💎💎💎💎💎💎
💎💎💎💎💎💎💎💎
*ITA CE SILAH*
📲(wayar Android)📲
~*it based on True life story*~
💎💎💎💎💎💎💎💎💎
💎💎💎💎💎💎💎💎
💎💎💎💎
💎💎💎
💎💎
💎

*Labari da rubutawa*:Faridat Husain Mshelia(Ummu-Jidda).

*FREE PAGE*
*Wannan shine shafin k'arshe kamar yanda na alkawaran ta Mu ku, ga mai bukatar siya sai ya turo da katin glo na 200 ta wannan numban 0815314 4521 domin samun k'arashen labarin*

*Shafin nan tukuici ne ga Hassan Atk ina godiya sosai da kulawar ka gareni tare da muhimman shawarwari game da wannan littafin,Allah ya yi mata tukuici da samun mace tagari*

*SHAFI NA GOMA*

Kunya ya sa Mu ka fara wasan y'ar b'uya ni da Abbi da Ammi har sai da su ka min tsiya-tsiya kafin na dawo normal Amman Sam na gagara sake wa,

Zaman d'akin da a baya shine al'ada ta shi ma Sam na daina ganin yanda na takura kaina da yawa ya Sa Umma bi na da nasiha a kullu yau min har na dawo abin ya bi jiki na.

Hamma ta fara Nabeel da ke kwance a jikin ta yace"Bacci ko?"

Ta girgiza mi shi kai alamun "A'a", gajiya ce kawai ga shi ka sha'afar da ni ban tambaye ka ko ka ci abinci ba ma?

Shafa shafaffen cikin shi ya yi Wanda rabon shi da abinci tun karyawan safe Wanda ya yi kafin su fara video call da Beelah,

Ganin abinda su ke aikata wa kuma shi ya mantar da shi ma yunwar cikin shi har ya kamo hanyar Suleja daga Minna ba tare da ya san me ya ke ciki ba,

Ba tare da ya ba ta amsa ba cikin shi ya bada sautin "quuuu"alamun jin yunwa d'aga kan shi ta yi daga cinyar ta ta fice tare da ce mi shi tana zuwa,

Direct gurin ma'aikatan wajen ta je ta tambaye su kalar abincin da za su iya ci,jin akwai komai ta yi order tare da sallamar su d fada musu room numbern su ta koma,

Cikin mintoci da ba za su gaza 10 ba su ka ji knocking Nabeel ya kai duba gare ta ta yi mi shi murmushi tare da fice wa ta k'arbi saqon ta dawo,

Ta da shi ta yi kafin ta fara feeding din shi da ruwan coffee mai zafi dan ganin yanda cikin shi ya yi laqam,

Sosai ta cika mi shi cikin shi da ababe marasa nauyi har sai da ya fara kau da kai,

ta had'a mi shi ruwa mai d'umi ya watsa a jikin shi Dan warware gajiya ko kafin ya fito ita ma ta yi dam tare da kakkabe gadon,

Da towel ya fito yana goge jikin shi ganin yanda ta sunkuyar da kai ya Sa shi jingina da jikin bango yana k'are mata kallo tare da tunanin meyasa duk mijin Beelah yin wasarairai da matar shi duk da ta kasance mace mai kyau na zahiri da bad'ini(jiki da ni'ima),

biyayya da ladabi kawaici da kunya duka ya lura Beelah ta tara su kuma a Dan zamantakewar su ya lura mace ce mai matuk'ar tsafta da tattali uwa uba kulawar da ta Saba ba shi duk ta *SILAR WAYAR ANDROID*,

Gaskiya ya kamata ya san menene ya SILAR da ya sa mijin ta yin sakaci da tarbiyar ta har ta fad'a cikin wannan halin?

Sanin ya fito ta ji kuma har lokacin bai karaso gare ta ba ya sa ta d'an dago da fuskar ta ganin yanda ya tsare ta da ido ya sa ta yin tattaki zuwa gare shi ta bada tazarar ta ku 2 had'e da tafa hannayen ta,

Firgitgit ya yi tare da dage mata gira alamun "ya ya dai an mata"

"Tunanin me ka ke yi"ta tambaye shi duk da matuk'ar kwarjinin da ya yi mata ganin surar shi cikin singilet duk jikin shi a mummurd'e,

" Kallon surar ki na ke yi tare da tunanin lusarin mijin da ya same ki amman ya yi sake da tarbiyar ki ba tare da ya killace ki ba"

Mamaki ya gagara bari na duba ga yanayin labarin da ki ke ba ni yanzu hankalina ya fi karkata da fad'amin wanene Mijin ki?

Shin mutum ne shi ko aljani dan Allah?,

Murmushi ta yi mai matuk'ar ciwo Wanda yafi kama da yaqe tare da fashe wa da wani irin kuka tare da nuna mi shi guri ya zauna a bakin gado,

Ji ya yi tamkar ya ce ya hakura da labarin Amman tuno da ya kamata ya Sani ya sa shi janyo ta jikn shi ya fara lallashin ta har sai da ya ji ta yi shiru tana ajiyar zuciyar zuciya a jajjere alamun ta sha kuka ta more cikin sanyin murya ta fara ba shi labarin..
..

*HADUWAR BEELAH DA AHMAD DEEDAT*

Yammaci ne mai matukar sanyi na ranar wata Asabar bayan mun ta so daga islamiyya sai sauri na ke domin in isa gida da wuri dan ganin hadarin da ya hadu ya yi baqiqqirin alamun ruwa yana gab da sauka wata zukekiyar murya mai cike da haiba ta yi min sallama da "Assalamu Alaikum",

A firgice na juya dan Sam ban ji alamun takun da ya yi min sallamar ba sai jin muryar shi na yi a bazata,

Amsa wa na yi sanin darajar sallamar ba tare da na tsaya ba na ci gaba da sauri na dan har guguwa da iska sun karade ilahirin gurin had'e da yayyafi yif-yif-yif,

Gudu-gudu sauri-sauri haka na cigaba da tafiya har na iso bakin titin kwar Gidan Mu in da na tsaya saboda irin mugun gudun da y'an achaba ke yi dan haka na tsaya raina a b'ace ganin ga k" oshi ga kwanan yunwa,

Da wannan damar Ahmad ya samu ta hangar janyo hannuna a bazata ya tsallakar da ni cikin mugun tsiwa da takaici na ce"Malam kai wani irin d'an iska ne da za ka kamo hannu na bayan kasan ni ba muharramar ka ba ne"

Murmushi ya yi mai had'e da sauti kafin yace"Daga taimako sai a jefe ni da mummunar kalma irin wannan?"kiyi hakuri ba da niyya na yi ba gani na yi in ba hakan na yi ba bazaki tab'a samu ki tsallake titin ba da fatan an min afuwa gimbiya.

Hararar shi na yi tare da murguda baki jin sautin ruwan ya na daf da iso Mu dan ya sauka ya sa na sheka a guje na shige cikin gida ba tare da na k'ara saurarar shi ba,

Bi na ya yi da kallo cike da sha'awa tare da ya ba ma tarbiyan ta har ruwan ya sauka kan shi ba tare da ya san lokacin ba,

Sanadiyyar ruwan mai iska ne ya sa shi fakewa A k'ofar shagu nan gidan Mu yana ta zabga murmushi tamkar Sabon Ango,

An shafe fiye da awa 1 ana zabga ruwan tamkar da bakin k'warya kirar Sallar magrib shi ya sanya ruwan tsagaita wa Wanda ya zamto silar fitowar Abbiy domin zuwa masallaci,ganin tsabar kaman da ke tsakanin Mu da Abbiy ya sa Ahmad rissina wa ya
ya gaishe shi a ladabce,

Sannan y d'ibi ruwan da ke zuba a in dararo domin yin alwalla a kusan tare su ka shiga cikin masallacin su ka yi sallah su na idar wa Ahmad ya k'arasa kusa da Abbbiy domin sanar da shi k'udirin shi,

Iznin fara tsayawa da ni ya nema nan ta ke Abbiy ya ba shi dan ya ya ba da hankalin shi matuqa ya tafi zuciyar shi cike da farin ciki.

Mu na zaune ni da Ammi muna cin tuwon shinkafa da miyar d'anyen kubewa Wanda ya sha tantaqwashi da soyayyen man shanu sai zabga k'amshi yake yi,

Abbiy ya shigo ya na"Alhamdulillahi,Allah ma ji rok'on bayin sa,tabbas wa man ya tawakkal alallah fa huwa hasbu"

"Mai kuma ya faru Abban Nabeela?cewar Ammi na,

" Abun farinciki yanzu ina fita na had'u da wani yaro a k'war gida............,nan ya fayyace mata haduwar su da Ahmad har izinin fara zuwa zance guri na da ya nema"

Kabbara ita kan ta ta yi cikin jin kunya da Matuk'ar haushi na tsame hannuna daga cikin abincin dan ganin tamkar su na Neman kai da ni ne na shige cikin d'akin Mu tare da fashewa da kuka.

*Alhamdulillah na kai k'arshen page d'in kyauta a yau,ga mai buk'atar Samun cigaban wannan littafin ya tuntubi wannan numban. 0815 314 4521 domin biyan kud'in karatu ko kuma ya yi min magana ta username d'ina na Facebook: Faridat Husain Mshelia.

*Masoyana tabbas na na b'ata ma wasu rai dalilin wannan rubutun dan ha ka su yi hakuri da ni dan duk d'an Adam ajizi ne ba bu Wanda ya ke wuce kuskure,kaunar da ku ka nuna min kad'ai ya isa in sa ku a fagen masoya na Haqiqa ina godiya sosai*

Godiya ta musamman ga fans d'ina na:
ITACE SILAH FANS 1&2
THE DMK'S WORLD.....
AUREN D'ANGARUWA...
JARUMAI WRITERS..........
MSHELIA HAUSA............
ATK GROUP FACEBOOK....
ZAHRA SURBAJO.........
YASMEEN........
HAFSAT AND AK SARAKI dama sauran groups din da ban ambata ba duka ina godiya Allah ya hada fuskokin Mu da alhairi.

*Ummu-jiddah*

 ITACE SILAH(Wayar Android).Where stories live. Discover now