🔥🔥🔥🔥🔥
*_LAST BONANZA_*
*KARO NA QARSHE!**_farincinku shine namu,ZAFAFAN DAI,sun sake amsa kokenku,sun sake rage muku kaso 20 cikin 100_*
*_Daga yau 29 ga wata,har zuwa 31 ga watan nan,xaku iya biyan 800 a amadadin 1000 na kudin litattafai biyar_*
*_za'a fara posting in sha Allah 3st January da yardar Allah_*
*HANZARTA KI BIYA NAKI KAFIN RANAKUN SU QARE*
*XAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYASAIKU TURA SHAIDAR BIYA
08184017082
GA MASU TURA KATIN WAYA KO KUMA VTU,SAIKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYANKU
09134848107
_______________________
Chapter Four.
...........Suna baro cikin asibitin Muhibbat ta kashe wayarta dan ma kar Yah Ammar ya sameta.
Tun farkon shigowa anguwar tace a saukesu. Amma sai Zahidah tace sam basu yarda ba a kaisu har ƙofar gida. Zata fara masifa Hafsat ta ce, “Kiyi haƙuri ya kaimu saboda bazan iya taka ƙafarnan ba Hibbah”.
Shiru tayi bata sake tankawa ba har suka iso ƙofar gidan su Hafsat daya kasance a farko, sai nasu Zahidah, Muhibbat ce ƙarshe. Saboda ciwon dake tare da Hafsat ɗin ya sakasu cewa a tsaya ƙofar gidansu. Zahidah ta bama mai taxi kuɗinsa tana godiya. Amma sai yaƙi amsa. Mamaki ƙarara a fuskar Zahidah da Hafsat. Sun buɗe baki zasu magana yay musu alamar suyi shiru.
“Basai kunce komai ba, inhar da wannan mai bakin tsiwar tare da ku anta kaiku waje ƙyauta kenan babu ko sisin ku”. Yay maganar idanunsa akan Muhibbat yana wani sassanyan murmushi.
Hararar da yay tsammani ta watsa masa, cikin takaici tabar wajen batare da tace komai ba. Kira Zahidah da Hafsat suka shiga ƙwala mata suna dariya, amma ko waiwayensu batai ba harta ƙarasa gaban wani gida mai baƙin gate. Sai da ta kama murfin zata shiga ta waigo, ganin har yanzu mai taxi ɗin na tare da su yasata jan tsaki akan laɓɓanta ta ce, “Maye kawai”. Daga haka ta shige ciki.Gida ne da zamu iya kiransa babba a girma da ginuwa. Dan a ƙalla akwai ɓangarori biyu zuwa uku a cikinsa. Ɓangarori biyu na farkon shiga gidan sunfi haɗuwa da tsaruwa, zakaga hakan tun daga wajema kafin ka kai ga shiga ciki, sai dai kuma ɗayan dake daga ciki ya fisu girma, amma bai kai su ƙyawu ba.
Harara ta zubama sashen guda biyu tana taɓe baki, tana gab da wucesu taja tsaki a zuciyarta wanda batai zaton ya fito har waje ba.
“K!! Dan ubanki wa kikema tsoki!!”.
Wata buɗaɗɗiyar murya mai cike da hargowa ta faɗa. Cak ta tsaya ƙirjinta na bugawar tsoro, tabbas da ace tasan mugun nan ya dawo gidan da bazata shigo ba sai magriba. Jin takun tafiya a bayanta alamar ya taso ya sakata juyowa. Ƙiris ya rage ya iso gareta, babu shiri ta kwasa da gudu zuwa sashen can ciki tana ƙwala kiran sunan Ummi!.
“Ya ilahi! Tanee lafiyarki kuwa? Wai sai yaushe ne hankali zai game jikinki kisan girma ya fara zuwa miki!”.
Ummi dake ƙoƙarin fitowa a kitchen riƙe da ludayin miya a hannu ta faɗa. Dai-dai isowar Hibbah cikin falon itama a guje. Bayan Ummi taje ta maƙale.
“K da wa kuma?”.
Ummi ta faɗa tana juyowa gareta fuska a ɗaure.
“Wannan mugunne fa Junaid Ummi. daga na shigo ina tsaki ya hau zagina kamar nasan da zamansa ma a gidan”.
Baki Ummi ta buge mata, tai saurin ja da baya daga jikinta tana dafewa.
“Wannan bakin naki da kanwa bata jiƙa a cikinsa shi zaisa kiyita shan wahala a wajen mutanen gidan nan Tanee. Mara kunyar banza matsamin a hanya”.
Gefe Hibbah ta matsa gudun kar Ummi ta sake kai mata wani dukan hawaye cike da idanunta. Sai da taga ta koma kitchen ɗin sannan ta nufi ɗakinta zuciyarta na ƙara jin tsanar mutanen gidan nasu. Da ace zata samu wata dama a hannunta koda ta yini guda ce sai ta bisu da bulala hansin-hansin, musamman ma Hajiya Mama da Abba da wannan azzalumin Junaid ɗin. Mukulli ta murza a ƙofar tata dan batason sake magana da kowa.
YOU ARE READING
TAKUN SAAƘA!!
RomanceTAKUN SAƘA littafi ne da yazo muku da wani salo na musamman. tare da tsaftatacciyar salon soyayya tsakanin wasu tom and jarry😂. halinsu ya banbanta da juna. hakama burinsu da halayyarsu. Ta yaya RUWA DA WUTA zasu kasance a mazubi guda bayan kowanne...