page ...34...

251 21 1
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...34....






A bakin kofar gidan ya faka motar a yah shiga,yara sai kallonta suke manya kuma suna mamakin yanda tashi daya mutari yasamu morewa a jin dadi a sama wasu suna inama sune suka samu hajiyar daya aura( hmmm dama haka mutane suke,a duk lokacin da'aka samu wani mai kudi yazo wucewa ko kuma wani talaka yayi kudi saikaji mutane suna cewa,ina ma mune da dukiyar nan,bayan basusan shin ta wacce hanya ya samuba,ko kuma wane irin kalubale yake fuskanta da dukiyar,burinsu kawai shine ina ma sune suke da dukiyar kawai.
Bayan bamusan wata dukiyar samun gwanda rashin samunta yafi kwanciyar hankali sau dari akan samunta din.
Allah ya taimakemu yabamu rufin asiri dakuma dukiya mai albarka wacce zata kawomana kwamciyar hankali ba akasin haka ba).

Babu kowa a gidan sai kajin inna kawai,gidan babu shara sosai amma kuma babu tarkace kaman da,dan ko girki dama bayi take ba bare kuma ta yi tunanin tara kwanuka.
Sallama mutari yayi a bakin kofar dakim innna yana kakkada makullin motar dayake hannunsa,dan dama mutari badai karyaba.
"Inna kina cikine?"
"Eh ina ciki mana mutari iso mana daga ciki"
Yamutsa fuska yayi yana furzar da iska kafim yace,
"Kai inna gaskiya bazan shigo ba ko fito dai waje,bakyajin zafin da akene,ina shiga kuraje zasu fiffitomin a jiki,musamman ma da man danake shafawa bayason zafi ko kadan"
Wani salati inna ta buga tana tafa hannu tareda dago labulen tana fitowa daga dakin,kare masa kallo tayi daga sama har kasa kafin tace,
"Iyee mutari,wannan ificin fah da karyah,kaifah dama tsiyatah dakai kenan,yanzu dakin da'aka haifeka a cikin shine zai sakaka kuraje?,hmmm babu laifinka samu kayi kana shiga ac,ni ina duk da samunnaku kun kasa sakani a sanyin nima"
"Shakuru minki inna kibar mita,indai sanyine har saikin jawo wani ma ciki,bari muje yawon kashashe mu dawo nida hajiya,zaki sha mamaki,akwai wasu kudi da aka dawo mata dashi daga Cairo wajen wani business dinta,kudin a gida ta ajieysu,so nake na sandeta nayi wuff dasu mugudu muje mu wana"
"Kai dannan karfah ta kamaka kuma"
"Karki Damu inna yau muka fara raba masu kudi da kudinsu,yamzu dai ka wannan dubu hamsinne da kuma kayan abinci yara zasu shigo dashi idan na fita,hajiyah tace a baki kafin mu dawo"
Rawar yan bori inna tafara tana kirga kudin tana sambatu,kwata kwata nutsuwarta ta bar jikimta ma.
Suna cikin hakanne shema'u ta fito daga dakin taci wani uban shiga dawasu English wares,bakaramin kama jikinta sukayi ba suka zauna,sai zuba uban kamshi take fatar nan tasha mayuka masu tsada ta bada kalar launin yellow kaman amaryar data sha dilka.
Ko kula mutari batayiba tasaka kai zata fice daga gidan,dan dama bashiri suke ba.
Har takai wajen bakim kofah mutari yace,
"Ke ina zakije ne haka da wannan shigar da tsakar rana"
"Wajen alhajina zanje kaman yanda kake daga wajen hakiyarka,sannan zamu dan shakatane kafin aure kaman yamda kuma kukayi taku shakatawar,ina fatan ka fahimta mutari.
Inna na tafi yau zam jarraba aikin maganin"
"To diyar nan kiyi taka tsantasan fah"
"Karki damu nasan takan wannan harkar"
Bayan ta fitane mutari ya kalli inna tareda cewa,
"Inna wane magani kuke zance akai keda ita za'a jarraba?"
"Bai shafe ka ba zancen matane nida itah,basai kajiba ehe"
Tun da shema'u ta fita daga gidan take wata karairayah da malkwasa kaman zata karye,a kwankwasa motar tayi lokacin data isa bakin wajen,zuge glass din alhaji Sama'ila yayi tareda kankance ido itah kuma tayi masa fari da nata tareda kashe masa daya.
Bude kofar tayi ta shiga tana sauke wani kasalallen numfashi na munafurci,
"Alhaji  nawa yakk ya jindadi,jiyah daya har nayi missing dinka"
Dariya yayi harda doka sitiyarin motar kafin yace,
"Kema kikayi missing dina inaga ni kuma danayi missing wannan lallausar fatar taki"
"Hmm baxaka gane bane yanda nake jinka a raina fah"
"Karki damu babY,menene kuma nafadin kewata,ai kawai saimuje mu shana,nifah banso ki nemi abu ki rasa matukar ina da yadda zanyi"
"Kai alhaji shiyasa kake burgeni sosai,yau so nake nabaka rana nan kyauta takace kayi yanda kake so da Ita"
Murmushin jin dadi yayi kafim yace,
"To ina gimbiya take so muje?"
Wani lumshe ido shema'u tayi tareda cewa anzo wajen a cikin ranta.
Wani rantsatstsen sunan hotel ta ambata naji da fada,tashi daya kuwa ba bata lokaci yah figi motar zuwa inda tace.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now