Episode Four: Obsession

16 2 3
                                    





Episode Four: Obsession

    Alokaci ɗaya na nemi  nustuwa ta narasa,me zan yi adaidai wannan lokacin?,domin nasan Salman farin sani, Mutum ne wanda baya jada baya aduk Abinda yasama gaba sai ya cimma ƙudurin shi akai, wannan tunanin ne yasa gumi masu zafi suka zubo min,nayi saurin fita daga Kitchen din kirjina na dukan uku uku, jikina na ɓari, ahankali yake bina yana faɗin"Asma Kenan,gudun me kike?ina zaki je da zaki samu kariya?".

Hankali tashe nace"Mommy!!! daddy!!!, Saliha!!!!,John driver!!!audu mai gadi!!, innalillahi wa'inna ilaihi raji'iun"nake cewa at the top of my voice,ina ƙoƙarin buɗe handle din ɗakina,ga mamaki naji kofar arufe,da sauri na juyo ina wurga ma Salman kallon tsana, kallon raini,takowa yake ahankali zuwa gareni,yace"unfortunately babu wanda zai iya taimaka miki".

Hawaye Masu ɗumi na zubo min nace"idan wanda na kira basu taimaka min ba, ALLAH zai taimaka min,kuma taimakon shi yafi na kowa,shine zai kuɓutar dani daga mugun nufinka kuma yayi maganin ka ta sigar dabaka taɓa tsammani ba".

"Saboda rashin imani da tausayin ka ya wuce tunanin mai tunani,duk da nasan gada bazatai gudu ba ɗanta yayi rarrafe amma kai mugune ne ɗan masara na ajin ƙarshe,so kake ka lalata min Rayuwa ta hanya mafi muni,abu ɗaya zan tabbatar maka dashi, Wallahi tallahi sai Inda ƙarfina ya ƙare,zan yi iyakar ƙoƙarina wurin kare mutuncina Da darajata ta ƴa mace da ALLAH ya bani,zanyi hakan da gumi na,da hawaye na,da kuka na,da ƙarfi na,da jini na harma da rayuwata".

Lafiyayyen marin daya ɗauke fuskata dashi ne yasa maganar tawa ta tsaya cak,ta dunƙule a maƙoshi na wanda ya bushe ko alamar danshi babu Saboda bakin ciki da takaicin marin da Salman ya zabga min,runtse idanu nayi na haɗiye Bakin cikin daya tokare min wuya, atake idanuna suka ƙafe suka daina zubar hawaye,domin kuka bazai min maganin matsala ta ba,jarumta ce da dakiya zasu zamto makaman yaki awurina,dasu zanyi amfani wurin yaƙar Daddy Da ahalin shi.

Sautin dariyar Salman ce ta katse min tunani,na wurga mishi kallon tsana wanda yake fitowa direct daga zuciyata mai balbala tana ci da wuta saboda tsananin takaici da baƙin ciki,rashin darajar tawa takai haka awurin Daddy Da ahalin shi baki ɗaya?

""ƙaramar mara kunyah,yau zan nuna miki ni babban mara kunyah ne wanda yayi degree Da master's harma da PhD a Ɓangaren rashin kunyah".
''har kin isa ki zagi iyayena wanda suka taimaka ma rayuwar ki da tuni yanzu kina agolanci agidan Anty Salma,har kin isa ki nuna bakya sona kina cikin gidan iyayena?uban waye ya baki wannan damar?kin ɗauka na hakura ne?kin zata na manta ne?Kin yi tunanin shikenan kinci galaba akaina,upon all burikan danake shi akanki? alokacin baya na soki da aure,naso ki amatsayin mata wacce zamu kasance tare aduk lokacin danake so,amma ayanzu amatsayin karuwa nake sonki,wacce zamu kasance tare batareda aure ba".

Kalaman Salman na ƙarshe sunyi min kaushi dayawa,ban taɓa zaton rashin hankalin shi yakai haka ba,cikin ɗaga murya nace"banason iskanci da rashin mutunci, I'm trying really hard kada na biye maka muyi abinda bai kamata ba,niba karuwa bace kuma bazan ga karuwanci arayuwata ba,kaje inda kasaba zuwa domin bazan ɗauki halin akuyanci ba,idan kai bakada hankali ni inada shi,idan bakada kunyah ni inada ita,domin tabbas da Kanada kunyah bazaka furta abinda ka faɗa ba,ita kunyah tana daga cikin imani, Salman bakada imani bare kunyah,dan haka ina gargaɗinka da babbar murya wannan ya zama karo na ƙarshe dazaka min irin wannan rashin ɗa'ar".

"Gameda zancen ina zama agidanku,kamanta sanda Daddy bashida komai,kamanta sanda kuke garari a gidan haya?ka manta sanda idan kunci abinci babana ne ya bayar?ka manta sanda babana ya baiwa daddy jarin daya fara kasuwanci,babana ya tallafi rayuwar ku daga duhun talauci,ya ɗaukaka Daddy fiyeda kowa Acikin Rayuwar sa,saboda me yayi hakan?kabani amsa saboda me yayi hakan?yayi hakan ne Saboda ALLAH sannan yana koyama Daddy yadda zai taimaka ma wasu ya tallafi rayuwar su kamar yadda aka tallafi rayuwar daddy Da taku,ban taɓa zaton zaku iya cutar da koda magen baba ba bare ni ƴar cikin shi daya haifa".ina gama faɗin haka nayi saurin matsawa kusada flower vases,gabana na tsananin faɗuwa, abin mamakin shine banji motsin mommy da Daddy ba,kuma Yakamata ace sunji hayaniyar Da mukeyi.

ASMA...Where stories live. Discover now