasu part da bata ga ko motsin mutum ɗaya a gurin ba, "hey baby " ya faɗa ya na waving hannunshi, dan ya lura ta lula wata duniyar daban, "explain" ta faɗa, murmushi ya yi ya ce "to ranki ya daɗe yadda ki ka ce ", "to ina ji, kiɗe-kiɗen minene"ta tambaya , "al'ada ce ta gidanmu, amma zan miki bayani, bana so ki yi magana har sai na gama", gaɗa kai ta yi irin ina ji, murmushi ya yi ya ce "good girl ", sannan ya ja hannunta, zuwa gaban waɗannan tsofaffin ya ce "wannan ce Mamana, ana ce mata Hajiya Khadeeja, Amma mu muna ce mata Hajiyar Yara", kallon Leesha ya sa ke yi ya ce "wannan kuma shi ne Babana mu na ce mishi Alhajin yara", jan hannunta ya yi zuwa gaban matar da ke zaune ita kaɗai ya ce " wannan ita ce Uwargidana Aseeya, waɗancan yaran da ki ka gani guda biyar " ya nuna mata yaran da ke tsaye daga can gefe ya ce "yaranta ne, Ammar, Amara, Ameer, Ameera da Ahmad autanta", gaɗa kai kawai Leesha ta yi, dan ita sai yanzu ta san yaranshi, murmushi ya mata ya ce " mu je na gabatar da ke ga sauran ƴan gidan, gaban mata guda biyu ya tsaya da ita ya ce "wannan ce Bilkisu matata ta biyu, mahaifiyar yara uku da ke gefen motar can, sunan yaranta Maryam, Hassan da Husaini, sannan wannan ce matata ta uku Haleema, mahaifiyar Hassana da Husaina yaran da kika gani kan mota, makaɗan da ki ka gani kuma al'adace ta gidanmu a duk lokacin da ka yi aure washe garin zuwan amarya za'a tarbe ta " ya ƙarasa magana ya na murmushi, Leesha kuwa tuni jikinta ya mutu, "ki na ji na ko, duk part ɗin da ki ka gani a nan, ban da na ɓangaren dama to duka haya ake yi, wannan dalilin ne yasa idan na auri mutum to zaman cikin gida ya kama ki, ko Hajiyar yara bata fita, amma fa idan na lamunce to kowa zai fito, ba'a musu akan hukunci na, bana magana ana yi, sannan duk hukuncin da na yanke ya zauna babu wani mahaluƙi da zai canza shi, sannan matana basa magana da juna sai na yarda, yarana basa min magana sai in ni na so haka, ina sonku duka, kuma ko gobe na ga wata ina so zan aura, dole ku zauna da juna " ya faɗa ya na nuna dafa kafaɗar Leesha, hannunta ta sa ka ta ture nashi, sannan ta koma ciki da gudu ta na kuka.

🔱🔱ŚĂQĂŔ ŚŐ🔱🔱Where stories live. Discover now